in

MADADI CHAPTER 2

MADADI CHAPTER 2

Ramlatu wata irin mata ce mai izzah da ta’kama! bata da hali mai kyau! Tayi ta wulakanta kishiyarta kasancewar ta yar talaka gorin yau daban na gobe daban! a duk sanda Alhaji Sama’ila zaiyi mata aiken kud’i ko kuma tufafi sai ya had’a da kishiyarta kafin ta bawa kishiyarta sai ta gama yi mata gori sannan! Ita kuwa da yake mai hakuri ce sai dai kawai ta girgiza kai ta kyaleta, gabadaya Ramlatu bata dauko halin mahaifinta da ‘yan uwanta ba. Lokacin data haifi ‘Danta na fari! sosai Mahaifinta ya gatantata daki guda aka cika mata da kayan barka, shi kuwa maigidan mota guda ta kayan abinci ya sauke masa, aikuwa Ramtalu ta samu abunda take so shiga take tana fita tana sakin habaici da gori! Cewar da abincin ubanta mutum ke rayuwa sannan kuma da tufafin ubanta mutum ke tun’kaho! Allah Sarki Sakina kishiyarta tasan da ita take, sai ta shiga daki taci kunanta ta koshi kuma ta dauki aniya kan cewar idan mijin nasu ya dawo zata fada masa abinda ke faruwa a gidan dan gaskiya ita ta gaji da wulakancin da matarsa keyi mata, gabadaya ta lura Ramlatu bata san mutunci ba ba kuma tasan mai kyautata mata ba, tunda ta haihu take hidima da ita ta kasa zama ta hutu kullum a tsaye take amma babu sannu bare nagode kullum cikin fada mata bakar magana take to gaskiya ta gaji hakurinta yazo karshe kudi ai ba hauka bane. Maigidansu na dawowa bayan yaci a binci ya huta sai ta shiga fada masa abubuwan da suke ta faruwa a gidan wanda shi bai san dasu

ba, tabbas ransa ya ‘baci sosai kuma ya sheda halin matarsa Sakina tana da hakuri sosai da kawaici ba zata takali Ramla da rigima ba duk da cewar itace Uwargida amma ta hakura da komai burinta ta kawo zaman lafiya da daidaito a gidin! Yace.”Kiyi hakuri insha Allahu zan sameta nayi mata fad’a amma kada irin haka ta sake faruwa kiyi shuru da bakin ki duk abinda ke faruwa tsakanin ki Ramla ki sameni ki fada mun zanyiwa tufkar hanci.” Tace.”To insha Allah.” Lokacin da ya shiga dakin Ramlatu tana zaune gefan gado taci uwar kwaliya da less an turo dauri gaban goshi kana kallonta zaka fahimci ‘Yar Alaji ce hannunta da kunnata gami da wuyanta duk Gold ne sai walwali take…Zama yayi kusa da ita ya mika hannu ya kar’bi yaron dake hannunta da ta gama bashi nono ya tofa masa addua kana ya kwantar dashi ya fuskanceta…….Babu cikakkiyar walwala a tare dashi yace.”Yanzu Ramlatu abinda kikewa Sakina a gidan nan ya dace.”!? Wani irin shan kunu tayi ta kumbura fuska tace”Me nayi mata ashe! zaunar da kai tayi tana fad’a maka karya da gaskiya ko.”? Yace.”Abinda Sakina za tayi nasa ni haka kuma abinda Ramla za tayi nasa ni dukkanin ku nasan halin ko wacce ba wai ina so nace Sakina tafi ki a gurina ba A’a dik matsayin ku d’aya a zuciyata, amma ki sani abinda kikewa abokiyar zamanki bai dace ba! wace iri ce ke mai manta alkairi? menene Sakina ba tayi miki ba, ina cewa gabadaya sai da kika daina girki sai dai ta dafa ta kawo miki har d’aki kuma hakan bai hanaki kwana da miji ba! idan muguwa ce ai zata hanaki ki kwana dani ba tunda itace take girki amma ta dafa ta baki kici kina kwance kuma ki rasa sakayya da zaki mata sai irin wannan.”!! Fashewa tayi da kuka tace”Shikkenan to ai ba sai ka futo fili ka nuna kafi kaunarta a kaina ba, amma meye haka daga zuwa babu tambayar ba’asi sai ka kama wasu maganganu ai bani ce nace tayi min girki ba ita taga zata iya ta dauka tayi ni ba burgeni tayi ba, kuma koda ba tayi min girki ba zansa a turo mai aiki daga gidanmu tazo ta kula dani har na haihu.” Yace.”Ni dai na fad’a miki wallahi duk sanda kika ‘kara ci mata fuska ko kikayi mata gori kan wani abu da aka kawo shi gidan nan sai ranki ya ‘baci!! Cikin ‘bacin rai tace”To ai shikkenan tunda uwata ce ita sai na kwanta ta takani saboda tana da daurin gindi a gurinka, akan me? kai da ita kuna cin arzikina amma kuma kuce sai nayi muku biyayya wallahi ba zai yuwu ba.””! Takarasa maganar tana buga cinya.”! Cikin fusata yace.”Zanyi maganin ki ai shashasha mara tunani meye abinci da kike gori a kansa, meye kuma tufafi wanda zasu lalace su barki da mutum! to zanje na samu Alajin da kaina zan fad’a masa bana bukatar k’wayar abincinsa a gidana ko ya aiko

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MADADI CHAPTER 1

MADADI CHAPTER 3