in

MADADI CHAPTER 16

MADADI CHAPTER 16

Bangaran Najaatu kuwa da tayi alkawari kan cewa babu inda za taje, sai kuma daga baya tayi wani tunani tayi sauri tayi shiri na mussaman ado da kwalliya tayi mai k’ayatarwa ta fito falo tana zabga kamshi turarruka masu kamshi da daukar hankali… Nan ta samu Ya Ramlatu da wasu daga cikin Family din Hajia suna zaune ta gaisa dasu a mutunce! Ta kalli Ramlatu da fad’in.” Ba yanzu zamu tafi bane.”? Ya Ramlatu tace”ko kawai kibi hajia Rabi ku tafi kada rana tayi ni zan jira zuwansu Hajia Rakiya sai mu had’u gabadayanmu mu biyo bayanku. Tace”To shikkenan, sama ta hau tayi sallama da hajia ta sauko Ya Ramlatu tace” Daddy tunda yay bacci a bayana to ki barshi kawai na tawo dashi. Tace”Kada fa ya tashi yayi miki rigima irin na jiya. Dariya ta d’anyi tace”Ba zai tashi ba insha Allah ai su Hajia Rakiyan suna hanya muma ba zamu dade ba zamu biyo bayanku. Tace to shikkenan sai kin tawo. Naja’atu tana sane ta yafa qaramin mayafi mara sirri ga yanayin dinki jikinta riga da siket sun matseta swiss les ne mai tsada amma tasa anyi mata matsatstsan d’inki! tana sane tasa kayan saboda tasan baya son suyi irin shigar su fita da ita.. Taji dadin ganin dukk motocinsa a harabar gidan da alama bai futa ba, kai tsaye bangaran maijego suka nufa…..’Yan uwanta ne duk a gurin suka gaisa a tsaitsaye suka wuce ciki. Zainab tayi kyau har ta gaji kana ganinta kaga matar Alhaji gold yaji a ko’ina ga wata uwar shadda tasa wacce taji uban surfani irin na manyan mata…Najaatu kallo daya tayi mata ta dauke kanta, kishi ne yake taso mata tana danneshi…To itama Zainab din nata bangaran ganin zahirin Najaatun ya firgitata jikinta yay sanyi dan bata ta’ba tsammanin cika da kasaitarta ya kai hakaba ashe cikakkiyar macace abar alfaharin ko wane da namiji lallai hijabi ba karamin sururta mace yake ba. Ta dinga satar kallon Najaatun tana jin wata shakkarta gabad’aya bata so ta had’u da mijinta dan kada ya ‘kyasa (Maman Hanan kinga mutuniyar ki ko 😹 sai kace tsinken sakace sai iyayin tsiya) Najaatu na hankalce da irin kallon da take mata sai kawai ta miqe da fad’n “Hajia bari na shiga gurin Aunty Halisa mu gaisa. Hajia Rabi tace” To shikkenan nima zan shigo yanzu insha Allah.” Najaatu ta juya tana wata iyar tafiya ta taqama! Zainab kasa dauke idonta tayi daga kanta har ta fita daga dakin. Da sallama a bakinta ta tura kofar falon ta shiga, Abbah Abbas na tsaye a tsakiyar falon yana magana da Saddiqa Halisa kuma na zaune a kan kujera tayi ado daidai misali Mussadiq da Mufida na kusa da ita a zaune. Ganin shigowarta yasa yaran suka ruga a guje suka rungumeta suna murna…Halisa na murmushi tace”Najaatu ke kika fara zuwa kenan sannu da zuwa karaso ki zauna. A nutse ta riqe hannun Mussadiq suka karasa falon ta samu guri ta zauna a nutse ta kalleshi yana tsaye a inda yake yana mata wani irin kallo mai kama da harara ita tasan ko kallon menene sai ta basar tace”Abbah ina kwana? ‘kin amsawa yay ya kalli Saddiqa da fad’in ta tashi maza taje gurin Zainab tace ta duba masa gilas d’insa a dakinta, Saddiqa tayi saurin miqewa domin tafiya aiken da yayi mata, Najaatu ba tayi zuciya ba ta sake gaishe shi, a dakile ya amsa ya bar gurin… murmushi kawai tayi ta juya suka cigaba da magana da Halisa…… 79******Halisa na murmushi tace” Ya kuma naganki a haka ina kika baro maigidan nawa.”? Tace”Yana goye a bayan Yaya Ramlatu lokacin da zamu tawo yana bacci shine tace na kyaleshi kawai ta tawo dashi.” Halisa tace” Ayya amma kin shiga gurin maijegon ko.”? “Eh Hajia Rabi ma can na baro ta.” Shuru falon yayi kowa yana tunani a cikin ransa……Kamshin turaransa ne ya sanya dukkaninsu suka dago kai suna kallonsa, Najaatu kallon sharia kawai tayi masa tayi kasa da kanta tana jin wani irin yanayi a jikinta, a duk lokacin da zata kalleshi sai sonsa da kaunarsa sun sake karuwa a cikin zuciyarta, Abbah Abbas kwata kwata baya tsufa kullum kara masa kuruciya ake babu wanda zai kalleshi yace yayi shekara hamsin a duniya saboda shi mutum ne dan gayu mai kula da kansa, Yanzu ma yayi ado cikin wani had’addan filtex irin na maza dark blue abinka da farin mutum sai yayi masa wani irin kyau, hula mai farin zanen zare yay amfani da ita, kafarsa sanye da takalmi sau ciki baki sai shaninig yake, farin gilashin da yake sakaye a idonsa yayi masa masifar kyau, Najaatu ta dinga jin wani irin

sanyi na ziyartar jikinta sha’awarsa ce take taso mata a jikinta sai ta shiga tunawa da irin zazzafar soyayyar da ya dinga nuna mata a lokacin da suke tare…….Muryarsa taji yana magana…”Yau ma kin bar yaron nan a gida ko ashe ke ba’a isa a fad’a miki magana guda kiji ba? yanzu meye amfanin saka wannan mayafin na jikinki da kin sani kin yar dashi a hanya dan bashi da wani amfani tunda gashinan a zahiri komai na jikinki ana gani. Shuru tayi ta kasa magana ba wai dan bata da abinda cewa ba kawai tana ganin kamar shurun shi yafi amfani saboda gudun kada ta fada masa wata maganar yace tayi masa rashin kunya. Halisa tace” Ni sai nake ganin ai ba wani abu bane dan ta bar yaron a gurin Yaya Ramlatu tunda yanzu zasu zo maganar hijabi kuma ka ajiyeshi a gefe yau daya dan tasa mayafi ai ba laifi bane tunda bata da nauyin kowa a kanta kuma ni wallahi banga abunda mayafinta ya nuna ba. tana yar dariya ta karashe maganar. Yace.” Ni na gani ai tunda ke baki gani ba, sannan ni nasan tana da wata munufa ta yafa mayafin tunda keda ita duk kun san bana son irin wannan mayafan marasa sirri saboda haka idan zaku tafi ki kar’bi hijabi gurin Halisa ki suturta jikinki baki burgeni ba idan dani kikayi…….Halisa tace”Ikon Allah shikkenan sai tayi kwalliya dan kai kad’ai bazawara ce fa kuma kowa yasan zawarawa da ‘yan mata gurin ado da kwalliya me zai sanya ka damu kanka…..Yace.”Ai shine abinda nake so ki fahinta ta bud’e tsaraicinta ne dan ni ko wani a waje ya gani yaji sha’awa to ni duk irin wannan basa burgeni.” Jin abinda yake cewa ne yasa tace”Haba Abbah yanzu dan Allah ina tsaraici anan.”? Tafada tana cire mayafin jikinta tare da gyara zamanta a kan kujerar. Saurin dauke kansa yay sakamakon ganin tudun nonowanta da suka fito ta saman riga…..Aunty Halisa tace”To nima dai haka na gani wallahi.” Najaatu ta cigaba da cewa”Wallahi ni banyi kwalliyata dan kowa ba dan kaina nayi kuma Aunty Halisa ni bazan fitar da tsaraicina saboda na samu mijin aure ba saboda nasan ko yanzu na bukaci aure zanyi tunda ni nasan kaina ba k’aramar mace bace.” Halisa ta dinga dariya tana kallonsa yana tsaye yana kallonsu, kowa dai yay zagi a kasuwa yasan da wanda yake, shuru kawai yay musu ya zauna kan kujera mai cin mutum daya, agogon hannunsa ya duba, ya kalli Mussadiq dake fama da game yace”Jeka gurun Zainab kace tazo amma tazo da baby Ummi.” Yaron ya ajiye game din da sauri ya tafi aiken da akai masa. Abbah shuru yay yana jin Halisa na fad’in “Najaatu kin birgeni wallahi ai dama nace ke ba k’aramar mace bace koda baki sa mayafi ba ya kasance kullum a cikin hijabi kike na tabbata ba zaki rasa miji ba haba ai ido ba mudu ba yasan ‘kima.” Shiru yay bai tanka ba dan ya lura Halisa naso ta tona masa asiri a gurin yarinyar shiyasa yaja bakinsa yay shuru ya shiga girgiza kafafunsa….Halisa kallonsa take a fakaice tana ‘boye dariyarta ita wallahi idan yana muzurai a kan rashin gaskiya dariya yake bata wai shi lallai ba zai fito fili ya nuna cewar ya damu da yarinyar ba alhalin duk gashinan ya nuna alama a zahiri kowa ya gani. Zainab ta shigo falon rugume da ‘yarta ganin Halisa da Najaatu na hira cikin fahimtar juna yasa taji haushin hakan, dauke kanta tayi ta nufi gurun mijinta….Baby Ummi ya kar’ba daga hannuta ya rungumeta a gefan hannunsa na hagu sai ya janyo zainab din ya d’ora a cinyarsa, ya rike kungunta da hannunsa na dama wayarsa ya bata yace tayi musu hoto…….Wannan al’amari ya duguzunma zuciyar Najaatu da Halisa ba kamar najaatu da taji gurin na juyawa da ita, Ita kuwa Halisa d’aga murya tayi tace”Me yasa ba kaje can gurinta kunyi hoton ba ai ina ganin kamar hakan sai yafi armashi.” Yace.”Akwai jamaa a gurun ne ko banda ikon nayi abinda nake so a inda na gada dama.” Ta’be bakinta tayi tace”Aa kayi komai babu damuwa ai.” Ya kalli su Saddiqa da fad’in su taso suzo gurinsa, yaran suka kewaye shi Zainab na zaune daram! a cinyarsa tana ta daukarsu a hoto farin ciki kamar ya kasheta hakika tayi farin ciki da yanda ya nuna musu cewa ita mai muhimanci ce a rayuwarsa, in da shi kuma anasa bangaran da biyu yake haka duk dan ya cuzguna musu, aikuwa ya hango tsantsar kishi da tashin hankali a idanun Najaatu dan har ja idanunta sukayi saboda tsabar bacin rai da takaici……Sai da suka gama dauke dauke hotonsu sannan yazo inda suke zaune da yake duguwar kujera ce sai ya shiga tsakaninsu, Najaatu kamar ta miqe ta bar gurin haka taji sai dai ta daure ta matsa gefe saboda jin yanda ya takureta….Baby Ummi ya kar’ba ya riqe yasa su Saddiqa suka shigo kowa ya tsaya, sannan ya umarci Zainab din ta daukesu, hakan be mata ciwo ba saboda tasan ita ya fara nunawa muhimanci…..Zainab tayi musu kusan biyar ta miqa masa wayar, tare da fad’in “Zata koma gurin ‘yan uwanta! Babyn ya miqa mata tare da fatan a tashi taro lafiya…..Ta ‘karbi ‘yarta ta tafi ba tare da ta kula kowa a gurin ba…..Shima tana fita ya miqe daga tsakiyarsu ya kama hanyar futa, babu wanda ya kulashi sai yaransa sune sukayi masa adawo lafiya. Ya amsa cike da walwala da farin ciki yasan yau da Halisa Da Najaatu dukkaninsu ba zasu yini cikin farin ciki ba, wato harshi zasu sa a gaba sunawa dariya sun mayar dashi sakarai shiyasa yay musu haka. bayan fitarsa Najaatu mamaki take sosai da yanda Halisa tayi sanyi yanzu gabadaya ta mayar da rayuwa ba wani abuba, idan da lokacin baya ne ai bai isa yayi mata irin wannan rashin kyautawa a falonta ba gaskiya kamar da akwai cin fuska a ciki sai taga kamar ma ita ta fita jin haushin al’amarin amma dai yanda ta dauke kanta daga kan abunda yayi yasa taji ta burgeta mutuka Taron sunan Zainab yayi kyau ya kuma k’ayatar anci ansha maijego ta fito sosai dan sai da tayi shigar kaya kala goma cikinsu duk babu na yarwa abunda yay musu cikas kawai rashin Dan Asharrale amma dai duk da haka ba suyi bikin Lami ba sai da suka saka (Mp) mai kid’an tsiya suka dinga jin wakokin *Gwanja* suna cashewa sai rawa suke suna murguda mazaunai

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MADADI CHAPTER 15

MADADI CHAPTER 17 KARSHE