in

MADADI CHAPTER 15

MADADI CHAPTER 15

Cigaba sukayi dayi mata taimako irin na gida, cikin ikon Allah ta dinga wani irin yunkuri kamar wacce zata sake sabuwar haihuwa mahaifar ce ta fad’o kafin wani uban jini ya biyo bayanta. Gabad’ayansu suka shiga godewa Allah dan ganin yanda ya gajarta musu wahala basu sha wahalar zuwa asibiti ba amma a zahirin gaskiya haihuwar tazo da tangard’a! amma dai tunda Allah ya raba lafiya sai su gode masa……..Kafin gari ya waye komai yayi tsaf! Hajia Rabi da Yaya Ramlatu sun gyara maijego da babynta mai kama da ubansa, dakin yayi tsaf dashi sai qamshin turaran wuta yakeyi…..Da Asubah Hajia ta sanar da Alhaji haihuwar ya dinga murna da farin ciki yana Allah Allah a idar da Sallar ya sanar da Mahaifin yarinyar, to shima Malam yayi farin ciki dajin cewa yarinyar shi ta haihu cikin koshin lafiya, cike da farin ciki ya shiga gida domin ya sanarwa da matarsa halin da ake ciki. Yaya Ramlatu itake tsaye a kan Naja’atu da yaronta dan da gari ya waye ma itace tayi wa yaron wanka ta shiryashi cikin kayan sanyi sannan ta kai Naja’atu toilet ta gasa mata jikinta sosai tasa ta ta zauna a cikin ruwan d’umi! Naja’atu ta dinga mamakin irin dawainiyar da Ramlatu keyi mata ko a mafarki bata ta’ba tunanin hakan na iya faruwa ba. Kafin takwas na safe Naja’atu tasha gayu tayi kyau tamkar ba ita ba, Ya ramlatu ta taimaka mata ta shirya jikinta cikin wani Swiss les mai kyau! Hajia kuwa da kanta ta shiga kicin tayi mata abun kari na mussaman sannan ta zauna a kusa da ita sai data tabbatar da taci ta koshi tukkuna ta fita daga dakin……Bayan kowa ya gama shige da ficensa a dakin, Naja’atu a hankali ta kai hannu inda yaron yake ta daukoshi ta riqe a hannunta, tsira masa ido tayi kawai tana kallonsa, yaron kamar sa daya da ubansa tamkar Bash yayi kaki! ya tofar, wasu irin hawaye ne masu zafi suka shiga zobo mata, wai yau itace ke dauke da d’an Bash a hannunta, ashe dai sai ta fara haifawa Bash d’a kafin ta haifawa Abbah Abbas, gabanta ne ya fad’i Data tuna irin kauce kaucen da Abbah Abbas din ke mata, to yanzu dai gashi ta haihu lafiya kome zai biyo baya oho! itakam idan Abbah bai mai da ita gidansa ba to tana jin ita da aure har abadah! Hawayen take sharewa wasu na sake kwararowa, cikin wannan halin ya shiga dakin ya sameta. Bata san ma ya shigo ba sai qamshin turaransa ne ya sanar mata shigowar tasa, da sauri ta dago kanta tana kallonsa suka tsirawa juna ido………Dauke kansa yayi daga kallonta cikin nutsuwa ya zauna gefanta tare dasa hannunsa ya kar’bi yaron yana dubashi. Tausayinsa da tsantsar kaunarsa suka sake karya mata zuciya sai kawai ta dukufar da kanta ta cigaba da rera kuka wanda na rasa ko na menene! Abbah bakinsa yasa kunnan yaron dama da hagu yayi masa kiransa sallah sau uku sannan yasa masa kalmar shahada duk dai a kunnuwan nasa ya d’ago kanshi cikin nutsuwa ya tsirawa fuskar yaron ido……….Hausawa sukace labarin zuciya a tambayi fuska ni kaina a lokacin dana kalli fuskarsa sai dana tausayawa masa, dan kallon fuskar yaron tasa yasa ya tuno da abubuwan da suka shud’e yana tunanin da Naja’atu na gidansa da tuni wannan yaron dake riqe a hannunsa nasa ne, kallon fuskar yaron tasa ya tuno da fuskar ubansa duk da sau daya ya ta’ba ganin Bash amma baya ta’ba tunanin zai mance kammaninsa, Tamaza! yayi yayi saurin aro dauriya da jarumta ya kalleta tare da fad’in “Sannu ina fatan babu abunda ke damunki.”! shuru tayi masa ta kasa magana saboda kukan da yaci karfinta Gyaran murya yayi a nutse ya kira sunanta.” Naja’atu.” Dago kanta tayi tana kallonsa hawaye na sake zubowa, “Kukan me kikeyi bayan Allah ya sauke ki lafiya ai sai ki gode masa.” Murya na rawa tace”Abbah tausayin ka nake ji wallahi dan Allah ka gafarta min abunda nayi maka wallahi ban zubar maka da ciki ba.” Kawai sai ya tsaya yana kallonta, Kafin yayi murmushi ya dan sunkuyar da kansa yana nazarin maganarta, wai tausayi shi maganar ma dariya ta bashi Yace.”Cikina daya zube a jikinki dama haka Allah ya hukunta, maganar tausayi kuma ki daina nima na kusa samun k’aruwa ko baki da labarin amaryata nada ciki.” Yafad’a yana kallonta ido da ido Sai taga maganar tasa kamar akwai cin fuska a ciki, a sanyaye tace”Na sani Allah ya rabasu lafiya.” Ya amsa da ”ameen ya Allah Wane suna kike so a sakawa yaron ki.”Da sauri ta kalleshi, yace.”Eh inaso nayi masa hud’uba ne kafin na tashi. Tace”Ko wane suna asa masa. “A’a kina da ikon ki za’bi sunan da kike so a saka masa dan haka ki duba dai. Kai tsaye tace” Kasa masa sunanka tunda a yanzu kai ka zame masa uba.” Girgiza kansa yayi yace.”Kece ‘Yata shi wannan sai dai a kirasa da jika na, dan haka ba sunana ya kamata a saka masa ba na Malam za’asa masa ko kuma a saka masa sunan babansa Bashir.” Da sauri tace”Abbah dan Allah kada kasa masa sunan wannan mugun mutumin azzalimi wanda ya kwashe kayansa daga gaban ma’aiki, ni sunanka nakeso kawai kasa masa. Yace.”Ki daina tsine masa kina kwashe masa albarka yana a matsayin uban danki sannan ita shiriya ta Allah ce watakila Allah ya shiryeshi ya dawo ku daidaita kanku……..Fad’ar wannan magana da yayi sai ta sake tunzura ta dinga zazzagin Bash din tana tsine masa albarka da fadin Sai dai ta mutu babu aure akan ta koma gidan Bash har da cewa insha Allahu ba zaiga annabi ba. Abbah da kyar ya sata tayi shuru a maimakon ta tsaya ta cigaba da sauraran nasihar da yake mata kawai sai ta kwanta ta juya

masa baya zafafan hawaye na zubo mata Yaron ya ajiye mata a kusa da ita ya fita daga dakin yana mamakin al’amarin…..Kafin ya tafi harkokinsa sai ya tsaya ta tambayi hajia ko da akwai abinda ake bukata, hajia ta fad’a masa duk abinda ake bukata yace insha Allahu zai turo yaronsa Aikuwa wajejan sha biyu na rana Abdulhamid ya kawo uban naman rago gami da kaji gyararru da kayan tea da uban cefane mai yawa………..A take Hajia ta umarci Yaya Ramlatu data taimakwa Jummai mai aiki da suyi wa Naja’atu miya irin ta masu jego. Sai bayan la’asar iyalin Abbah Abbas suka sauka a gidan dukkaninsu har da yaran tinda washe garin ranar haihuwar jumaa ce sun taso daga makaranta da wuri yaran sai murna sukeyi zasuje suga d’an jinjiri……To bayan sun gaisa da hajia kai tsaye dakin da maijego take suka nufa…Naja’atu da aunty Maryam suna hira sukaji sallamarsu, halisa kamar ba itaba ta karasa cikin dakin da faraa a tare da ita take fadin”Lallai haihuwa da lafiya abar alfahari ce gaskiya na taya ki murna naja’atu Allah ya raya ya baki lafiya.” Aunty maryam ta amsa da ameen tana miqa mata yaron, Halisa ta karba tana dariya kamar ba itaba suka gaisa da Aunty maryam din cikin sakin fuska, aunty maryam ta dinga mamakin al’amarin, Zainab kuwa sai dauke kai take tana ya mutsa fuska, aunty maryam tace “Sannu uwar biyu kema ai kin kusa Allah dai ya raba lafiya.” A hankali ta amsa da “Ameen.” Najaatu ta dan kalleta na minti biyu ta kau da kanta ta rasa me yasa gabad’aya Zainab din ke bata haushi iyayinta shine abinda tafi tsana a tare da ita Halisa ta gama duba yaron ta miqawa Zainab da fad’in ”Gashi ki daukeshi kema kisa albarka.” Zainab ta ya mutsa fuska da fad’in aunt Halisa bana iya daukarsa ni kai dai nasan abunda ke damuna Allah yasa masa albarka.” Babu wanda yaji dadin abinda tayi ai ko yaya ne ta daukeshi koda kuwa bata jin dadin jikinta…Naja’atu taji haushi sosai sai dai ta bawa zuciyarta hakuri ta cigaba da amsawa Halisa maganar da suke……Su Saddiqa ne suka shigo dakin suna murmushi. Aunty Maryam tace”Yawwa dama tun dazu ‘kaninku yake neman ku da har yayi fushi na bashi hakuri.” Da sauri mussadiq ya karasa kusa da Halisa yana dariya yana leqa fuskar yaron, Halisa tace zauna nasa maka shi a jikinka. Ya zauna da sauri tasa masa yaron ya rungumeshi su Saddiqa na leqen fuskarsa! Aunty Maryam ta kalli Mufida da fad’in “Albishirin ku.” Mufida tace”Goro.” Aunty maryam na dariya tace”To dai yaro yaci sunan Abbanku dan sunan da mamansa ta za’ba masa kenan.” Ai gabad’aya sai yaran suka shiga murna da farin ciki Halisa na ‘yar dariya tace”To ikon Allah ashe sunan maigida aka saka masa gaskiya dole na fito da kyau ranar suna.” Aunty Maryam ta dinga dariya tana fad’in “Aikuwa hakan nada kyau. Zainab kamar ruwa ya cinyeta a dakin tayi d’if bakin ciki kamar ya kasheta jin wai sunan mjinta ta sakawa yaronta yasa ta sake jin wani sabon kishi na taso mata….Gabadaya zaman dakin ne ya gundureta mutukar zata waiwaya ta kalli Naja’atu shar da ita tana dariya da farin ciki to ji take kamar zata mutu saboda bakin ciki….Miqewa kawai tayi ta kama hanya fita, dukkaninsu suka bita da kallo har ta futa babu wanda yayi mata magana a cikinsu…..To aunty maryam dai da Halisa ba yara bane dukkaninsu sun gane abinda ke damun yarinyar itama Naja’atun taso ta fahimci wani abu kawai ta share abun ne dan a zauna lafiya amma zahirin gaskiya irin halin ko in kulan da Zainab ke nuna mata yana yi mata ciwo. Zainab falo ta fito ta zauna ita kadai abun duniya ya isheta, ita kuwa Yaya Ramlatu sai shige da fuce takeyi a tsakanin Dakin maijego da kicin tana sakin habaici ga Zainab din(😅 mai hali baya fasa halinsa hausawa suka ce idan ka kwana biyu ba kaga mutum ba to kana ganinsa ka fara tambayarsa halinsa) Zainab muzanta tayi kwarai da gaske sai ta shiga data sanin fitowa falon , sunkuyar da kanta tayi kuka na kokarin kufce mata….Yaya Ramlatu bata qyale Zainab ta sarara ba sai da taga hajia ta sakko tukkuna ta rabu da ita. Har yamma suna gidan aunty maryam kuwa ganin yamma tayi yasa tayi musu sallama ta tafi gidanta……Halisa da Zainab suka zauna jiran zuwan mijinsu domin haka yace su zauna su jirashi idan yazo sai su tafi tare…..Daf da magariba Abbah da Abbah magaji suka shiga gidan Alhajin Abbah Abbas da kansa ya jagoranci Abokin nasa

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MADADI CHAPTER 14

MADADI CHAPTER 16