in

MADADI CHAPTER 14

MADADI CHAPTER 14

Sajida sukayi sai hankalinsu ya kwanta suka daina kuke kuken da sukeyi…Abbah ya bude mota ya shiga minti biyu ya fito hannunsa ri’ke da kudi yan dubu dubu sun kai talatin ya miqa wa Naja’atu da fad’in ta basu.” motar ya koma yana zauna yana qoqarin tashinta…..Mmn Sajida ta rungume Naja’atu tana zirarar da hawaye da kyar ta saketa Mmn Ladi ma tazo ta rungumeta sukayi sallama cike da alhini da damuwa Naja’atu ta bud’e mota ta shiga, suna tsaye a gurin suna daga musu hannu har sai da motar ta ‘bace daga gurin…..Sannan suka juya da mataccen jiki, Mmn Sajida hada ido sukayi da Dantalle daya zubo mata ido yana kallonta shima tamkar yayi kuka! Yarinyar da yake qulafuci ashe ba tsararsa bace, yaso ya yaudareta da kudi da kayan kwadayi ya biya bukatarsa sai ya lura ba wannan ne a gabanta ba, sai yanzu ya qara tabbatar da cewar yarinyar ‘yar manyan mutane ce ganin motar da’a kazo d’aukar ta yayi masifar sanyayyar masa da jiki da duk wani wanda yake mata kallon banza a gurin.. Abbah gabad’aya hankalinsa nakan driving din da yake sai dai kiraye kirayen wayar da yake shigowa wayarsa shine yake so yasa masa rashin nutsuwa a qalla an kirashi yafi sau ashirin bai daga ba, yasan dai labarin gizo baya wuce na’ko’ki duk wanda zai kirashi a yanzu zaiyi masa jajen abinda ya sameshi ne, wannan dalilin yasa ya’ki daga wayar kowa kawai ya mayar da hankalinsa kan driving din da yake…….Naja’atu kanta a qasa nauyi da kunya gami da nadama ya hanata kwakkwaran motsi! a duniya ita kuwa tana da masoyi wanda ya kai Abbahnta kuwa? Wai tambayar kanta takeyi….(To nima dai a ganina baki da masoyin daya wuce shi) Taji wasu hawayen na kokarin kwace mata data tuna zalintar kanta da tayi, yanzu data hakura ta zauna da auransa da tuni tana zaune hankalinta a kwance, da tuni ma wannan cikin dake jikinta nasa ne zata haihu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ba tare da fargabar abinda ka iya zuwa ya dawo ba, yanzu ya za tayi da d’an Bash idan ta haifeshi? wane namiji zata aura wanda zai ri’ke mata d’anta! hawayen da take ta kokarin dannewa suka shiga zuba a kumatunta…..Inama ace ana dawo da abinda ya wuce a baya data gyara kuskuranta, ita da kanta tasan ta aikata kuskure mai muni wanda har ta mutu ba zata daina nadama ba…………..Wayar da yake ce ta dawo da ita hayyacinta. “Halisa bana gari a halin yanzu ku kwantar da hankalinku dukkanin abinda ya faru da sanin Ubangiji na samu labarin komai bayan tafiya ta jos wuta ta cinye d’aya daga cikin rumfunana to bana mamaki da ikon Ubangiji da kuma abinda ya saukar a kan dukiyata, kada ku manta shine ya bani ita lokacin da banyi tsammani ba, nasan idan yaga dama zai mayar min da abinda na rasa cikin lokaci kankani babban farin cikina wutar bata ta’ba kowa ba shine abinda yafi komai faranta min rai! Dukiya a duniya na sameta kuma anan zan tafi na barta to banga abin tashin hankali ba, kuma ba wai gabadaya abinda nake dashi ne ya ‘kone ba akwai kaya masu yawa a sauran rumfunana ina da kudi a banki wanda ban san yawansu ba to me zai sanya na kasa tawakalli dan Allah ya zartar da ikonsa, inaso dukkaninku ku kwantar da hankalinku kuyi addua akan Allah yasa haka shi yafi alkairi.” Halisa jikinta yayi sanyi tace”To shikkenan gabad’ayanmu ma muna gidan Alhaji kowa hankalinsa ya tashi gashi babu wanda ka fad’awa inda kake sai da Salim ya dawo yake fad’a mana wai tun misalin biyu na rana ka tafi jos dauko Naja’atu.” Yace.”Eh nayi haka ne saboda wani dalili nawa amma yanzu gamu a kan hanya nida Naja’atun insha Allah kafin gari ya waye zamu sauka.” Halisa a sanyaye tace”To Allah ya saukeku lafiya.” Ya amsa da ameen tare da kashe wayar tashi gabadaya. Halisa a sanyaye ta shiga sanar dasu Hajia abinda yace mata Zainab ta cika ta batse sai haushi takeji kishi kamar ya kasheta, akan me zai tafi dauko Naja’atu ya bar iyalinsa ai bashi ne yake da alhakin daukota ba tunda iyayenta da dan uwanta suna raye shi meye nasa, zainab sosai take kishin naja’atu dan Halisa bata gabanta tunda lura kamar ta tashi daga aiki……..Naja’atu a sanyaye ta kalleshi tace”Abbah wani abu ya faru da kaine naji kamar kana maganar gobara.” Ba tare da ya kalleta ba yace.”Eh bayan na dauko hanya da niyyar zuwa nan sai al’amarin ya afku wuta ta cinye babbar rumfata dake cikin kasuwa.” Jikinta yayi sanyi sosai tace”Allah ya mayar maka da alkairi Abbah Allah ya sadaka da rabo mai amfani.” Yaji dadin adduarta sai ya amsa da “ameen ya Allah nagode sosai.” motar tayi shuru kowa na tunane tunane a cikin zuciyarsa, Abbah Abbas sosai yake gudu kan kwalta dan gabad’aya ba yaso su kwana a hanya dalilin da yasa kenan ya kashe dukkanin wayoyinsa ya mayar da hankalinsa guri guda…….Sai gefin asubahi suka shigo garin kano a lokacin Naja’atu ta dad’e dayin bacci dan da yaga tana gyangyad’i sai tsayar da motar ya umarceta da ta koma bayan motar ta kwanta, Lokacin da ake kokarin shiga massalaci domin gabatar da Sallah asubahi yayi parking din motarsa a kofar gidan mahaifinsa, Allah ya godewa kafin ya bude motar ya fito da sauri ya nufi masjid din dake jikin gidan Alhaji, yana kokarin shiga massalacin Baba malam shima na kokarin shiga, sai sukayiwa junansu sallama suka shiga massalacin a tare, baba malam ya wuce ciki shi kuma ya tsaya bakin famfo domin daura alwala…..Naja’atu tun bayan fitarsa a motar ta tashi zaune tana muzarai gami da kalle kallen jama’ar dake shiga massalaci a gaban idonta Baba malam ya fito daga gida ya shiga massalacin ta dinga jin faduwar gaba da wani irin

tsoro gami da kunya da nadama na damunta yanzu da wane ido zata kalli iyayenta da sauran jama’ar gari?……………… 64*********Ta jima zaune a cikin motar kafin ta yanke shawarar budewa ta fito a hankali tana waige waige, gidan alhaji ta nufa domin bata tunanin zata iya shiga gidansu dan bata san irin kar’bar da mahaifiyarta za tayi mata ba. A sanyaye ta tura kofar palon hajia ta shiga da ‘yar karamar sallama a bakinta, shuru palon babu kowa sai dai tana d’an jin motsi gami da magana sama-sama a dakin data zauna kafin auranta da Bash, A sanyaye ta zauna kan kujera tana takure jikinta ta kai minti goma a zaune babu wanda ya fito hajia na sama su kuma su Halisa da yaran na cikin wannan d’akin babu wanda yasan da shigowarta, ganin gari ya soma haske yasa ta yanke shawarar miqewa domin taje tayi sallah….Dakin dasu Halisa suke ta nufa tana tafiya salau salau wanda kana ganinta zaka fahimci karfin hali kawai take yi…….A hankali ta tura kofar dakin ta shiga da sallama a bakinta, gabad’ayansu suka juyo suna kallonta, Mussadiq ya miqe a guje yaje ya rungumeta yana tsalle da murna had’e da kiran sunanta duk ya cikwikwiye mata hijabin jikinta Mufida taje gurinta tana ta murna da farin ciki….Saddiqa kuwa tana zaune a inda take ba zaka tantance yanayin da take ciki ba….Naja’atu ta miqa mata hannu murya na rawa tace”Zo.” Saddiqa ta mayar da kwallar dake kokarin zubo mata ta miqe a nutse ta nufi inda take Zeey dake bacci sakamakon ihun! da Mussadiq yayi yasa ta miqewa zaune tana ‘bata ranta, tana kokarin yin magana Halisa ta fito daga toilet sai kawai idanunta ya sauka akan Naja’atu dake tsaye a bakin kofa ta rungume yaran sai hawaye take Halisa tace”Naja’atu dama ke suka gani suke wannan ihun? ni ina bandaki naji ihu ina addua Allah yasa ba fad’a suke ba ashe kece.” Tace.”Nice aunty Halisa ya kuke ina fatan na sameku lafiya.” Halisa babu yabo babu fallasa tace”Muna lafiya gabad’ayanmu.” Daga haka sai ta wuce ta dauki dadduma da hijabinta ta tayar da sallah…..Ita kuwa Zainab komawa tayi ta kwanta tana jan qaramin tsaki ita dai tana bala’in kishin Naja’atu mussaman yanda taga maigidanta gami da yaran sun damu ita. Tace”To kuje ku zauna nayi alwala nayi sallah sai mu zauna mu sake gaisawa.”suka samu guri suka zazzauna suna kallonta ta nufi toilet sai murmushin jin dadi suke…..Mussadiq kasa hakuri yayi cike da farin ciki ya nufi gurun Zainab yana fad’in “Auntymu ki tashi ku gaisa ga Yaya Naja’atun ta dawo daga tafiyar da tayi.” Zainab idanunta a rufe tace” Mussadiq bacci ne a idona idan na tashi a bacci zamu gaisa.” Yaron jikinsa yayi sanyi dan baiji dad’in abunba jiki a sanyaye yaje ya zauna kusa da ‘yan uwansa…….Ita kuwa Halisa bayan ta idar da sallar carbi ta shiga ja tana istigifari ga Allah(😅 Su Halisa an musulunta an koma ga Allah to Allah ya kar’bi tuban ta damu baki daya) Abbah Abbas da kyar ya samu kansa dan ana idar da sallah jama’a sukayi caaa! a kansa suna masa jajen dangane da qaddarar data fad’a masa a kasuwa kowa sai fad’ar albarkacin bakinsa yake, to shi dai magana d’aya yake fad’a cewa komai ya sameshi daga Allah ne yana rokon Allah ya kare dukkanin musulmi da mugun ji da gani…….Sai kusan bakwai da kwata ya samu ke’bewa dasu Alhaji nan ya tabbatar musu da cewar ya dauk’o Naja’atu daga inda take kuma tana cikin koshin lafiya kamar kowa sai dai maganar cikin jikinta ya sanya duk jikinsu yayi sanyi suka shiga cikin halin jimami daga bisani suka barwa Allah ikonsa domin kuwa duk abinda Allah ya zartar a kan bayinsa shine daidai, babu wanda yasan abinda Allah yake nufi dangane da faruwar al’amarin shiyasa gabadayansu sukayi wa yarinyar adduar sauka lafiya tare da adduar Allah ya inganta abinda zata haifa. Koda ya duba cikin motar yaga bata ciki bai damu ba saboda yasan bai kulle motar ba zata iya budewa ta shiga cikin gida……sai kawai ya nufi gidan Alhajin dan nan yake tsammanin samunta. Lokacin Naja’atu da yaran suna sama gurin hajia dan bayan tayi sallar jansu tayi domin suyi mata jagora zuwa gurin hajian masifar kunyar had’a ido take yi da ita shiyasa taja yaran domin su zame mata garkuwa. Magana yaji ‘kasa-‘kasa a cikin dakin dasu Halisa suke, sai kawai ya nufi dakin dan yaji kamar muryar Zainab na magana…….”Nifa aunty Halisa jikina yay sanyi wallahi anya kuwa Abbansu Mussadiq ba mayar da Naja’atun nan zaiyi ba? Kinga ni mahaifina malami ne amma ba malamin zaure ba malam ne mai fad’a akan abi sunna gami da dokokin ubangiji mu ba ma asiri da tsafi! amma tun kafin na auri mijinki muka samu labarin abinda ke faruwa ance shi wannan Baba malam din asiri yake yi ya asirce Alhaji dashi Abbansu Musaadiq din sannan kuma baya bari ‘ya’yansa su wulakanta kullum cikin aiko musu da asiri yake shiyasa da waccar matar tasa ta rasu aka dauki qanwarta aka maye gurbin ta! wallahi ganin yanda kowa yake rawar jiki akan Naja’atun nan yasa jikina ya mutu wani irin tsanarta nake ji a cikin raina.” Halisa ta ajiye carbin hannunta tana wani irin murmushi kai da ganinsa kasan na takaici ne tace”Zainab kenan to ni kam bansan abinda zance miki ba, tunda kin yarda da cewar Baba malam asiri yake sai kiyi takatsantsan da kanki kowa ya iya allonsa ya wanke ni yanzu duk ba wannan ne a gabana ba, maganar wai Abban Mufida zai dawo da Naja’atu gidanshi, ban sani ba, idan ma ya dawo da ita ni babu abinda ya dame ni ko wacce tata ta fishsheta.” Zainab tace”Aikuwa mu bama boka bama malam Allah kad’ai muka dogara dashi saboda haka banga asirin da wani boka zaiyi yayi tasiri a kaina ba.” Duk wannan maganganun a kunnansa, gaskiya yayi mamaki sosai! wai me yasa mutane suke hakane? duk wanda akaga babu ruwansa da duniya yana bin Allah sau da qafa sai a takura masa , tunda ya taso a unguwar kofar na’isa bai ta’ba jin wani yayi mummunar kalma akan Malam Sani ba, sai Halisa itace kullum ke kiransa da boka ko dan tsubbu to yau gashi an wayi gari itama Zainab tana kiranshi da wannan sunan duk kuwa da cewar ta fito daga cikin gidan da ba’a yarda da shirka da asiri ba gashi kishi yasa tana gazgatawa! duk akan ya tsaya a cikin al’amuran Naja’atu suke wannan surutan har suna zargin ko zai mayar da ita dakinta hmmmm! baya tunanin zai sake zaman aure da Naja’atu a yanzu duk wani abu da yake a kanta yanayi ne domin Allah da manzonsa da kuma lalurar cikin da take dauke dashi, Gyaran muryarsa ne ya dawo dasu hankalinsu, ya shiga dakin da sallama a bakinsa, Zainab da sauri ta riga Halisa magana tana wani irin murmushi na iyayi da kissa tace”Habibi sannu da zuwa ina fatan ka dawo lafiya.” ? Ba tare da yayi mata cikakken kallo ba ya amsa yana kallon Halisa da tayi qasa’ke tana kallon ikon Allah…Zainab ganin yanda ya amsa mata a banzace sai jikinta yayi sanyi tunda take dashi bai ta’ba yi mata irin hakaba. Halisa ta gaisheshi a nutse tana tambayarsa hanya ya amsa babu kyakkyawar walwala a tare dashi yace.”Waye ya baku izinin zuwa nan gidan ku kwana.”? Sai sukayi tsuru tsuru suna kallonsa domin duk cikinsu babu wacce take da hujja.” Halisa da yake tasan halinsa idan yana fushi ba’a katse masa hanzari sai taja bakinta tayi shuru…..Ita kuwa Zeey sarki karambani tace”Habibi Hajia ce tac…….Hannu ya d’aga mata da fad’in “Rufe min baki sarkin magana! Hajia ce tace me? kina so kiyi mata karya ko.”? shuru tayi tana girgiza kanta, Yace.”Dama ai so nake na dawo na tambayeki dalilin daya sa kika fitar da hannu kika mari Yaya Ramlatu ashe dama baki da kunya da tarbiya.”? Halisa cikin zuciyarta tace ” Anzo gurun. Zainab ta fashe da kuka tana kallonsa tace”Waye ta fada maka na mareta wallahi ni sharri akayi min yaushe ma zan mareta ba haba sai kace mara hankali itace fa kawai ta shigo gurina tana zagina amma ni ban mareta ba sai dai itace ma ta dokeni iya son ranta.” Yace.”Bakin daya fad’a min ba zaiyi min karya ba kin mare ta ko baki mareta ba.”? Zainab ta dinga rantse ranste ita bata mareta ba sai kuka take tana neman mafita…..Yana ‘kokarin yin magana hajia tare dasu Naja’atu suka shigo dakin…Ganin Zainab na kuka yasa hankalinta ya tashi tace”To me yake faruwa haba kai kuwa daga dawowa sai ka aikata abunda bai dace ba .” Yace.”Hajia yarinyar nan bata da kunya wallahi wai sun samu sa’bani da Yaya Ramlatu shine ta fitar da hannu ta mareta.” Hajia tace”Subahanallahi yaushe akayi hakan.”? Ya kalli su Saddiqa da fad’i! Saddiqa Zainab ta mari Yaya Ramlatu ko kuwa.”? Saddiqa da sauran yaran suka sunkuyar da kansu saboda basu iya karya ba.” Yace.”Yanzu kin tabbatar da ba sharri akayi miki ba ko, a gabansu kika tsinkawa uwarsu mari sabida baki da kunya ko me tayi miki ai sai ki bari na dawo ki fada min aa sai ki ka shirya karya da gaskiya kika kira ni a waya kika fad’a min to jiya Salim ya sheda min duk abunda ya faru a tsakaninku.” Zainab bakinta ya mutu murus sai hawaye dake zubo mata ta kasa magana ma ballantana ta kare kanta, Hajia tace” Idan ya kasance Zainab ta mari Ramlatu sai mu kira al’amarin da sunan hakkin wasu ne ya kama ta! Shin Ka tambayi dalilin zuwanta gidanka? Ramlatu ni na haifeta amma nafi kowa sanin halinta

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MADADI CHAPTER 13

MADADI CHAPTER 15