in

MADADI CHAPTER 13

MADADI CHAPTER 13

zaune kasan kafet abin duniya ya taru yayi mata yawa, ga tarin magunguna nan a gabanta Halisa har yanzu taqi lafiya daga an toshe waccar matsalar sai wata ta bayyana yanzu wasu irin qananun kuraje ne suka feso mata a gabanta da matsematsin cinyarta kullum cikin susa take duk ta kwailaye fatar jikinta! Wannan dalilin yasa Abbah Abbas baya yarda wata mu’amula ta aure ta shiga tsakaninsa da ita ko toilet dinta baya shiga yayi wani uziri saboda a gabansa Dr Sa’adatu ta tabbatar masa da cewar Halisa na dauke da mugun sanyi wanda yayi masifar cin karfinta, wannan dalilin yasa ya janye jikinsa sosai da ita sai dai kuma duk wani abu da take bukata yana yi mata kuma yana tsaye kan duk wani maganin da Dr zata bada umarnin siya komai tsadarsa kuwa zai fitar da kudi ya siya sannan kuma ya jajurce a kan ta tayi amfani da maganin a kan ka’ida Ganininta a firgice a lalace! yasa jikinsa ya d’anyi sanyi, Halisa sarkin kwalliya da gayu itace ta koma wata iriya tamkar mara hankali! Tausayinsa yaji saboda yasan duk irin halin da ta jefa kanta a kansa ne wannan dalilin yasa ya sassauta fuskarsa ya shiga dakin ya zauna gefan gado yana kiran sunanta. Ta dago tana kallonsa wasu lafiyayyun hawaye suka wanke mata fuska! In da saboda ya saba da ganin wannan hawayen nata Gyaran murya yayi a nutse yace.”Ina fatan kinsha maganin naki a kan ka’ida.”? Hanci ta shaqa! wasu hawayen na sake shararo mata, Yace.”Kiyi hakuri wannan koke koke bashi ne mafita ba a gurinki addua ce mafita ki roki Allah ya yaye miki sai dai kuma ba zan gaji da fada miki cewar kece kika siya da kudinki dan haka dole kiyi hakuri ki ‘kar’ba! ni nayi miki al’kawari insha Allah daga dubu daya zuwa miliyan daya zan iya fitarwa a kan lafiyarki saboda haka ki kwantar da hankalinki! ki cigaba da rokan Allah ya baki lafiya .”( Lallai Abbah Abbas ka cika dan halak) Halisa hannu tasa ta goge hawayen fuskarta tace”Abbahn mufida nagode sosai dan Allah kada ka juya min baya.” Murmushi yayi yace”Halisa nasan fa duk wannan masifar da kika shiga saboda da ni ne to akan me zan sake ki ko na juya miki baya ni ba haka nake ba, zaki cigaba da zama a matsayin matata har karshen rayuwarki.” Hanci taja ta sunkuyar da kanta a qasa tare da fadin “Nagode Abban Mufida.” Mikewa yayi yana duba agogon hannunsa yace.”Ni zan tafi gurin daurin aure.” Ta kalleshi le’banta na rawa tace”To Allah ya sanya alkairi.” Amin yace a takaice ya juya da niyar fita daga dakin…..Kallo ta bishi dashi hawaye wani na bin wani lallai babu shakka abunda yafi karfinka dole ka saka masa ido…Yau mijinta da take bala’in so zai daura aure da dalleliyar budurwa tabd’ijam! ashe da ranta za taga wannan ranar. *To Alhamdullhi* An daura aure lafiya ‘Bangaran Amarya suna cikin tsantsar farin ciki tare da taya ‘yarsu ‘yar uwarsu Zainab dace da samun miji nagari…..Yayin da kuma ‘Bangaran ango dashi kansa angon suke cikin damuwa da tararrabi al’amarin da yake damunsu, ha’ki’ka! Yanda suka nuna damuwarsu a kan al’amarin Naja’atu zaka fahimci cewar suna tsananin qaunarta gami kuma da tausaya mata, wannan dalilin ne ma ya sanya bayan hankula sun kwanta suka ke’be kansu gabad’aya harshi angon suna tattaunawa dangane da abunda ya faru, a nan ne Alhaji ya sake sanar musu da shawarar da ya yanke na tura Hajia Rabi taje ta daukota …Gabad’ayansu sun amince da hukuncin da Alhajin ya yanke. Cikin gidan Alhaji ma hakane ya kasance Baba Talatu da Hajiya aunty Maryam su kad’ai ne suka san abinda ke zuciyarsu kawai dai sun sake ne suna hidima da jama’ar da suka tara……Ita kuwa Yaya Ramlatu ta manta da wata Halisa yanzu ta amarya take, ta tara mutane a gefe guda sai hira suke suna shewa babu abinda ya dameta, burinta kawai a kawo amarya taga wace iri ce idan irin wacce za’a had’u da ita a rufawa kai asiri ce to za tayi kokarin riketa hannu biyu! Zata kuma yi kokarin ta d’orata a kan hanyar data d’ora Halisa a kai……Kwana biyu da Halisa ta daina daukar shawararta duk a dame take ga rashin kudi da yake damunta! a lokacin da suke tare da Halisa kudi basa yanke mata dan sosai Halisa take sato mata kudin mijinta ta bata, to cikin kwanakin duk a takure take, dan tayi tayi da Halisan akan tazo su sake komawa gidan Boka Halisa taqi amincewa shine take jin haushinta ta daina zuwa dubata! so take amarya tazo su had’a kai su muzgunawa Halisan. *ANGO DA AMARYA* Abbah Abbas kasa Ta’bukawa amarya komai yayi saboda rashin nutsuwa da kwanciyar hankalin da yake ciki, hakanan yana ji yana gani ya sanyawa dalleliyar amaryasa ido bayan sun

gabatar da sallar ma’aurata sai kawai ya umarceta da taje ta kwanta! Zainab ta mike a nutse taje ta kwanta tana mamakin rashin walwalar angon nata, duk da bata da shekaru da yawa amma tana da wayo kuma tasan yanda ango ke rawar jiki a kan amaryarsa idan bata manta ba akwai wata kawarta mai suna Mariya da akayiwa aure ta dinga basu labarin irin rawar jikin da angonta ya dinga yi mata a daran amarcinsu…….Kuma itama ba saurayi bane zaiyi Abbah Abbas d’in! Dan har da sukaje gidan suka dinga sha’awar irin rayuwar da ‘kawarsu mariya takeyi da sugar dady d’inta! lokacin itama taji tana sha’awar auran manyan mutane saboda taga yanda mijin Mariya ke kula da ita yanda ya kamata! To sai gashi burinta ya cika angon nata sai wani salalaf-salalaf! yake yi kamar wani mara laka a jikinsa sam baya wani nuna gand’okin sa a kanta……Haka tayi bacci cike da takaici da bakin ciki…Da asubah ta gane a dakin ya kwana dan ganin wayoyinsa a kan bed kusa da ita…Alamu sun nuna mata cewar ya tafi.massalaci. Sai ta mike ta nufi toilet, tayi wanka da alwala ta fito ta shirya jikinta tsaf tsaf! ta hau kan dadduma ta gabatar da sallar! Sai da tayi addua sosai kana ta mike ta nufi mirror dinta dake shaqe da kayan kwalliya, Zainab ta zauna ta tsantsara kwalliya mai kyau da burgewa har dasu gashin ido sosai tayi kyau ta fito amarya sak! Zama tayi kan bed tana jiran shigowarsa….Koda ya shigo dakin kasa dauke idonsa yayi daga kanta..Yaushe rabon da yaga irin wannan kwalliya tun kafin Halisa ta kwanta ciwo, dama itace ke yi masa irinta Naja’atu dama can wannan kwaliye kwaliyen bai dameta ba! Shi kuma gashi yana san gayu! Zainab sarkin dubara da wayo ko a fuska bata nuna masa jin haushin abinda yayi mata jiya ba ta tsuguna har a qasa ta gaidashi, ya amsa yana mirmushi mai kyau da ma’ana, kanta ya dafa a nutse yace.”Allah yayi miki albarka! Ta amsa da ameen tana fari da idonta! saurin dauke kansa yayi yace”Tashi muje ku gaisa da Halisa da yaran ki ko.” Murmushi tayi a nutse tace”To Habibi.” Mikewa tayi ta yafa mayafi a jikinta sai murmushi take tana sunkuyar da kanta! Ya kama hannunta ya ri’ke a cikin nasa suka fita daga dakin…..Kai tsaye ‘bangaran Halisa suka nufa……. *******59 Baba Larai kad’ai suka samu a palon tana aikace akaice kamar ko da yaushe suka gaisa a mutunce ya tambayeta kwanan yara tace”Sun tashi lafiya kalau.” Zainab ta dan risina cike da ladabi ta gaisheta, Baba Larai ta amsa cikin farin ciki tana jin dadin girmamata da yarinyar tayi lallai babu shakka duk inda ta fito gidan mutunci ne….Zainab din ya dan kalla yace.”Ki zauna bari na shiga gurin ‘Yar uwar taki.” Tace”To tare da samun guri ta zauna kan kujera, Baba Larai ta juya domin cigaba da aikinta tana murmushi Lallai Allah ya musanyawa da Alhaji zankad’ed’iyar mata sarkin ado da kwalliya dama hausawa nacewa wani hanin ga Allah baiwa ne……Su saddiqa ne suka fito daga dakinsu ita da Mufida suna sanye da Atampa iri daya shi kuma Mussadiq yana sanye da shadda blue color tsaf tsaf dasu suna gudanar da komai nasu cikin tsari da tarbiya dan sosai baba larai take tsaye a kansu da kula da tarbiyarsu. A nutse suka gaishe da

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MADADI CHAPTER 12

MADADI CHAPTER 14