in

MADADI CHAPTER 12

MADADI CHAPTER 12

tsayawa guri daya sai yawo takeyi a gurin ita a karan kanta tayi tayi duburar da za tayi ta ri’keshi abin ya fassakara gurin ya riga ya sakwarkwace! ya saki tamkar bakin tsohuwar rijiyar data zaizaye ta tana kokarin ruftawa! kokarin kama jijiyar tasa takeyi wai tayi masa dabura irin wanda take masa idan tana al’ada! aikuwa a fusace! ya tureta ya mike yana jan tsaki! bandaki ya nufa domin ya gyara jikinsa, Halisa ta dora hannunta aka tana kuka mai tsanani da fad’in “Na cuci kaina nayi wa rayuwata illah yanzu menene mafita a gareni? na lalata martabata da mutuncinta nasan yanzu zanyi ta fuskantar kalubalan rayuwa…(‘Kalubale gareku mata masu sake saken maganin matsi a gabansu wallahi ku kiyayi kanku akwai manya manyan cutuka da zaku janyowa kanku) Koda ya fito ya tarar da ita tana kuka babu walwala ko ta kwabo a tare dashi yace ta bashi guri baya son damuwa yana so ya kwanta ya huta! Jikinta a sanyaye ta dauki rigar baccinta tasa ta kama hanya ta fita daga dakin cikin wata iriyar tafiya tamkar wacce ta rasa laka a jikinta, saboda tsananin bacin ran da yake ciki ko binta da kallo beyi ba ya sanya jallabiyarsa ya hau kan dadduma domin gabatar da sallar nafila kamar yanda ya saba yi a dik daran duniya. *KADDARA TA RIGA FATA!!!!!* To jama’a da yawa sun sheda da daurin auran Naja’atu malam Sani da Bashir Aminu dan jarida akan sadaki naira dubu hamsin wanda bayan an watse daga gurin daurin auran kowa ya kama gabanshi Alhaji Sama’ila ya samu Naja’atun da kudin sadakinta ya damka mata a hannunta kana kuma cikin tattausan lafazi ya shiga yi mata nasiha mai ratsa jiki! daga karshe yayi mata fatan alkairi gami da zaman lafiya da mijinta….Naja’atu na kuka tana sauraran nasihar da Hajia Abu ke mata itama dai kwatancin irin ta mijinta tayi mata sannan itama tayi mata fatan alkairi tare da zaman lafiya a gidan auranta…..Sannan da kanta ta dauketa ta kaita gaban iyayenta tace lallai su sa mata albarka kuma suyi mata adduar zaman lafiya a gidan auranta….Baba malam addua sosai yayi mata Baba Talatu itama tayi kokarin kawar da abinda ke cikin zuciyarta ta sanyawa auran albarka kamar yanda hajian ta bukata. Alhaji Sama’ila ne ya yanke shawara kan cewar dole a wakilta mata guda biyu ko uku domin suje suga inda za’a ajiye naja’atun Baba malam yaji dad’in shawarar da alhajin ya kawo babu shakka shawararsa a bar dubawa ce……….Hajia Rabi amaryar Alhaji da wasu mutum uku daga bangaran Baba Talatu suka shirya tsaf domin rakiyar amarya garin jos………Naja’atu jin shawarar da aka yanke yasa ta k’ebe a guri guda ta kira wayar Bash din ta sanar masa halin da ake ciki wanda shi da a tsarinsa kawai yana so ya dauketa ita kadai su tafi, to amma uzirin data kawo masa bai girgiza shi ba yace mata babu damuwa insha Allahu su jiraye shi da misalin karfe biyu na rana yana wani uziri daga ya gama zaizo ya daukesu,

dama shi da abokansa guda biyu ne kawai suka rage dan ana gama daurin aure mahaifinsa da sauran jama’ar da suka rufo musu baya suka tafi…Shi da abokansa suka rage domin daukar amarya kamar yanda suka tsara. Baba Magajiya da Hajia Rabi har suka wayi gari a garin jos a kuma gidansu Bash wato gidan alhaji Aminu dan jarida basu ji ance su shirya a nuna musu gidan amarya ba, tun bayan saukar su garin aka saukesu a wani daki ba’a kara bi takansu ba sai dai daga zarar lokacin cin abinci yayi za’a kai musu mai rai da lafiya, Naja’atu kuwa dama suna sauka a garin ko awa daya basu yi ba Bash ya kirata a waya ta sameshi a dakinsa, Munira ce tayi mata jagora har dakin nasa, lokacin abokansa kowa ya kama gabansa sai shi kadai daga shi sai garamin wando yayi wata iriyar kwanciya yana shafa kirjinsa da hannunsa Naja’atu Ganinsa a haka ya tayar mata da wani irin feeling mai zafin gaske! a take tsigar jikinta ta dinga tashi ta dinga tunano irin zazzafar soyayyar da yayi mata al’kwarin zai gwada mata duk randa sukayi aure! Cikin kasala ta karasa shiga dakin, Bash a d’imauce ya mike zaune ya janyo hannunta ta fada saman kirjinsa ya matseta sosai yana kokarin sa hannunsa a cikin rigarta! ajiyar zuciya mai zafi ta dinga saukewa tana langwabewa a jikinsa yana cigaba da lugwigwitata tana jin dadi! bargo guda suka shiga ita dashi suka dinga tsotse tsotse suna rungume rungume! har dai suka kasa hakura suka fara kokarin aikata mai gabadaya! dan saboda yanda suka fita daga cikin hayyacinsu! Na’jaatu kanwa takar tsami kwarnafi ya kwanta dan duk tarin sha’awar data tara tsayin wattanin da suka gabata sai da bash ya kawar mata dashi! Suka yini suna abu daya ko nan da can bash yaki bari ta fita a haka tana ji tana gani ta kwana a dakinsa sai da safe tukkuna ya bari ta koma cikin gidan….Lokacin ne ta tarar da su Hajia Rabi sun shirya tsaf domun tafiya gida! cikin kunya gami da jin nauyi ta samu guri ta zauna tana gaishesu! suka amsa mata babu wata cikakkiyar walwala a tare dasu dan saboda gabad’ayansu sun sha jinin jikinsu dangane yanayin zamantakewar mutanan gidan! haka dai sukayi sallama da juna kowanne da damuwa a cikin zuciyarsa…..Naja’at ta d’an ji damuwa da tafiyarsu amma dare yanayi da ta kasance da Bash ya mantar da ita kowa da komai ya shiga wanke mata zuciyarta da kalolin soyayarsa mai wahalar samu. To koda su hajia Rabi suka koma gida babu wacce ta fadi wata magana da zata tayar da hankalin jama’a! Hajia ta shiga har dakin Amaryata bayan tayi mata barka da dawowa sai take tambayarta yanayin gidan da aka kai Naja’atun….Hajia Rabi tace”Guri ne mai kyau da tsari sannan kuma kamar yanda Bash din yayi al’kawarin cewar zai sawa matarsa kayan daki da duk wasu abun bukata ya cika alkawari dan haka gida sai dai a godewa Allah. Hajia Abu tayi farin cikin jin wannan labarin da amaryarta ta fad’a mata dan haka gabad’ayansu har gidan baba malam din sai kowa ya kwantar da hankalinsa suka yiwa amarya fatan zaman lafiya tare da mijinta. A cikin kwanaki bakwai da auran Bash da Naja’atu sun ‘barje soyayya sosai dan gabadaya Bash daina fita yayi kullum yana gida suna aikin abu daya Naja’atu tayi sabo da sex sosai dan wani sa’in ma kafin bash din ya nemata da wata bukata ta nemeshi! haka suke wannan rayuwa tamkar tumakai duk ibadah irin na Naja’atu tarayyarta da Bash sai da tayi rauni yanzu Naja’atu ta daina sallahr asubahi a kan lokaci kullum sai gari ya waye takeyi saboda raba dare suke suna aikin abu daya idan suka gama babu maganar su tsarkake jikinsu Bash zai rungumeta da najasa a jikinsu suyi ta bacci shi kuwa shed’an dama haka yake so kullum cikin kara ingizasu yake suna ya dinga qissima musu a zuciyarsu cewar dan basu yi sallar asubah a kan lokaci ba ai ba wani abu bane…. ***** Rayuwar Bash da Naja’atu haka ta cigaba da tafiya cikin rashin tsari! Sun mayar da kansu tamkar tumakai basu da aiki sai abu d’aya su kwana su yini a makale da juna Naja’atu ta zama wata fitinanniya ta gaske inda shi kuma

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MADADI CHAPTER 11

MADADI CHAPTER 13