in

MADADI CHAPTER 11

MADADI CHAPTER 11

matsiyacin dad’i ya rufeta wayyo yau da ita kadaice a gurin sai ta taka rawa ciki ya zube burinta ya cika…….Kukan munafurci ta fashe dashi ta shiga tafa hannu tana fad’in”Innalilihi wa’ina ilahi raji’una! yanzu yarinyar nan sai da ta zubar da cikin nan? anya naja’atu tayi maka adalci kuwa? me kayi mata take maka irin wannan ‘kiyayyar Allah ya baka zuria tayi maka asararsa kuma sabida bata da kunya cikin izigila take fad’a maka ga abunda ta aikata maka kai jama’a amma wannan yarinyar bata kyauta ba wallahi.” Shuru yayi domun bakinsa mutuwa yayi murus! ya dinga kallon fuskar wayar yana ta karanta text din kamar me koyon karatu!! ya jima cikin wannan yanayin kafin ya samu damar furta kalmar innalilihi wa’ina ilaihi raji’un!!! Ya kashe wayar ya ajiyeta kana ya mike ya nufi toilet domun dauro alwala…Halisa murmushin jin dadi tayi ta juya bayanta tare da jan bargo ta rufe jikinta cike sa nishadi da farin ciki bacci mai dadi ya dauketa. Dadduma ya tsaya ya fuskanci al’kibula ya tayar da sallah…Raka’a biyu yayi ya jima a sujjadar karshe yana rokon Ubangiji sassauci ya d’ago tare da sallame sallahr nan ma ya jima hannunsa a sama yana addua kafin ya shafa a fuskarsa ya mike yana jin wani kuzari a jikinsa zuciyarsa tayi wasai babu wani bacin rai tabbas tunda har Allah ya zartar da irin wannan hukunci to hakan shine alkairi a rayuwarsa…..’Yar jakarshi da yake tafiya da ita ya dauko ya zauna kasan kafet ya bud’eta a nutse ya dauko wani memo ya ya bud’e ya yagi pepar d’aya ya dauki biro a nutse ya soma rubutu a jiki…. *Jikina na karkarwa na le’ka domun naga mai yake rubutawa……😤 yanke jiki nayi na fad’i hawaye na ziraro min shikkenan Naja’atu ta cuci kanta* _NI ABBAS SAMA’ILA NA SAKI MATA TA NAJA’ATU MALAM SANI SAKI DAYA INA RO’KON ALLAH YASA HAKA SHINE YAFI ALKAIRI A TSAKANINMU._ *Kuyi hakuri dan Allah👏🏻😢 Nima ba’a son raina ba Labari ne yazo a haka* *MANZIR _ALWAFIR ABUJA🌴🌴* _*Sun tanadarwa da mata kayan gyaran jiki masu kyau da inganci magungunansu babu almundahana a ciki mutukar kika fara amfani da ingantattun magungunan company manzil alwafir to ba zaki daina ba saboda ingancin magungunansu ko wace matsala kike fama da ita mutukar ta shafi zamantakewar auranki manzil alwafir zasu share miki hawaye da akwai gruops na mussaman da suka bude domin taimakon mata masu fama da matsaltsalo a gidan auransu idan kanki na cikin duhu mutukar kinyi rijistar dasu to kukanki ya ‘kare idan kina bukatar kiyi rijistar sai kiyi magana.*_ Mddbhrmbn46 A nutse ya linke takardar da yayi rubutun ya bud’e tsakiyar memo d’in yasa ya mayar da jakar ya rufe tare da mikewa da ita a hannunsa zuwa yayi a dana ta a inda take kana ya nufi bed din ya kwanta yana jin nutsuwa da kwanciyar hankali na saukar masa a zuciyarsa tabbas rabuwa da auran Naja’atu shine alkairi a tare dashi, dan idan ya tilasta kansa zama da ita to kuwa zai ta had’uwa da takaici da ‘bacin rai watakila ma sanadiyar hakan ciwo ya kamashi dan a yanda yake da kaunar ‘ya’ya gami da adduar Allah ya bashi zuria da yawa baya tsammanin zai iya zama da kowacce irin macece mutukar zaiyi wahalar dasa ‘kwai ta zubar masa babu shakka ko wacece zai iya rabuwa da ita rabuwa ta har abada…Cikin kwanciyar hankali yayi bacci da asubah ya tashi zuciyarsa wasai baya ta’ba nadamar abinda ya aikata ga yarinyar. ‘Bangaran Naja’atu kuwa kwana tayi tana munanan mafarkai wanda taga Halimatu tazo mata da wasu fararan kaya masu kyalkyali sai dai yanayin yanda taga ‘Yar uwartata ya bata tsoro fuskar Halimatun babu walwala ta tsira mata ido kawai tana kallonta ita kuma sai magana take mata tana kokarin rike hannunta sai ta fizge ta bar gurin da sauri ta dinga waige waige tana kiran sunanta amma bata ganta ba……Sannan kuma duk a cikin mafarkin taga mahaifiyar ta na kuka ita da Mussadiq suna kiranta….a tsananin firgice ta tashi tana had’a gumi! ta dinga kallon dakin gabanta na fad’uwa gaskiya mafarkin nan ya bata tsoro tunda Halimatu ta rasu bata ta’ba yin mafarki da ita ba sai yau shiyasa jikinta yayi sanyi…Wayar *Bash* ta dauka ta kunna ta haske dakin a maimakon ta tashi taje ta dauro alwala sai kawai ta shiga dube dube a wayar wai ko bayan kwanciyarta Abbah Abbas ya turo replay ta gama dube duben ta ba taga komai ba a sanyaye ta ajiye wayar ta mike ta nufi bandaki domin yin alwala…..Kafin ta tayar da sallah sai da ta tashi Munira tukkuna ta hau dadduma…Munira kuwa zuwa tai tayi fitsari ta dawo ta sake kwanciya dama can Munira bata sallah sai gari ya waye…Naja’atu bayan ta idar da sallah zama tayi kan daddumar abin duniya ya dameta mafarkin da tayi yayi masifar bata tsoro mussaman ganin mahaifiyarta na hawaye tasan duk inda suke suna can cikin tashin hankali da damuwa, ta dinga share hawaye tana fad’in Ba laifina bane tun farko na fada muku bana so bana sonsa kuka kasa fahimtata.” Munira tayi firgigt ta mike zaune tana kallonta tace”Naja’atu lafiya kike kuka.”? Hawaye ta share tace”Munira wani mummunan mafarki nayi wallahi tabbas iyayena na cikin damuwa da rashin ganina.” Munira tace”To ai dama dole su shiga damuwa da rashin ganinki ai tun farko laifinsu ne yanzu dan sun neme ki sun rasa ai kansu zasu tuhuma sai su gane auran dole ba

abune mai alfanu ba.” Girgiza kanta kawai tayi tace”Munira naga Yaya Halimatu a mafarki tana cikin ‘bacin rai ga Mussadiq na kuka yana kiran sunana jikina ya soma sanyi da wannan al’amarin wallahi.” Munira taja tsaki tace”Ai shikkenan sai kije kiyi tayi waye ya fada miki mafarki gaskiya ne? dan Allah ki daina wannan maganar idan zaki saki jikinki ki saki jikinki kawai ki watsar dasu koma meye ya faru ai sune suka janyo me yasa suka aura miki wanda bakya so.” Girgixa kanta ta cigaba dayi hawaye na sake zubo mata…Ita kuwa Munira ta mike ta nufi bandaki tana surutai kan damuwar da taga Naja’atun ta shiga…. Abbah Magaji na zaune yana karya kummalo Halisa ta fito daga dakinta hannunta rike da wayarta ta zauna kusa dashi, tace”Kaga ina ta kiran numbar ba dauka ba kuma wannan numbar itace nake tsammanin ta ‘Kawarta, dan bana mance ranar da tazo tace na bata aron waya zata kira ‘kawarta a jos.” Yana goge bakinsa yace.”Bani numbar na gwada kira.” Wayar ta mika masa yasa numbar a wayarsa cikin ikon Allah tana fara ringing aka dauka….Hands free yasa yayi sallama…Munira ta amsa da fad’in ” Da waye nake magana.”? Yace.”Kina magana da wani bawan Allah ne daga kano shin ko kinsan wata yarinya Naja’atu.”? Naja’atu sai da ta kusa sakin fitsari a wando jin muryar Abbah Magaji radau a kunnanta!!! Munira tayi saurin kallonta idanunta duk sunyi gwale gwale. Abbah Magaji yayi gyaran murya had’e da fad’in “Hello kina jina kuwa.”? Munira ta shiga inda inda da fad’in ” A’a ban santa ba wallahi.” Yanayin yanda take maganar cikin rashin gaskiya yasa ya fahimci cewar yarinyar da hadin bakinta dangane da faruwar al’amari…Yana kokarin yayi magana Munira ta kashe wayar suka ‘kurawa juna ido ita da Naja’atu, ya akayi tun ba’aje ko ina ba asirinsu zai tuno..Naja”atu kuwa ai tuni hawaye sun ‘balle mata fargaba da tsoro duk sun cika mata zuciya. Abbah Magaji yabi wayar da kallo yana mamakin kashe masa da yarinyar tayi girgiza kansa yayi tabbas biri yayi kama da mutu, wayar ya sake kira….Munira ta zabura tana kallon wayar ta’ki dauka har ta katse Abbah magaji ya sake kiran wayar nan ma Munira taki dauk’a..Sai kawai ya ajiye wayar yana murmushi hade da kallon anty Maryam yace.”Duk yanda akayi yarinyar nan tasan inda Naja’atu take kuma da alama da akwai hadin bakinta dangane da faruwar al’amarin.” Anty maryam tace”Nima tunda naji yanda take amsa maka a tsorace yasa na fahimci tana da masaniya akan abinda yake faruwa yanzu

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MADADI CHAPTER 10

MADADI CHAPTER 12