in

MADADI CHAPTER 10

MADADI CHAPTER 10

al’amarin…..Naja’atun kuwa wani irin ajiyar zuciya take saukewa gumi na tsatstsafo mata daga jikinta tsabar tashin hankalin da take ciki yasa taji jikinta yayi garau zazzabi dake damunta tuni yayi nasa guri! babu abinda ke d’aga mata hankali gami dasa ta a fargaba sai maganar cikin dake jikinta d’an kimanin satika uku….Aunty Maryam tace”Yawwa dama so nake ki dawo hayyacinki sai muyi magana dake irin ta masu hankali Naja’atu inaso kiyiwa maganata kyakykyawar fahimta shin kina so ki butulcewa Allah akan irin baiwa da ni’imar da yayi miki ko? shin kin san dubban mutane nawa ne suke neman haihuwa amma Allah be basu ba me yasa ke Allah ya azirtaki da samun karuwa kike cewa bakya so har kina i k’irarin zubarwa kinsan babban laifin da kike kokarin aikatawa kuwa.”? Aunty maryam ta’kare maganarta cikin kwantar da kai gami da rarrashi. Ido jawur! ta kalli anty maryam din tace”Aunty maryam ke yanzu kin yarda da abinda Dr sa’adatu ta fad’a! ni wallahi bani da wani ciki ki daina wannan maganar insha Allahu ba zan haihu da wannan mutumin ba dan ni bana sonsa.” Aunty Maryam ta ri’ke bakinta tana kallonta ranta a ‘bace! tace”Wai ke har wata shahararriya ce ko kuma wata mai muhimanci ce da kullum idan anyi magana sai kice bakya son Alhaji Abbas dame kike fishi? wallahi tallahi Naja’atu kiyiwa kanki fad’a ki kuma daina wasa da damar da Allah ya baki! Alhaji Abbas yafi karfin wannan iskancin naki! kinsan babu ‘ya mace da zai nuna yana so a garin nan budurwa ko bazawara ba’a bashi ba amma saboda tsabar butulci ke kin same shi cikin sauki kina iskanci! dole na fad’a miki gaskiya koda zagi zage ni saboda ina gudun ranar da zaki zo kiyi nadama kiyi kuka da idanuwanki a ranar da kika watsar da damar da Allah ya baki.” Hanci taja tace”Aunty maryam ni bazan ji haushinki ba dan kin fadi ra’ayinki a kan wannan auran kowa ya fad’i abinda yake so nima kuma na fad’i abinda yake raina bana munafurci shiyasa shima Abbah Abbas din kullum cikin fad’a masa gaskiya ta nake kancewar ko ‘kwayar zarra bana jin sonsa a cikin zuciyata, in banda abinku a’ina kuka ta’ba ji anyi zaman aure ba soyayya! Kiyi hakuri idan maganata ta baki haushi. Aunty maryam tace”Oh!o ni ai yanzu kin daina bani mamaki da haushi al’amarinki sai dai addua ciki kuwa tunda Dr ta duba ta ganshi to tabbas da akwai shi tunda gashinan kin kasa lafiya ni dai shawarata ta karshe dake shine kije ki zauna kiyi tunani a kan maganar dana fad’a miki idan kina ganin abinda kika kudurta a zuciyarki shine dai-dai ni sai nace Allah ya jishshe mu alkairi.” Tana gama maganarta ta dauki jakarta ta shige dakinta, tana zama gefan bed ta ciro wayarta ta kira mijinta ta sheda masa abinda Dr Sa’adatu tace dangane da rashin lafiyar naja’atun..Amma bata fad’a masa irin iskancin da yarinyar keyi ba. Abbah Magaji cike da tsantsar farin ciki ya nemi numbar abokin nasa ya shiga kiransa…Abbah Abbas yana harami yana addua kiran wayar ya sameshi guri ya samu ya ke’be kana ya daga wayar, suka gaisa da abokin nasa yana tambayarsa iyali Abbah magaji yace kowa lafiya lau sai ‘karuwar da muka samu ashe wai wannan zazza’bin da Naja’atu keyi na al’kairi ne yau da safe nace maryam ta kaita asibiti a dubuta nan Dr Sa’adatu

ke tabbatar mata da cewar yarinyar na dauke da ciki na tsayin sati uku.” Wani irin murmushi ne ya su’bce masa a take ya zube a gurin yayi sujjadar godiya ga Allah kafin ya mike tsaye cike da tsantsar farin ciki yace.” Gaskiya naji dadin wannan albishir din naka na kuma ‘kara tabbatar da cewa Allah sami’uddua’o ne ina gabansa ina rokonsa akan ya azurtani da ‘ya’ya masu albarka ashe ya bani ban sani ba dole nagode wa Ubangiji a bisa wannan babbar kyautar da yayi min.” Abbah Magaji yace na taya ka murna abokina hakika aure yayi albarka tunda gashi kafin aje ko’ina an samu karuwa Allah ne abin godiya muna kuma rokonsa da ya sauki yarinyar nan lafiya.” Abbah Abbas ya amsa da “Allahumma ameen abokina nagode kwarai yanzu haka gabadaya hankalina yayo gida wallahi. Abbah Magaji yasa dariya da fad’in ” Haba Alhaji ka daure ka zauna ka cigaba da addua sati d’aya kamar yau ne insha Allah. Shima yana dariyar yace.”Kasan ni da son yara ina ganin kamar idan na dawo babyn kawai zan gani.” Abbah magaji yayi tai masa dariya kafin suyi sallama cike da mutunta juna. Abbah Abbas cike da farin ciki ya koma masaukinsu Halisa na zaune ita kadai a palo ita kuwa Hajiya Abu na daki bayan ta idar da sallar walha sai ta shiga jan carbi dama haka takeyi ko tana gida sallar walha bata wuce ta. Halisa na ganinsa cikin walwala da farin ciki sai itama ta ara ta yafa ta dinga dariya tana kallonsa…Rungumeta yayi tare da sumbatar gefan fuskarta yace.” Halisa Allah ya sake azurtani da samun ‘karuwa.” Sai ta kasa gane maganarsa ta shiga kallonsa dariyar da takeyi ta ragu gabanta ya shiga bugawa da karfin gaske. Yace”Yanzu nan Alhaji magaji yake sheda min da cewar Naja’atu nada juna biyu ashe zazzabin nan da takeyi bayan tawowarmu na alkairi ne.” Wani irin rugugi! kirjinta yayi lokaci guda cikinta ya hautsine ta nemi yawu ta tarasa a bakinta gwiwowinta kuwa kamar an kwad’e mata su da ta’barya! kallonsa takeyi kamar sabuwar mahaukaciya baki na rawa tace”Ya akayi hakan ta faru..”? Ya kalleta cikin wani irin yanayi yace.”Wannan wace iriyar banzar magana ce tambayata kike ya akayi haka ta faru.”? Sosa kanta tayi cikin wayancewa tace”To ai gani nayi auran naku ko wata d’aya ba’ayi ba ya za’ayi ace har kayiwa yarinyar ciki? anya kuwa ba ‘karya bane ? idan ma da gaske ne to wallahi mybe dashi tazo.” Wani irin mari! ya kifa mata cikin fusata! yace.”Ashe baki da hankali Halisa jinina kike ‘kokarin shegantawa! Wannan wane irin rashin mutuncin ne.”? Halisa tuni ta shiga hankalinta ta dawo hayyacinta ashe zancan zuccin da takeyi a fili ta fad’e shi..Hakuri ta shiga bashi da fadin” Wallahi bata san ta fadi maganar ba kuma dai abin ne ya bata mamaki shiyasa take kwokwanto.” Tsaki yaja mai karfin gaske ya mike daga kusa da ita tare da fad’in “Shashasha mara hankali kawai.” Kallo tabi shi dashi lokacin da yake kokarin shiga dakin da hajiyarsa take

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MADADI CHAPTER 9

MADADI CHAPTER 11