in

MADADI CHAPTER 1

MADADI CHAPTER 1

“Innalillahi wa’ina ilaihi rajiun.”! Abinda Baba Talatu tafad’a kenan ta kalli Saddiqa dake gefe a tsaye tana hawaye tace” Yi sauri ki d’ebo ruwa suma tayi.” Saddiqa ta futa daga d’akin da sauri, karo suka ci da Baba Malam da Babban d’ansa Alhaji Magaji.” Baba Malam yace.” wato dai har yanzu Kuka kuke yi ko da alama dai kuna so ku hana Halima ta kwanta lafiya a kabarin ta.” Tana girgiza kai had’e da ‘kokarin mayar da hawayen idonta tace”Baba Malam mun daina kuka Yaya Naja’atu ce tafad’i ta suma shine Baba Talatu tace na d’ebo ruwa.” Da sauri Baba Malam da Alhaji Magaji suka shiga d’akin. ita kuma ta futa da saurin gaske, ruwa ta d’ebo cikin kofi ta shigo d’akin dashi. Baba Malam dake tsugune kusa da Naja’atu yana mata addua ya kar’bi ruwa ya shiga yayyafa mata a

fuska, Baba Talatu hawaye kawai take sharewa tana girgixa kanta.  Baba malam sai da ya yayyafa mata ruwan sau uku sannan ta saki wata ajiyar zuciya mai kar’fi! idanunta ta shiga kiftawa, sai ta mi’ke zaune da sauri ta shiga rarraba idanunta a kansu. Baba Talatu ta ri’ke hannunta tana fad’in “Naja’atu kiyi hakuri kada ki jazawa kanki lalura.” Ihu! ta zumduma! tasa hannu ta toshe kunnuwanta jikinta na wata iriyar kyarma! tace”Baba Talatu kunnuwa ba zasu iya d’aukar wannan maganar taki ba! a ina aka ta’ba haka *Uba ya Auri ‘Yarsa* ashe dama dake da Baba malam dashi kansa Abban nawa dukkanin ku maguzawa ne ku baku san addin……..Kafin ta ‘karasa Alhaji Magaji ya kwad’a mata mari! yace.”Ke ki nutsu ki shiga hankalin ki bama son shirme da shashanci ki saurara ayi miki bayanin yanda al’amura suke.”  A zabure! ta mi’ke tsaye! kamar wacce zata tada iska tace”Baba Magaji ni bazan fuskanci komai ba ba kuma zan nutsu ba, saboda ni ba kafura bace wallahi sai na kashe kaina idan kuka d’aura min aure da Ubana, wai baku ji sunansa bane Abban Naja’atu fa sunansa amma shine zaku daura mun aure dashi! to dukkaninku sai na kaiku *Hizbah!.* Ta’karashe maganar tana wani irin kuka mai cin rai. Baba Malam ya goge guntin hawayen idonsa ya ri’ke hannunta da fad’in “Auta zauna ni da kaina zan warware miki abunda baki sani ba.” Fuzge hannunta tayi tana ‘kokarin tsallakeshi ta wuce! Alhaji Magaji yayi sauri tare mata hanya Yace.”Naja bakya jin magana ko? To shikkenan idan baki kaimu *Hizbah* bakya ‘kaunar Allah.” Yafad’a babu wasa a tare dashi.  Hannunsa ta ri’ke jikinta sai mazari yake tace”Abba Magaji ka duba maganar nan da kyau fa! Kayi duba na tsanaki! ya za’ayi dan kawai Mamanmu ta mutu sai suce zasu d’aura min aure da Ubana wace irin rayuwa ce wannan.”!!! Tafada cikin wani irin sauti!! Shima a fusace! Yace.”Wai ke waye ya fad’a miki Alhaji Abbas Ubanki ne.”!? Shuru tayi tana binsa da wani irin kallo! bakinta sai rawa yake yi. da kyar ta iya bud’e bakinta tayi magana…..”Baba Magaji bangane maganar ka ba.”! murya na rawa tayi maganar, Baba Malam ya zaunar da ita kusa dashi hannunsa cikin nata ya rike sosai yana kallonta, tausayi take bashi sosai, tabbas yasan dole ne ta shiga rud’ani da tashin hankali sakamakon bayyanuwar abinda yake rufe tsayin shekaru goma sha shida! da suka wuce. Wanda ta d’auka a matsayin mahaifinta dashi ake maganar d’aurin aure a tsakaninsu, babu shakka duk wanda ko yaji wannan lamarin dole ya shiga halin d’imuwa da tashin hankali  ‘Dakin ne yayi shuru na tsayin mintina uku kowa jikinsa yayi sanyi mussaman Naja’atu wacce take jin wata irin fargaba da fad’uwar gaba, tunda Abba Magaji yayi furucin cewar ba Abba Abbas ne mahaifinta ba take wata zabura tana rarraba idonta a kansu bakinta motsi kawai yake tana so tayi magana amma ta rasa me za tace! fashewa tayi da wani kukan tana kallon Baba Malam da kansa yake sunkuye sai zufa yake gogewa, tace”Baba malam kuna so nima na mutu ko? kuna so kamar yanda kuka rasa mamana

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 10

MADADI CHAPTER 2