in

GADAR ZARE CHAPTER 2

GADAR ZARE CHAPTER 2

Umar na gani tsakiyar rik’ak’un ‘yan daba suna ta shaye-shaye shi Umar hannunsa ma rik’e da kwalbar giya, wani daga cikin su naga ya kalli Umar yace ” Oga, a fili na maimaita Oga, a raina nace yanzu ashe iskancin Umar da ake fad’a da gaske har ya wuce tunanin mutane, yanzu Umar d’in mu ma shine Oga? nayi kaina tambayar.
Ina cikin tunanin naji wanda yace Oga yaci gaba da magana ” Oga kaga gidan Alhajin Sama da mukaje fashi sun samu ta sosai, shege mutumin nan kullum yana kukan babu ashe k’arya yake, mak’udan kud’i ne jibge a gidan sa, wata mahaukaciyar dariya Umar yayi irinta mashaya yace ” yo ai irinsu suna da yawa ka manta sanda muka tare hanyar kano, nawa muka samo?
Wani daga cikin su yace ” ai Oga munyi fashi da yawa wanda mu kanmu bazamu iya lissafa su ba, ni bama zan iya tuna wanda kake maganar ba, dariya Umar ya k’arayi yace ” aikai k’aramar kwanya gare ka, shiyasa baka saurin gane abubuwa, ni na rasa ma yadda ka dad’e kana shaye-shaye amma ba hau bola ba, gaba d’ayan su suka tuntsure da dariya irin ta mashaya.
” Oga wai ni ‘yan idan ku har yanzu basu farga dakai bane?
Dariya Umar yayi yace ” an fad’a maka kowa ma sakarai ne irinka, aini duk abinda zanyi da tunani nake yinsa, kuma kaga tun muna Jss 2 da Abdul na fara shaye-shaye da haura gatangar mutane ba, d’ayan yace ” da lab’e a lungu ana latsawa mata nono, dariya Umar ya k’arayi yace ” shege ashe ba manta ba.
“Ah haba Oga yaza’ayi na manta, ni wallahi abin ma har mamaki yake bani, wai ku kwana ku tashi da Abdul amma bai tab’a gane munanan halayenka ba, dariya Umar yayi yace ” kuma wani lokacin har a gidan nake cakewa ta ba, saboda fa na samu damar fashi da makami nak’i yin jami’a, dan nafi samun sakewa, ” hmmmmm gaskiya Oga kai shege ne gaka marar imani, wallahi ban tab’a ganin mutum marar imani irin ka ba, to wai ita Ramlat da gaske kana santa, kuma tsakanin ka da Allah aurenta zakayi?idan ba aurenta zakayi ba muma ka bamu mud’an tab’……
Wata muguwar shak’a Umar yayiwa yaran ya hau dokan sa tako ina yana dukan nasa yace ” idan ina shirmen mu karka k’ara sako min ahalina, dangina ko ‘yan uwana bana kisa amma akan su zan iya kashe mutum har lahira saboda sune ni, kuma koda wasa idan na k’ara jin sunan Ramlat a bakin ka wallahi saina gorje maka shi, saboda ita rayuwata ce itace duniya duk abinda kaga inayi dan ita nakeyi, wallahi akan Ramlat zan iyayin komai cikin kuwa harda salwantar da rayuwata akan Ramlat bank’i kowa ya mutu ba, ita nake so, itace Uwa ta kuma itace Uba na, ban d’au kowa nawa ba sai ita ina mata mahaucin so, duk wanda yanemi rabani da ita to tamkar ya d’aukowa kansa hitila ne, yana kaiwa nan yayi jifa da yaran yana huci kamar Lion, yace ita ba irin sauran matan banza da muke bi bace, ita sarauniya tace.
Abdul dake lab’e a ransa yace ” wallahi ko Ramlat zata mutu ba aure bazan tab’a bari ta auri Umar ba, ya fito daga inda yake lab’e yayi gida, ba k’aramin tashin hankali Abdul yashiga saboda munanan aiyunkan dayaji d’an uwansa Umar na aikatawa, yana komawa gida direct dakin su ya wuce ya rufe kansa a d’aki ya saki kuka ya manta da yunwar da yake ji balle gajiya, a fili yake magana cikin kuka ” Umar ka ha’ince mu ka cuce mu, Allah ya sani ba irin tarbiyyar da iyayen mu suka bamu ba kenan, duk munayan halaye ka had’a ZINA, FASHI, SHAYE-SHAYE, MUNAFURCI, YAUDARA, K’ARYA, ka yaudare mu, sannan kaci amanar mu, kai mak’aryaci ne, a haka zan d’auki tilon k’anwata in baka, daga bakin k’ofar d’akin Mama ta tsaya tana sauraron Abdul.
Duk maganar da Abdul yakeyi cikin kuka Mama najinsa, a hankali cikin rawar murya tace ” Abdullahi bud’e k’ofar, ba musu ya tashi ya bud’e mata k’ofa, ta shigo tana shigowa ta k’ura masa ido sai kuma ya kuma fashewa da kuka, ya rungumeta a hankali Mama ta zaunar dashi, ta d’ago kansa tace ” fad’a min meye faru?
Bai b’oyewa Mama komai Ramlat dake lab’e jikin window ta saka kuka, a hankali Abdul ya mik’e yaje har inda take ya rik’o ta zaunar kusa da Mama ya kuma kwashe komai ya fad’a musu bai rage komai ba, daga Mama har Ramlat kuka suke sosai, haka ma Abdul, saboda ba k’aramin tashin hankali suka shiga ba, sosai abin ya girgiza su, cikin kuka Mama tace ” iya yarda mun yarda da Umar mun bashi amana, koda ake zuwa ake yawo k’arar sa bamu tab’a yarda ba, haka mahaifinku ma har ya rasu bai yarda a aiyukan da ake danganta Umar dashi ba, mai yasa Umar zaiyi mana haka mai muka rage shi arayuwarsa ko so yake yaja mana zagin da zargin duniya.
Ta k’ara fashewa da kuka, “Allah ya sani irin rik’o da tarbiyyar danayi muku ita nayiwa Umar koda wasa ban tab’a banbanta tsakanin ku ba, amma mai yasa zi zab’i irin wannan mummunar rayuwar, a hankali Ramlat ta shiga gogewa mahaifiyyar su hawaye, Abdul ya kalli Ramlat yace ” wannan rayuwar ki ce zab’i ya rage nake ko kiwa kanki gata ko sab’anin haka, ki tuna yau idan ni da Mama muna raye gobe bama nan, kiyi k’ok’ari ki zab’awa yaranki uba na gari, ni dai gaskiya Ramlat ban amince ki auri Umar ba, kwari ki samu wani can ki aura, koda zan rasa rayuwata bazan tab’a yarda ki auri d’an fashi, mazina, d’an shaye-shaye ba, bazan tab’a bari ki lalata rayuwarki ba.
Rungume Abdul tayi cikin kuka tace ” wallahi Yaya koda maza sun k’are bazan tab’a auren Umar ba, bana sanshi na tsane shi, Umar mugune, Yaya nayi maka alk’awarin bazan tab’a auren Umar ba koda kuwa baka raye, sosai ya rungumeta, Mama najin su ta kasa koda furta kalma d’aya.
Ana haka Umar ya shigo d’auke da sallama a bakin sa hannunsa rik’e da carbi, ya shiga d’akin yarda ya gansu babu kuma wanda ya amsa masa sallama, da wani irin kallo da Abdul ke jefa masa ne yasashi shan jinin jikinsa, yakai dubansa ga Mama yaga ta k’ura masa ido tana zubar hawaye kamar mai san gano wani abu, ya kalli Ramlat yaga ta duk’ar da kanta k’asa ita kukan take, a bakin k’ofar d’akin ya tsaya ya kasa shiga, duk ya tsargu yasha jinin jikinsa, cikin rawar murya Mama tace ” zo ka samu guri ka zauna muyi magana, sosai jikinsa ya k’ara mutuwa, cikin rashin kwarin jiki ya koma can gefe ya zauna.
Mama ta kalli Abdul tace ” maimaita abinda ka fad’a min yanzu, tas Abdul ya k’ara kwashe komai ya kuma fad’a, dammmmmm!!!! gaban Umar yayi muguwar fad’uwa, ba k’aramar tsorata yayi ya shiga mummunan tashin hankali babu abinda gabansa yayi sai dukan uku uku, a firgice a kuma razane yake sauraron Abdul harya gama jawabinsa, a zuciyar sa yace ” tab yaufa ruwa ya k’arewa d’an kada, amma dayake d’an duniya ne sai kawai ya fashe da kuka kamar ransa zai fita.
” Mama Abdul dan girman Allah kuyi hakuri, wallahi nima ba’a san raina na tsinci kai na da kuma rayuwar danake ciki ba, nasan banyiwa kai na daku adalci ba, Mama nasan na watsar da tarin kuma ingantacciyar tarbiyyar da kika bani, da rarrafe ya rarrafo gabanta ya dafa k’afafuwanta yana kuka yace ” wallahi Mama kunyar had’a ido nakeyi daku, naci amanar ku, na yaudare ku, na cuci kai na, wallahi duk hukuncin da kuka yanke a kaina zan karb’e shi hannu bibbiyu, dan Allah Mama kiyi hak’uri ki yafe mana, nayi alk’awari zan daina duk munanan halaye na zan zama mutumin kirki kamar yadda kike so wallahi Mama, ya juya wajen Abdul yace” please kayi hak’uri wallahi damuwa da bak’in ciki ne ya jefa ni wannan mummunar rayuwar amma in sha Allah na daina.
Cikin kuka Mama tace ” wacce irin damuwa da bak’in ciki ne wannan da har zaka salwantar da tarbiyyar dana Baja, wacce irin damuwa ce dabazaka zameni a matsayin mahaifiyar ka ka fad’a min ba, wanne irin bak’in ciki ne da bazaka iya samun d’an uwanka kuma amininka ka fad’a masa ba.
Umar ka bani mamaki, kasa na kasa ganin kaina a matsayin cikekkiyar uwa, wacce zata iya amsa sunanta uwa a ko’ina a gaban kowaye, kasa na raina tarbiyyar dana baku, kasa naga gazawata, Umar na yarda da kai fiye da yadda na yarda da kai na da kuma ‘yan uwanka, haba Umar mai yasa haka? ta fad’a tana matsanancin kuka, gaba d’ayan su kukan suke Abdul ya kalle shi yace ” kaji dad’i kasa mahaifiyar ka, da ‘yan uwanka wallahi Umar inda ba da ido na naganka ba, na kuma ji da kunne ba dako kashe ni za’ayi bazan tab’a yarda ba, idan ko wani ne ya tare ni ya fad’an wallahi sai inda k’arfi na ya k’are, cikin kuka Umar ya mik’e yace ” shikenan tunda ba wanda zai karb’i uzurina, zan fita daga

rayuwarku, zan koma can gefe naci gaba da rayuwa bana san na zame muku matsala, amma duk inda zani ku sani zuciyar Umar na tare daku, har abada zaici gaba da amsa sunan d’an ku kuma d’an uwanku, Umar na kune kuma yana k’aunar ku, ya mik’e zai fita wani wawan mari yaji an sauke masa har hud’u.

Mama ta k’ara d’aga hannu zata sake marinsa yayi saurin rik’e hannunta yace ” Mama karki ji ciwo, idan zaki dage ni madoki ya kamata ki samu, wallahi Mama ki ko kashe ni zakiyi bazan tab’a yi miki musu ba, ya fita ya samu icca ya mik’a mata yace ” mama ki dake ni idan hakan ne zai sama miki sauk’i a zuciyar ki, ki dake ni Mama ya k’arasa maganar yana kuka ya rik’o hannunta, yarda iccan tayi ta rungume shi tana kuma.
” mai yasa kake tunanin barin mu, ashe zaka iya barin mu, zaka iyayin rayuwa cikin farin ciki ba tare damu ba?
“A’a Mama zan yi nesa daku ne zan samawa zuciyar ku sauk’i, amma wallahi nasan bani da sauran jin dad’i idan bana tare daku, “daga yau kome zai faru karka k’ara k’ok’arin barin mu, mu naka ne kai namu ne har abada.
Dariya yayi yana hawaye yace ” in sha Allah Mama, ta baya ya mik’awa Abdul hannu ya kauda kai, kallon Mama Umar yayi yace ” Abdul har yanzu bai huce ba, fushi yake dani, Mama ta kama hannunshi takai shi har gaban Abdul, Umar na zuwa ya rungume Abdul yana kuka yace ” kayi hak’uri d’an uwana, in sha nadai na, sosai Abdul ya rumgume shi yace ” laifinka d’aya ne na barin mu da kake k’ok’arin yi, laifin barin mu har yafi wanda ya aikata.
Gaba d’aya sukayi dariya amma banda Ramlat wacce a lokaci d’aya taji ta tsani Umar bata ko k’aunar ganin shi, tana yi masa kallon wani Monster ne, ya lura da yanayin Ramlat dan haka ya mik’e ya nufi inda take zaune ya durk’usa a gabanta, yace ” please kiyi hak’uri ban kumawa, ko kallansa batayi ba tace ” kama kuma mana ni ina ruwa na.
Wata muguwar fad’uwar fad’uwa gaban Umar yayi dan ba k’aramin so yake yiwa Ramlat ba, dan shi gani yake kamar itace rayuwarsa, akanta yana iyayin komai, ” please kiyi hak’uri ma….. bata bari ya k’arasa ba ta d’aga masa hannu tace” please ka rabu dani, ka fita harka ta da rayuwa ta please, dariya yayi dan shi a tunaninsa b’acin rai ne yasa ta haka yace ” bakomai idan kin huce mayi magana, ” na huce me?
“Aini na gama magana wallahi Allah ko maza sun k’are bazan tab’a auren ka ba Umar, wallahi koda kuwa zan mutu ba aure, wallahi dana yi rayuwa dakai a matsayin miji gwamma na mutu, wata k’ara Umar ya saki ya mik’e ya dafe kansa da duka hannunsa biyu, ya nufi Abdul, wanda shi hakan da Ramlat tayi bak’aramin dad’i yayi masa ba, ransa yake godewa Allah a haukace Umar ya kalli Abdul yace ” kaji me take cewa?
Murmushi Abdul yayi yace ” naji kuma hakan ya faranta min rai, wallahi nima koda zan rasa raina bazan tab’a bari Ramlat ta auri d’an fashi ba, hakan ma zai fiye mana kwanciyar hankali kowa ya fita waje ya nema yayi auren sa kawai.

Zumbur Umar ya mik’e ya saki wata mahaukaciyar dariya yace “………..

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GADAR ZARE CHAPTER 1

SOORAJ CHAPTER 1