in

GADAR ZARE CHAPTER 1

GADAR ZARE CHAPTER 1

GADAR ZARE CHAPTER 1

Hankalin jama’ar dake tafiya akan titi. duk ya koma ga kallon tsadadddun motocin dake wucewa ta gabansu wanda sau dayawa idan wa’yan nan motocin zasu wuce duk mutane suna maida hankalinsu akansu . Mutane dake zaune a ‘bakin titi yara da manya Kai wani lokacin hatta mata auren dake ‘cikin gadajensu zaka Ga suna lekawa ta saman gidajensu suna kallon wayan nan lafiyayayun km tsadaddun motoci k’iarar range rober, hummer jeep, bens,4mart final discussion tare da
dandazon ‘yan sanda, masu fararen kaya wato ss sai manya manya sojoji, da special securities zagaye da wayan nan tsadadddun motocin yayinda ajikin kowacce mota an rubuta *SIX STARS COMPANIES* Uhmmmm shin ko kunsan su waye masu wayan nan motocin? Wasu mutane wayanda su ba masu milkin kasa ba ko gwanoni sannan km ba wasu bane a wannan kasar tamu ta Nigeria Amman abin mamaki da alajabi shine yadda mutane garin ke kyawun kaunarsu . saboda wata daukaka da Allah Yayi musu yayinda jamar har sun fi kaunarsu fiyye Ga shugaban kasa ko meyasa hk ? Ni dai nasamu balarin cewa mutane masu tsananin kyauta da daraja

manya mutane sannan km basu da yawan girman Kai suna da tarin dukiya wacce mutane sukace baza a iya auna yawan tarin dukiyar su ba a gida Nigeria da sauran kasashen duniya abinda ke sake daure min kai ,yadda ni kaina ke kadayin son ganin wayan nan mutane sbd ba’a ganinsu , sai dai Daga nesa ka hangosu ‘cikin jerin motocinsu masu matukar daukar hankalin jama’a.. motocinsu basu tsaya a koina ba sai katafarin company dinsu sukayi parking ‘cikin rawar jiki direbobinsu suka fito da hanzarin gaske . Kofar motocin suka bubbude hade da sandarewa a tsaye duk yan sanda da
sojojin dake wajen suka Sara tare da kamewa sai da akayi wajen 10mints sannan suka fito da kafafunsu atare ‘cikin isa da takama me tattare da jin izza …..duk wanda ya fito sai ya tsaya ,sai da suka jeru su shida sannan suka fara takawa ahankali zuwa’cikin company escort da securities dinsu suna take musu baya . A katafaren Company sukayi parking, cikin rawar jiki drivers d’in suka fito, k’ofar motocin suka bud’e had’i da sandarewa a tsayi, duk ‘yan sandan da sojojin dake wajen suka sara, had’i da k’amewa, sai da akayi wajen 10mnts sannan suka saka kafafunsu a tare, cikin isa da tak’ama suka fito. Fuskar kowanne d’auke da kwantaccen murmushi, da farincikin kasancewarsu tare . duk inda suka ratsa sai

d’aruruwan mutane na zubewa suna kwasar gaisuwa, har suka k’arasa shiga cikin office d’in , a k’ofar kowanne office akwai sunan mamallakinsa, a jere suke reras guda shida. Office na farko an saka NASEER, sai na 2 ABDUL, ZAID, AMMAR, KHAMAL, FAHAD Zaid ne ya juyo yayi wa escort d’in su iyaka da hannunshi dasu tafi, kawai gaba d’ayan su suka kuma sara masu sannan suka jiya da hanzari.. Company six stars ya shahara sosai a kudancin duniya dan babu k’asar da basu da reshe, sun d’aukaka sosai, wajen inganta amfanin noma da kayan masarufi, daga na gida Nigeria har dana k’asashen k’etere. , mamallakan wannan Company wasu matasan samari ne wanda a shekaru babu wanda ya haura 38yrs zuwa 40yrs, kan su a had’e yake sosai haka ma matan su da yaran su, tunda ake ba’a tab’a jin wani abu daya shiga tsakanin su ba, asalima a kwai kyakyawar fahimta da jituwa a tsakanin su, Naseer, fari ne dago kyakykyawan gaske ga manyan ido da siriri kuma me dogon hanci, sai d’an k’aramin baki, yana da mata d’aya yara 5 maza 3 mata 2,kwata-kwata Naseer baya san yawan magana, ko surutu idan kaji surutun sa to da abokanan sa ne ko ZARAH sa, sai ko hirar ball. Khamal daka ganshi kaga cikekken bafulatani usul, sai da shi ba fari bane black beauty ne, dan duk cikin su babu wanda ya fishi kyau, shi kuma Allah yayi shi mutum ne mai san musun tsiya da hira yana da matar aure FATEEHA yana da yara 4 mata 2 maza 2. Abdul daga kanshi kaga asalin buzu, domin babu abinda ya rage na buzaye, fari ne fat, dogo siriri, mai manyan idon, shima kamar Khamal yake da shegen san suruntu tsiya, yana da mata YASMEEN da yara hud’u 3 mata 1 namiji. Ammar yaro mai ji da isa,ga kyau ga kud’i dan shi magana tanayi masa wahalar gaske, dan zai iya sati baiyiwa kowa magana ba, miskili ne shi sosai, yana da mata BASMA, sai yara 2 duk mata. Zaid, yaro mai tak’ama da kwarjini ga uwa uba aji da yanga, kyau da kud’i, yana da san magana amma ba sosai ba, dan shi baya san surutun banza, yana da mata LUBNAH, da yara 5 mata 2 maza 3 Fahad, Allah sarki mutum mai hak’uri ga dattako, ga sanin ya kamata, yana da mata KAUSAR da yara 3 mata 2 namiji 1 Duk cikin su babu wanda baya ji da kyau da idan kaga wannan sai kace wannan yafi kyau, amma da wani daga cikin ya fito sai ka rasa wanda yafi kyau,ga kud’i sun zauna dan su kansu k’arya suke susan yawan abinda suka mallaka,a duniya Allah yayi su da hak’uri, hankali, da sanin ya kamata, yara ne da suka ga iftila’i iri iri acikin rayuwarsu. Allah ya basu farin jinin jama’a dan duk inda suka shiga sai kaji ana SIX STARS, ga kwarjinin da Allah ya basu, dan duk rashin kunyar mutum idan yazo gaban su baya iya
tab’oka komai, suna da masifar tausayi da kula hakkin na k’asa dasu, kwata-kwata basa son suga sun shiga hak’k’in wani, suna da gudun zuciya, ga taimako talakawa sosai. mutane da suka taimaka a rayuwarsu Allah ne kad’ai ya san su. Da sunji ana neman taimakon, da gudu suke kaiwa, sun biyawa mutane da yawa karatu, sun taimaki al’umma iya taimako, sun gina gidajen marayu, masallatai, islamiyyoyi, sunfi a k’irga. Babban abinda suka fi tsana cin amana, k’arya, ha’inci, yaudara, mutane na mamakin yadda ake ta rad’e rad’en wai ba ‘yan uwan juna bane su . , a duniya kawai suka had’u, babban abinda yafi bawa mutane mamaki had’in kansu,t tattare da zaman tafiyarsu . dan ko kaya iri d’aya suke sawa, babu abinda ke raba su sai gidajen su, dan duk inda kaga d’aya to sauran ma nanan. , idan d’aya nasan abu to dukkan su suna so, idan ko d’aya yace no suma duka no zasu ce. Zaka iya zagin su, su hak’ura amma daka tab’a d’aya daga cikin su . ka tab’o tashin hankali, babu abinda kowannen su ya tsana irin yaga d’an uwansa cikin damuwa. Gidajen TV da radio sun sha kawo musu katin gayyata suna k’i, babu abinda al’umma ke so, sai sanin asalinsu, da tushen su, da mafarin abotar su. Amma fir Naseer yak’i, duk ‘yan uwan nasun bada labarin nasu a duniya, domin hakan yama iznah, da darasi ga al’umma amma haka suka hak’ura. Lokacin tashi daga office nayi, Abdul ya k’ada bell, a tare suka fito, direct wajen motocinsu suka nufa, da gudu escorts d’insu da sauran jami’an tsaro suka taso, har inda suke aka kawo motocin, cikin rawar jiki drivers suka bud’e musu motocin, da izza kowannan su ya shiga ya zauna, dayake ko mota mutum d’aya baya shiga shi kad’ai ya zauna, sai dai biyu, a k’ofar gidan Zaid aka fara yin parking, gaba d’ayan su suka fito, a tare suka shiga cikin gidan, da fara’a Lubnah ta tare su, ” oh kaga mazan fama, iyayen had’in kai, dai-dai da gida sai an kawo mutum, ku kullum baku gajiya, maimakon idan aka tashi daga aiki kowa ya wuce gida? Sosai suke dariya Khamal yace” kinga marowaciya mu ba abincin ki zamu ci, inma rowa kike mana. “Lahhh haka kuma abin ya koma daga fad’ar gaskiya, kawai dai ina taya ‘yan uwana ne, dan nasan suna can suna jiran mazajen su. Sosai suke dariya Fahad yace” au wato har gulmar mu ma kuke yi ko? to mudai murucin kan dutse ne. Dariya tayi tace ” ku kuma sakaran tsoro ba, kuda ko gida sai kun raka junan ku, Ammar yace ” ba haka bane Matar mu, kawai mun sadaukar da rayuwar mu ne ga junan mu, idan wani abu ya samu d’ayan mu bazamu iya d’auka ba, balle har Mu jure, yayi maganar kamar zaiyi kuka. Gaba d’aya suka rungume shi, Lubnah tace ” kunga ni bazan iya muku ba, ga tuwo can nayi, da sauri Abdul yace ” tuwon me? Dariya tayi tace” acici kawai, tuwon dawa nayi miyar bushsshiyar kub’ewa da kifi, da naman rago, sai man shanu, ai kafin ta k’arasa Khamal ya nufi dining,Ammar yace ” nima dai inaga ta Khamal zanyi, Naseer yace” wane ni, ai Zarah nacan na jira, dariya Lubnah tayi tace ” ai suma suna kan hanya. Hanya kuma? Naseer ya tambaya kafin Lubnah ta bashi amsa sukaji sallamar matan su, cikin zuloya Basma tace ” au wato da nan zaku cika cikin ku? Dariya sukayi gaba d’aya, kowa ya zauna a dining, abincin suka ci cikin fara’a da barkwanci, sannan kowa ya d’auki matarsa da yaran sa sukayi gida. Naseer da Zarah na komawa gida, ta zube a parlor, kallon tayayi yace ” lafiya my life? Cikin shagwab’a tace ” wanka zakayi man, dariya yayi yace “ok shiyasa dama kika lallab’a kika barwa Lubnah yaran? yayi maganar yana sungumar ta hannu tasa ta sak’alo wuyan sa, a kunnanshi ta rad’a masa “hakan ai ba laifi bane danna so hak’k’i na daga wajen miji na. Dariya yayi cikin mutuwar jiki dan yadda take maganar duk ta gama kashe masa jiki, cikin bath d’in wanka ya dire ta, a

hankali ya cire mata kaya shima ya cire nasa . rungumo shi tayi sosai ta d’ora k’afar ta akan bath d’in yayi da gwiwarta ke gogar joy stick d’inshi , a hankali tasa hannu tana shafa faffad’an k’irjinsa mai yalwataccen gashi, cikin wata irin murya tace ” ina san ayiwa little Basma k’anwa, ta fad’i maganar tana gatsa kunnensa, Wata irin zubura Naseer yayi kamar an juna masa electric, a kid’eme ya d’ago ta cak sai kan bed ko wankan ba’ayi ba aka fasa, plat yayi da ita akan gadon ya soma raya sunna.

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

ZULFA CHAPTER 7

GADAR ZARE CHAPTER 2