in

DAN MACE CHAPTER 5

DAN MACE CHAPTER 5

Bayan fitar Hajiyarsa a apartment d’in tunani yayi ta yi yana jin yadda zuciyarsa tayi masa nauyi saboda damuwa,yayi shiru shi kad’ai kamar wanda aka tsikara ya kira Clark,ya shigo cikin girmamawa ya ce “Here i am sir” RAFEEK ya kalleshi idanunsa sun k’ank’ance sun canja launi yace “Ina report na binciken dana sa kayi min.!?” Clark yayi ajiyar zuciya yayi tunanin wani abune daban yasa boss d’in kiransa,yace “Sir ana nan ana binciken,but kamar yadda ka buk’ata,duk binciken mu ya tabbatar mana babu wani namiji a gidan sai wannan likitan mahaukatan” Rafeek ya kalleshi cike da son k’arin bayani,yace “Ka tabbatar babu.!?” Ya gyad’a kai yace “Sure sir” yace “Sai kuma me ka samu.!?” Yace “Sir. Maganar matar da kayi,gaskiya tunda muke zuwa bamu ganta ba,amma dai muna yawan ganin shi Dr Psycho d’in tare da wata” Rafeek ya zuba masa ido yace “Wata kamar yaya.. Aure ne da shi.!?” Clark yace “Ban sani ba sir,but kullum tare suke fita,wani lokaci tana dawowa ita kad’ai a cab,ko su dawo tare da shi” ya tab’e baki yace “Bana zaton yaron nan yana da aure,but abunda za kayi shi ne idan ka sake ganinsu sun fito ka bi bayansa kaga inda yake kai ita waccan d’in da kace suna fita tare” Clark ya amsa da girmamawa,Rafeek yace “jeka idan ka samu wani abu ka sanar da ni.!” Ya amsa sannan ya fice dai² lokacin da Hajiya take k’ok’arin shigowa,ya koma ya kwanta yana rufe idonsa,Hajiya ta k’araso tana kallonsa,sai data zauna sosai sannan ta tab’a shi,ya bud’e idonsa a hankali ya sauke su kan mahaifiyarsan,tace “Rafeek waye ka sa ayi maka following footstep nasa.!?” Bai damu ba yana sake rufe idanunsa yace “My kid” tayi squeezing face looking tana neman k’arin bayani,tace “Ka samu inda suke zaune ne.!?” Ya gyad’a kai ba tare daya bud’e idanunsa ba,tace “Me yasa to baka je da kanka ba.!?” Yayi saurin bud’e idonsa yana kallonta da idanunsa a waje,a tsorace yace “Hajiya naje fa kika ce.!? Idan tana da aure fa.!? Shi kenan na jefa kaina a masifa.??” Ta girgiza masa kai tace “Ba nufi na kaje gidan ba,ka je ka nemi yaron kuyi magana da shi” ya girgiza kai fuskarsa tana turning zuwa wani irin yanayi yace “Hajiya ba zai tsaya muyi magana ba” tace “Me yasa.!?” Duk hiran da aka yi da shi d’azun daya gani ya kwashe labarin ya sanar mata,Hajiya tayi shiru tana tunani kafin ta d’ago kanta ta kalleshi tace “Duk da haka dai kayi k’ok’arin ka samu kusanci da shi” yayi shiru yana tunani kafin ya amsa,bcos baya son ya sake yin musu da maganarta,bai san mene ne zai gani ba kuma gaba yace “Shi kenan Hajiya in sha Allah zanyi yadda kika ce”,tayi ajiyar zuciya bata sake cewa komai ba,sai can ta tuna tace “Kun yi magana da Maimunatu.!?” Ya girgiza mata kai yace “A’ah” tace “Ok.! D’azun munyi waya tace zata kira ka,da na fad’a mata ka ga Hauwa’u,amma baka gano inda take ba” yayi ajiyar zuciya yace “Bamu yi waya ba” tace “Wata k’ila zuwa anjima ta kira” bai sake magana ba ya sake rufe idonsa saboda maganar ma wahala take bashi idan yayi,ji yake k’irjinsa yana masa wani irin ciwo da kyar yake samu yake fitar da numfashi ma a time d’in.+

***
Ihunta shi ne ya janyo hankalin Nuraz da sauri ya d’aga kansa ya kallo inda ya barta zaune d’azun daya shigo,mik’ewa yayi saurin yi ya d’auki robe d’in yasa da gudu² ya tsallako realer wajen duk tsayinta ya sakko ya nufo gurin,a durk’ushe ya ganta saman grasses tana kuka mai tsuma zuciya,ya k’araso inda take ya tsuguna yana kallonta fuskarsa d’auke da damuwa ya fara tambayarta “What happened.!?” Ta d’ago jajayen idanunta da suka rikid’e tana ci gaba da kuka mai tsanani,sake tambayarta yayi ta kasa magana gaba d’aya,banda kuka babu abunda take yi,yayi still yana kallonta har na wani lokaci,ganin bata da niyyar yin magana yasa shi mik’ewa zai bar wajen,taku uku yayi ya jiyo maganarta ya dakata kad’an yana saurarenta
“I don’t know what to do.! How can i tell him the story.!?”
Yayi saurin juyowa yana jifanta da wani irin kallon bai fahimci abunda take fad’a ba
“He said he wanted to hear it,i didn’t know how to tell him what had happened to me.. How could i tell him that my father drove me out of his house.? Ba ni da wani y’an uwan da suka fi min ku a rayuwa ta,idan ya sani zai iya aure na a hakan.!?”
Kasa sake motsawa yayi ya zuba mata idanu yana kallon yadda take yi kamar za ta cire ranta ta jefar,a hankali ya dawo inda ya tashi ya sake tsugunawa kan k’afafunsa,shiru yayi na kusan mintuna biyu kafin ya samu k’arfin guiwar tambayarta “Did he asked u.!?”
Ta sake d’ago jajayen idanunta ta sauke a kansa ta kad’a masa kai,yayi shiru yana tunani zuwa wani lokaci yace “What are u crying for,tambayar da yayi miki ne bakya so.!?”
Tayi saurin sake kallonsa ya kawar da kansa kad’an yace “Whatever happens,try to tell him the truth of ur situation.. The lie does nothing but ruin ur dignity.. If he really care about u zai iya zama dake no matter who u are or what kind of life u face,every person who truly loves u idan har kin fad’a masa gaskiyar al’amarin ki will live with u till the end of life,,but sab’anin haka,surely ba so bane,muradi ne..”
Ta kafe shi da ido ko k’iftawa babu har ya gama maganar,tace “to ni ai ban san ta yaya ne zan fad’a masa ba”
Yace “Do ur best ko yaya ne ki fad’a masa,idan ba son ki yake tsakani da Allah ba za ki gane da kanki.”
Ta sake gyad’a masa kai a hankali tace “if i tell him shi kenan.!?” Ya gyad’a mata kai a hankali,ta fara share hawayenta tace “Ok.! I will tell him”,ya d’aga kansa looking at the sky yace “Do u love him that much.!?” tambayar da yayi mata tasa ta kalle shi,a hankali tayi taking deep breathe ta gyad’a masa kai,ya d’an rik’e gefen lip d’insa kad’an yace “Ok.! talk to him,idan kun yi waya kice masa yayan ki yana son magana da shi,sai ki bashi number muyi magana”
Ta tsaya kallonsa tace “What would u say to him.!?” Bai kalleta ba yace “Ba lallai ki san mene zan fad’a ba” ta marairaice fuska kamar za tayi kuka tace “To ni zan fad’a masa maganar.!?” Ya d’age shoulder yace “idan kina ganin ba zaki iya fad’a ba,ina ganin ki tsayar da alak’ar ku shi yafi alkhairi.”
Ta kalleshi za tayi magana ya tashi ya bar gurin,saurin tasowa tayi ta biyo bayansa tace “To ai baka bari mun gama magana ba” yana ci gaba da tafiya yace “What else do u want me to say.!?” Tace “To ai ni baka bani shawaran yadda zanyi ba”

Ya tsaya bakin entrance yace “What.!?”
Ta tsaya tana sakin ajiyar zuciya,yana kallonta ta gama saita nutsuwarta,suka had’a ido ya d’aga mata gira,tace “To baka ce komai ba ai” yace “Me kike so na fad’a kuma.!?” Tayi shiru kad’an a hankali tace “I don’t know what to say first” ya tsaya kallonta da wannan idanuwan nasa yace “Thought na ce ki fad’a masa komai.!?” Ta gyad’a kai tace “Everything.!?” Ya lumshe ido ya bud’e a d’an fusace yace “Yes.! Haka nace”,tace “Ok.! I will tell him” tab’e baki yayi kamar baya son magana yace “Ko ba zaki iya bane.!?” Tayi saurin gyad’a kai tace “No.! I will try” ya sake tab’e baki yayi knocking,Bareerah ta fito ta bud’e,ya fara wucewa sannan ta biyo bayansa,bedroom ya nufa fuskarsa a had’e kamar wanda yayi gamo da mutuwarsa,shi kad’ai yasan mene ne yake damunsa a rai,yana shiga ya fad’a bathroom ya sakarwa kansa ruwa,itama Nusrah bedroom ta shige sai dai ta kasa zauna,kamar wacce ta yiwa sarki k’arya haka taita zarya tsakanin walls na bedroom d’in,tana tunanin yadda zata iya fad’awa Aatif asalin labarinta,wata zuciyar tace “Ko dai na masa k’arya ne.!?” Da sauri ta tuna abunda ya fada mata,ta gyad’a kai tace “No.! I will tell him the truth” tafi mintuna goma tana yawo daga nan zuwa nan kafin ta tsaya kan magana d’aya,jikinta a sanyaye ta zauna saman study table,karatu take son yi though she have no test,but al’adarta kenan bata bari sai lokacin da zata yi exam ko test sannan tace za tayi karatu,inwardly tunanin maganarsa yak’i barin zuciyarta da ta motsa ko tayi tunanin ta b’oyewa Aatif gaskiya zata ji sautin maganarsa a kunnenta
_”Whatever happens,try to tell him the truth of ur situation.. The lie does nothing but ruin ur dignity.. If he really care about u zai iya zama dake no matter who u are or what kind of life u face,every person who truly loves u idan har kin fad’a masa gaskiyar al’amarin ki will live with u till the end of life,,but sab’anin haka,surely ba so bane,muradi ne..”_
K’irjinta taji ya buga da sauri ta tambayi kanta “Did he loves me the most.!?” Tayi shiru tana tunani,a hankali ta sauke ajiyar zuciya tace “Yeah.! Ai ya fad’a min and i know it”,ajiyar zuciya ta sake yi sannan ta d’auki wayarta data ajiye ta tura masa short text message mai tsuma zuciya.
Sai dare sannan Aatif ya kirata,sun yi hira sosai,yadda take komai a sanyaye hatta maganarta ta canja,but bai tambayeta ba,sai dai yayi k’ok’arin sata farin ciki,sunyi hira sosai can dare ya fara yin nisa suka yi sallama,ta kwanta babu damuwar komai a ranta,da yake bai tambayeta ba sai itama bata damu ta fad’a masa ba,ta barshi zuwa sanda zai sake tambaya sai ta fad’a masa.

In the morning,ya fito cikin shirin tafiya hospital,itama ta fito da shirin fita skul suka had’u a dining,bai kalleta ba ya zauna ya fara break cikin sauri,ta waiwaya bata ga Annie ba ta ajiye handbag d’inta a parlor ta nufo hanyar kitchen,yi tayi kamar za ta wuce ta saci kallonsa tayi murmushi kad’an tace “Good morning” yana ci gaba da abunda yake yi ya amsa “morning how are u.!?” Tace “Alhamdulillah” bai sake cewa komai ba daga nan itama haka,ta lek’a kitchen taga Bareerah suka gaisa tace “Annie fa.!?” Tayi murmushi tace “Ina tunanin suna tare da Aunty” tayi murmushi tace “Ok” ta juya ta koma dining,tana zama ya tashi da sauri ya wuce,ta fara break taga ya wuce d’akin Lolly,har ta gama bai fito ba,ta tashi ta tattara kayan ta kai kitchen sannan ta yiwa Bareerah sallama,handbag d’inta ta d’auka ta wuce d’akin Lolly,tayi knocking ta shiga da sallama,Lolly tana kallonta tayi murmushi tace “Baby har kin shirya.!?” Tayi murmushi tana zama tace “Good morning Aunty” tace “Morning dear,how are u.!?” Tace “Alhamdulillah.!” Ta kalli Annie da yake ita sun gaisa tuni,Annie tayi mata murmushi tace “Saura tafiya skul ko daughter.!?” Ta gyad’a kai tace “In sha Allah” Annie da Lolly suka musu addu’ar fatan alkhairi sannan suka musu sallama suka fito,yana gaba tana binsa a baya,shi ya fara shiga mota ta bud’e side ta shiga ta d’aura seatbelt,a hankali ya fara drivern,sun yi nisa da apartment d’insu ta cikin mirror ya d’aga kansa kad’an ya kallo baya,yaga wani motan kamar tana following d’insu ya tab’e baki ya d’auke hanya,almost five minutes again ya sake ganin motar,duk inda yayi sai yaga tare suke tafiya,idan ya k’ara speed sai yaga motar itama ta k’ara,idan ya tafi slowly still yaga dai motar ta yi slow,ya rasa gane ma’anar hakan,tambayar kansa yayi “Why do they following me.!?” Rashin wanda zai bashi amsa yasa yaci gaba da drivern but inwardly ya damu sosai da rashin sanin dalilin,sun yi nisa sosai har sun kusa da skul d’in ya juya ya kalleta k’asa² ya furta “Do u talked to him.!?”

Ta waiwayo a hankali tace “A’ah” yace “Me yasa.!?” Ta juya tana kallon side tace “he didn’t ask ai.” Ya juyo da sauri ya kalleta yace “Sai ya tambaya.!?” Ta gyad’a kai,ya girgiza kansa yace “Ki sanar masa” tace “Toh ai bai tambaya ba!” Yace “there’s no need to ask” tayi shiru tana tunani,ta jiyo shi yana fad’in “Idan kika fad’a masa ba tare daya tambaya ba,zai fi d’aukan maganar serious” ta jirkita kai gefe,silently tace “Toh”,suka yi shiru duka,har suka zo skul d’in babu wanda ya sake magana,ta sauka tayi masa godiya,sannan tayi masa sallama,tana kallo ya fara tafiya da reverse kafin ya juya kan motar ya d’auki hanyar fita daga skul d’in,sai da taga yayi nisa sosai sannan tayi ajiyar zuciya ta fara tafiya,tana daf da shiga class wayarta tayi vibration,ta ciro ta daga jaka ta tsaya answering,sunan Aatif yasa ta tsaya gefe ta zauna saman wasu kujeru,sai da suka fara gaisawa ya tambayi lafiyarta,sun tab’a hira kad’an yace zai shigo anjima kad’an idan ya fito daga office,tace Allah ya kawo shi lafiya,har zai katse kiran tayi saurin cewa “Idan ka zo i’ll tell u the story ko.!?” Tayi furucin kamar tana tambaya,yayi murmushi yace “Duk yadda kika ce” tayi ajiyar zuciya kad’an tace “sai ka zo toh” suka yi sallama,kiran yana katsewa ta tsaya tunanin yadda zata fuskance shi ta fad’a masa,da kyar ta lalubo idea sannan ta tashi ta shige class ganin tahowar Mr.Thomas Martin.

Bayan sun fito daga lectures suna tare da Veronica Jackson,Maria Robles sai Sarah Alee da yake ita y’ar 9ja ce karatu ya kaita suke gaisawa sosai har mutunci ya had’a su suke fita tare,a wajenta ta san su Maria da Veronica kasancewar apartment d’aya suke zaune,suna tafiya za su cafeteria kiran Aatif ya shigo wayarta,ta d’an tsaya kad’an ta fito da wayar tayi answering,sallama tayi masa ya amsa yana fad’in “Ina gimbiyata za taje ne take tafiyar k’afa.!?” Tayi murmushi tace “Ba dai ka ganmu ba.!?” Yayi murmushi yace “A’ah ban ganku ba amma dai na gano ki ke d’aya” tayi murmushi tace “Ba ni kad’ai bace ai” yayi murmushi cike da zolaya yace “Idanuna ni kuma ke kad’ai suka nuna min” tayi murmushi bata ce komai ba,yace “Ina za kuje ne.!?” Tayi ajiyar zuciya tace “cafeteria” yace “Okay.! Bari mu tafi tare” tayi saurin katse shi tace “A’a mu had’u a can” yayi shiru kamar bai son hakan sai kuma yace “Ok.!”,basu jima sosai da shiga cafeteria ba suka sa akawo musu drink da snacks,tana zaune tayi facing inda duk mai shigowa za ta gansa,ta hango shi yana shigo wajen,sanye yake da white trouser da white shirt mai V-neck,idanunsa a cikin sunglasses mai duhu,tunda ya shigo ta kalle shi haka nan taji gabanta ya fad’i,ta lumshe ido a hankali ta bud’e taci gaba da kallonsa har ya zauna d’an nesa da su kad’an,k’arshen had’uwa,kyau da tsari Aatif yana da su kuma ya kai namijin da ko wace mace za tayi fatan samunsa,tsarin rayuwarsa da komai nasa cikin nutsuwa yake yinsa and dai² iyawarsa yana bawa duk wanda suke tare girma da muhimmanci,fari ne shi sosai dan ya fi Nuraz haske,kana kallonsa zaka gane yana tattare da duk wani nau’in hutu da jin dad’i,sai dai fa idan ana batun kyau dole ne a fara ambaton Nuraz kafin ace shi,asalin mahaifinsa D’an Nigeria ne daya fito daga jihar Gombe,k’aramar hukumar Akko,cikin garin *KUMO* haka ma Mamansa itama y’ar Gombe ce amma ita ainihinta a *JEKA DA FARI* ta taso,,kiranta yayi duk da ya ganta bata d’auka ba ta nemi excuse wajen su Sarah ta nufi inda yake,tun kafin ta k’araso ya zare glasses d’in idonsa yana sakar mata murmushi,ta sake yi masa sallama ya amsa,ta zauna tana gaishe shi,cikin sakin fuska ya amsa mata yana tambayarta lectures,shiru suka yi na wani lokaci kafin yasa a kawo musu drinks,ta kalleshi tace “Bana shan komai fa”,ya kalleta zai yi magana tace “Ai mun sha tare da su Sarah” ya tab’e baki kad’an bai kulata ba yasa waiter ya kawo,ya tafi kawowa tayi shiru tana tunani,ya d’an buga table d’in kad’an,tayi saurin kallonsa yace “Yaya ne.!?” Ta girgiza masa kai tace “Nothing” yace “Allah ya sa” tayi saurin kallonsa saboda kalmar daya fad’a sai taji kamar Nuraz ne a gurin,tayi shiru ta sunkuyar da kai ya katse mata tunani “Ehmn.! Wane labari ne kike son fad’a min.!?” Ta d’ago da sauri tana had’iyan wasu irin terrified saliva’s,a hankali tayi blinking idanunta tace “My story” ya gyara zama yana murmushi yace “Wawhh.!” Tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya yace “Kin yi shiru,and u know am eager naji” ta d’anyi calming kanta sannan a hankali ta fara fad’a masa,tunda ta fara yake kallonta da wani irin yanayin tausayinta a idanunsa har ta gama,fuskarta da hawaye sosai ta d’ago idanunta for da first time tunda ta fara magana ta kalleshi,yadda ya zuba mata idanunsa ko k’iftawa babu yasa taji duk guiwoyinta sunyi sanyi,a hankali cikin mutuwar jiki ya ciro handkey ya mik’a mata,ta karb’a a hankali ta goge fuskarta,ta mayar masa ya karb’a yasa a aljihu,kusan mintuna biyar taji bai ce komai ba,ta kalleshi yayi shiru da alamun tunani yake fuska da damuwa,kamar za tayi magana Sarah ta k’araso ta musu sallama,Nusrah ta kalleta tana k’irk’iro murmushi,suka gaisa da Aatif ta kalli Nusrah tace “Baby we will go home” Nusrah tace “Ku jira mu wuce tare sai ku sauke ni a hanya” Sarah za ta amsa Aatif yace su tafi zai kaita gida da kansa,tayi saurin kallonsa za tayi magana taga bai kalleta ba,suka yi sallama da Sarah,tana zaune su Maria suka zo wucewa,suka yi waving d’in juna tana kallo suka fita daga cafeteria,a hankali tayi ajiyar zuciya,bayan tafiyarsu babu jimawa Aatif ya mik’e yace “Muje na kaiki gida” ta tashi bata ce komai ba har suka fito inda yayi parking,ya bud’e mata front seat ta shiga,ya rufe ya koma side d’in driver ya shiga,sai daya fara sa seatbelt sannan ya tada motar suka fara tafiya a hankali har suka fita daga skul d’in,a bakin apartment d’insu ya tsaya,da wani irin murya ya rarrasheta,after ya nuna mata shi ita yake so ba komai ba,suka yi sallama yace idan ya isa gida za suyi waya,ta masa fatan komawa lafiya,a hankali ya d’age glasses yayi reverse tana d’aga masa hannu,har ya kusa fita daga arean sannan ta juya zata shiga gida,ta fara tafiya ta hango motar Nuraz tana shigowa line bata tsaya ba ta shige ciki.

Tun da ta dawo ta shige d’aki tayi zamanta a can tana jiran kiransa,har after maghreb bata sake fitowa ba,sai da Lolly tayi kiranta jin shirun ya yi yawa,ta fito rik’e da wayarta ta zauna kusa da ita,Lolly ta kalleta tace “Ke kam baby kina jin dad’in zama kiyi shiru,shi kenan shi mutum sai yayi ta zama cikin d’aki shi kad’ai” tayi murmushi bata ce komai ba,wayarta ta duba taga ko Aatif ya kirata,taga babu alamun miss call akai,ta bud’e network ta fad’a duniyar gizo²,nan ma ta duba babu sak’onsa,tayi shiru tana tunani,har to 11 tana zaune shiru duk bayan mintuna ta sake dubawa ko ya kira sai taga bai kira ba,zuciyarta ta damu sosai,Nuraz ya saci kallonta ya ganta a damuwa,yayi shiru yana tunanin yadda zai tambayeta ko ta samu sun yi maganar da shi.!?,idea ya zo masa ya d’ago yana niyyar tambayarta ta mik’e tana k’irk’iro hamman k’arya tace “Aunty good night” ta kalleta tace “Toh.! Angel sai da safe” ta kalli Annie tace “Annie sai kin shigo.” Ta gyad’a mata kai tana lumshe ido,ta yiwa Bareerah sallama ta wuce,har ta tafi idanunsa suna kanta,ya rasa me zaice da zaisa ya bar wajen ba tare da su Annie sun gano shi ba,zuwa wani lokaci ya mik’e shima yayi musu sallama,ya wuce bedroom d’insa…..

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

DAN MACE CHAPTER 4

SOYAYYAH CHAPTER 1