in

DAN MACE CHAPTER 3

DAN MACE CHAPTER 3

DAN MACE CHAPTER 3

Gefe guda ta samu ta tsaya da tunanin yadda za tayi ta samu damar yin magana da ni,ta jima sosai tsaye tana kalle² da tunanin wanda zata aika ya kira ni,tana nan tsaye ta rasa mafita k’arshe taga tana b’ata lokaci,ta yanke shawaran zuwa da kanta,,ta nufo k’ofar gida tana tunanin idan ta samy Baba a gida kuma fa.!? suka kusa bugar juna,yana k’ok’arin fita zuwa wajen taron su na siyasa,tayi saurin komawa baya muryarta na rawa tace “Kayi hak’uri Baba,ban san kana hanya ba”+ Ya kalleta ya d’aure fuska cikin hayaniya yace “Wa kika zo nema a nan.!?” Tayi shiru tana sunkuyar da kanta k’asa,a bakin hanya ya
kafe ya kama waist ya k’i matsawa,ta d’ago a hankali tana gaida shi,bai amsa ba sai tambayar daya sake jefo mata “waye tazo nema a gidansa.!?” Ta daure tana jin fad’uwar gaba sosai tace “Baba na zo naga Yaya Maryam ne” Ya kalleta kamar zai yi magana ya fasa,cikin gidan ya wuce ya barta a tsaye,zuciyarta a lokacin har ta fara saka mata Baba ya tafi ya kira mata ni,kamar yadda tayi zato haka ce ta faru sai dai sab’anin da aka samu,ko da Baba ya sako ni a gaba muna fitowa ya kalleta yace “Ita ce wannan.!?” Hauwa ta gyad’a kai tana kallonsa idanunta cike da hawaue,Baba ya juyo ya kalkeni yace “Maryam kin san wannan.!?” Jikina yana b’ari na amsa na santa,yace “Wace ce ita kuma mene ne alak’ar ku.!?” Nayi shiru ina tunanin tambayar da amsar daya dace na ba shi,ya daka min tsawa,cikin hargari yace “Ba da ke nake magana ba dan uwarki” Ban iya kallonsa ba nace “Na santa” yace “A ina.!?” Nace “A nan gidan” Ya girgiza kai “ita wace ce d’inki.!?” Na d’ago kaina na kalli Hauwa a sanyaye nace “Y’ar uwata ce.” Wani irin girgiza kai naga babanmu yana yi,kafin ya juyo kaina yace “Maryam.!” Na amsa “Na’am” yace daga yau “ita ba y’ar uwarki bace” Na d’ago zanyi magana baba yace “Kul! Kika ce min wani abu,yanzun nan zan sallamaku duka” nayi shiru ban ce komai ba,ya kalle ni yace “kin ji me nace!?” Na girgiza kai” yace “Daga yau na haramta miki zama ahalinta,na raba ku rabuwa ta har abada,idan ta sake zuwa ta aika a kira ki,kika kuskura kika tsaya magana da ita Allah ya isa ban yafe miki ba,kuma wollahi thumma billahi,kinji rantsuwa ko.!?” Na girgiza kai da sauri cikin tsoro yace “Sai kin bar min gidana,daga ranar ina so ki d’auka ni ba mahaifinki bane,tunda kin zama mara jin maganata” Ina kuka ina kallon Hauwa da tausayawa,baba ya wuce ya barmu tsaye a nan kamar wad’anda aka sassak’a,kusan zan iya cewa gara ni na samu hawaye sun zubo min,amma ita Hauwa tunda ta kafe a nan Allah kad’ai ya barwa kansa sanin abunda ya faru da ita,tana raye,suma ta yi ko ta mutu Allah shi ne masani,,bayan tafiyar Babah da jimawa yayi tunanin ya aiko yaro ya duba masa na shiga gida ko ina nan,yaro yazo ya koma ya fad’a masa ban tafi ba,sai ganin Baba nayi ya dawo da kansa cikin fushi,ina ganinsa na matso da sauri ina kuka zanyi magana tun kafin na bud’e baki cikin fad’a kamar zai dake ni ya korani gida,ina tafiya ina waiwayen y’ar uwata kamar ba zan tafi ba haka har na shiga gida,baba ya koma kan Hauwa da fad’a ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba,sai daya tabbatar ko zuwa unguwar ba lallai ne ta sake yi ba,sannan ya juya ya barta,,cikin tsananin tashin hankali bayan dogon lokacin da ta d’auka cikin halin da bata san a wace duniyar take ba ta ja k’afafunta da kyar ta shiga shop d’in dake a nan line mu ta siya Biro da takarda,doguwar wasik’a ta rubuto min mai d’auke da duk wani abu daya faru da ita a zaman da tayi da Rafeek da ahalinsa,a k’arshe ta rok’i alfarmar na nema mata yafiyar Baba,,bayan ta tabbatar sak’onta ya iso gare ni ta juya ta bar unguwar zuciyarta cike da k’unci. Ina cikin gida bak’in cikin abunda ya faru ya same ni,d’an sak’on data aiko ya kawo min wasik’a,na warware bayan na keb’e kaina na fara karantawa,tun ban yi nisa karantawa ba hawaye sun wanke min fuska,na daure na karanta,lokacin da Baba ya dawo na je masa da wasik’a,dana fad’a masa duk abunda yake faruwa ya nuna bai yarda ba,na karanta masa

takardar da ta aiko min. Baba ya kalle ni ya jinjina kai yace “Na ji wannan tatsuniyar,,sai dai abunda nake so ki gane Maryam ni ban amince haka ta faru ba,kuma ko na ce na yarda shin zancen ya wuce ko.?” Na girgiza kai nace “Ehh.! Baba” Ya kalle ni yace “To ban yarda ba..” Na d’aga kaina nace “Saboda me ba zaka yarda ba Baba.!? Kai nefa ka haifemu dukan mu,ka san halin kowa a cikin mu,duk abunda za mu iya aikatawa ka san shi haka ma wanda ba za mu iya ba” Baba yayi min kallon banza yace “Idan na yarda shin sauran mutanen gari za su yarda.!? Ko kuwa su d’inma za ki bisu da takarda ki karanta musu ne.!?” Na girgiza kai cike da bak’in ciki,baba yace “Though tunda kin san da haka,ko da wasa kada ki sake nufo ni da irin wannan shirmen,na riga na yi muku shamaki da juna,idan har kin d’auke ni mahaifi ki bi maganata,idan kuma y’ar uwarki kike son bi,k’ofa a bud’e take dan na cire y’ay’a biyu daga cikin ahalina ba abune da zai tada min hankali ba,zab’i ya rage naki ni ko ita.!” Nayi shiru ban iya cewa komai ba,Baba yace “Za ki iya tafiya idan maganar da ta kawo ki kenan” jiki a sanyaye na juya ina ci gaba da kukan zuci har na koma d’aki,babban abunda yafi damuna ya tayarmin da hankali a lokacin ba komai bane,illa rashin sanin address na inda Hauwa take,tunda ta kama hanya ta tafi kuma ko a labari banji wani mutum d’aya da ya zo yace ya san inda take ba,a haka kwanaki suka yita zuwa suna wucewa ba tare da na samu wani gamsashen labarin inda kuka nufa ba,,na ci gaba da rayuwa a gida amma fa tamkar mutum-mutumi na zamewa y’an gidanmu,idan aka yi min magana daga Umm sai um’um,na daina shiga maganar kowa,idan hayaniyar su ta tashi can suke yin abunsu su kad’ai,,kullum cikin jiran tsammani da tunani nake naji ko da wucewarta ne wani ya zo yace min ya gani,amma shiru tamkar an shuka dusa har muka cinye sama da sati biyu. 3 Month later… Laying and rising is loss of living,haka nan a gurin ubangiji a year is like a day,cikin hukuncin ubangiji tun daga wannan tafiyar da Hauwa tayi sai ya zama bata sake tunanin waiwayar gida ba saboda abunda ya faru tsakaninta da Baba,bayan tafiyarta babu jimawa damuwa tayi mata yawa,har ya zama ciwo ya fara k’ok’arin kayar da ita,tun tana yi a tsaitsaye taba jurewa har lamarin ya so fin k’arfinta,damuwa da fargabar abunda zai iya faruwa da rayuwarta yak’i barin zuciyarta ta samu nutsuwar sake dawowa,ta ga al’amarin still ba mai k’arewa bane,duk da tsoron dake tare da ita ta sake yanke shawaran dawowa ko da zai kasance skasance wannan shi ne zuwanta na k’arshe,but ta gwammace zuwan da ace ciwo ya yi ajalinta ita kad’ai a gurin da babu wani cikin ahalinta,cikin y’an watannin ta yi wani irin ramewa ta yi duhu kamar ba ita ba,duk wanda ya santa idan ya ganta a wannan tak’aitaccen lokacin na tabbata zai yi wahala lokaci d’aya yayi saurin ganeta,ta kamo hanyar K’ofar Na’isa a karo na biyu cike da fargaba,but data tashi zuwa wannan lokacin sai bata yi k’ok’arin shiga gida ba ko nema na,ta sake aiko min wasik’a,ina zaune cikin d’aki jigum sak’on ta ya riske ni,na karanta naga fiye da rabin maganarta akan na nema mata yafiya ne a gurin Baba,sai sauran mutanen da nasan wani mu’amala ya tab’a had’a su,ina kuka ina karamtawa har na zo inda take barmin wasiyya tana sanar min ta jima ba ta da lafiya na taimaketa na nema mata alfarma gurin Baba na zo na ganta ko da sau d’aya ne kafin ta Allah ta kasance mata,a wannan wasik’ar nayi gamo da tsananin tashin hankalin da ya wuce tunani na _”Kiyi hak’uri y’ar uwata.! Babu yadda zanyi,ya zame min wajibi na sanar miki,duk da na san kema ba laifinki bane da kika kasa zuwa inda muke,,a halin da nake ciki,bayan dawiwa ta ciwo ya ci k’arfina,ina jin kamar ba zan rayu ba,idan haka ya kasance ina rok’on za ki nema min alfarma a gurin Baba,idan ya barki ko da a shek’ara sau d’aya ne zan yi alfahari da hakan,kema ina fatan za ki je ki duba min yarona,ban san yadda rayuwa ta zata kasance ba,shi yasa na yanke shawaran sanar da ke tun yanzun,zan kai Nuraz orphanage,idan kin samu dama dan Allah Yaya ina rok’on ki kije ki ganshi,na san Yarona ba zai yi maraici ba idan kina raye,na san yana da wata mahaifiyar kamar ki kuma za ki kula da shi fiye da yadda zanyi masa,ni dai tawa ta zo k’arshe sai dai ina yi mana fatan mu kasance tare har a aljannah,idan na yi miki wani laifi ina neman afuwar tun daga yarinta har zuwa girma na,ki yafe min y’ar uwata… Allah ya k’addara saduwarmu.. BISSALAAM.!”_ Daga k’anwar

What do you think?

-1 Points
Upvote Downvote

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

DAN MACE CHAPTER 2

MU ZUBA MU GABI CHAPTER 1