in

DAN MACE CHAPTER 2

DAN MACE CHAPTER 2

DAN MACE CHAPTER 2

Murmushi tayi ta sake matsawa jikinsa ta rik’o hannayensa duka tace “Mene ne ya faru ne.!?” Ta nuna kamar bata san abunda yake nufi ba,fuskarsa d’auke da wani irin expressions da baka tab’a rarrabewa yake ci gaba da kallonta,muryarsa tana wani irin trembling yace “Mene ne wannan d’in.!?” Ya nuna k’aton cikinta,hannunsa d’aya dake rik’e a nata ta kai kan cikin ta dafe,suna kallon juna fuskar kowannensu da irin sak’on da take bayyanarwa ta fara masa magana in a calmness way “It’s a gift from Allah (S.W.T),he has blessed us with it..” Da
mamaki shimfid’e a fuskarsa ya gwalo ido yace “what.!?” Tace masa “yeah.!” Girgiza kansa yayi ya lumshe ido ya bud’e yace “how and when..!?” Tace “bayan tafiyarka babu jimawa ne na fara rashin lafiya,da Hajiya tasa likita ya duba ni shi ne yace ina da juna biyu..” Kallon mamaki still yake mata yace “Bayan tafiya na..!?” Da wani irin muryan dake nuna rashin gamsuwa da amsarta,tace “Ehhh.!” Still yake sake kallonta sai yayi shiru ya kasa cewa komai,ya d’auki tsayin lokaci cikin halin mamaki da tunani,jikinsa ta shige da damuwa tace “ain’t u happy with it.!?”,kallonta kad’ai yayi ya tureta daga jikinsa cikin b’acin rai,bai sake yin magana ba ya fita daga d’akin,fad’uwa gabanta ya dunga yi cikin tsananin tashin hankali ta sakko ta biyo bayansa,parlor Rafeek ya fito gaba d’aya ya kasa fahimtar yadda akayi ta samu juna biyu

“When did that happen.!?” Ya tambayi kansa a fili da muguwar damuwa,zuwan Maimunatu yasa shi saurin kallonta yana tambaya “Ke tun yaushe ne waccan bata da lafiya.!?” Maimunatu da murnanta tace “Yah ai tun bayan tafiyar ka ne” jinjina kai yayi yana shirin yin magana Hauwa ta rik’e masa hannu,a fusace ya juya yana kallonta ya fizge hannunsa,sake kai hannunta tayi zata rik’e shi ya buga mata tsawan da sai da ta firgita,hak’oransa suna datsewa da wani irin traction mai fidda sauti,muryarsa cike da warning yace “don’t u dare touch me.. I warned u” Cikin tsananin firgita muryarta na kyarma tace “to wai mene ne ya faru ne.!? Ni mene ne nayi maka kake fushi,ban san laifina ba,ya kamata ka fad’a min..” Harararta yayi yace “Really.!?” Ta gyad’a masa kai kamar za tayi kuka,jinjina kai yayi kafin yayi magana Hajiya da Abba’nsa sun iso,har Maimunatu ta kai rahoton su zo ba lafiya,shi ne fa da sauri suka fito daga site d’in Abba’n sunyi tunanin ma ko wani abu ya samu Hauwa,suna shigowa cikin parlor’n Hajiya taga Rafeek tsaye ya kasa zama ta fiddo ido da mamaki tana tambaya “kai kuma fa.!? Saukar yaushe.!?” Bai iya kallon mahaifiyar tasa ba yace “Yanzun.. Nazo” zuciyarsa duk babu dad’i “Amma shi ne baka ce za ka zo ba,sai dai mu ganka kawai.!?” Bai iya tankawa ba,yana ci gaba da kallon ta har lokacin da b’acin rai yace “Hajiya! When did she got pregnancy..!?” Murmushi Hajiya tayi dake nuna tsantsar jin dad’i ta tace “Bayan tafiyarka ne babu jimawa,so sai muka yi deciding mu b’oye maka saboda muna son maka surprise,yanzun kam ko shakka babu naga alamun ka ji mamaki da ganinta d’auke da juna biyun..” Ta k’arasa fad’a so excited,jinjina kai yake babu k’ak’k’autawa yace “K’warai kam naji mamaki Hajiya da na ganta d’auke da k’aton ciki,but still noe i don’t even know cikin na wane ne..!?” Kallon mamaki Hajiya suke binsa da shi yayin da shi kuma yake watsawa Hauwa wani irin lafiyayyen kallo mai kama da na tsana,Hajiya cikin rashin fahimta tace “Ban gane abunda kake nufi ba Rafeek,,ya kamata ka fito kai tsaye ka mana bayani,maganganun ka sun fara sa ni shiga rud’ani.” Yace “Nifa Hajiya ba wani abu nake nufi ba,kawai dai i was confused about her pregnancy..” Idanun su duka a waje suna had’a baki suka ce “Meh.!?” Yace “Ehh! Hajiya gaskiya i didn’t agree with…” Tsawa Hajiya tayi masa tun bai k’arasa ba tace “kai Rafeek kada ka mai damu wasu marasa tunani mana,cikin ne baka yarda da shi ba.? Kasan duk inda za’a je a dawo kai ne mammallakin cikin nan ko..? Idan ka ce ba naka bane yanzun ka yi min bayani na uban waye.?” “Ni dai Hajiya kiyi hak’uri amma ki daina cewa nawa.. Ni ban yi mata ciki ba.” Wani irin tashin hankali ne ya ziyarce ta tunda ta tsaya tayi shiru sai kallonsa take ta kasa cewa komai,maganar da yayi a lokacin yasa har bata san ta dawo gabansa ta tsaya ba she feels like the whole world where lost ta rik’o rigarsa bakinta,jikinta da muryarta suna kyarma tace “Rafeek kada kace haka,,cikin ka ne fa,kada kayi min haka,ka tuna ban san kowa ba a bayanka,,kada ka sake furta cewa ba naka ba ne..!” Fincike ta yayi a jikinsa cikin tsawa yace “kada ki rainawa kanki hankali malama,ni nayi miki cikin nan kike son cewa.!? Tun yaushe ne rabon mu da juna.!? And tsayin wane lokaci muka zauna duka bayan aurenmu.!? It’s just a week,after then na tafi na barki.. Ta yaya ne wannan zai zama nawa.!? Lokaci guda kanta yayi wani irin bugawa da kyar take ganinsa a idanunta saboda hawayen dake shirin zubo mata,taci gaba da girgiza masa kai “Rafeek kada kayi min haka.. Wollahi ban san kowa ba sai kai,believe me cikin nan naka ne..!” Tsawa ya sake yi mata cike da hayaniya yace “Na rantse da Allah kika sake cewa nawa ne sai na nakasta miki rayuwa,,how za’a kalli wannan uban cikin a kirasa nawa.!? Da yaushe nayi miki shi.!?” Gaba d’aya ya mance da kasantuwar iyayensa a gurin yake sakin layi babu kunya bare tsoron Allah,su kansu iyayen mamakin da suke bai wuce yadda ya dage yana musanta cikin a matsayin nasa ba,a yadda suka san komai ya faru su dai sun gama tabbatarwa kansu ciki nasa ne,so why shi d’in yake arguing zancen.? Why don’t him accept.!? Gaba d’aya sun shiga rud’ani sun kasa gane kan maganar. Maimunatu na gefe ta saki baki sai kallon d’an uwanta take ta kasa cewa komai tun da aka fara maganar,sai idan wani cikinsu yayi magana ta juya,ta kalli wannan ta kalli wancan duk ta zama wata speechless a

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

DAN MACE CHAPTER 1

DAN MACE CHAPTER 3