FmD4FRX3FmXvDZXvGZT3FRFgNBP1w326w3z1NBMhNV5=
Your Ads Here
items

ZUCIYA CHAPTER 10

ZUCIYA CHAPTER 10 <
Yau ce ranar da za'a fara gudanar da event, da sassafe Little da Habib sukazo suka d'auki Nafi, sunyi murna sosai da ganin juna sai dai Little ta damu da ganin yadda Nafi ta rame sosai, hatta Habib yaga haka, nan suka taho a hanya Little nata tsokanarta akan ta bata labarin makaranta, Nafi kam sai dai tayi dariya kawai. Haka sukai ta tafiya, Little duk ta isheta da labarin biki, Nafi kam shiru kawai tai sai yake da takeyi, daga kazaure zuwa kano ba wani nisa ne dashi ba amma saboda Little ta kyaleta da zancen bikin nan sai Nafi ta tsiri yin bacci a hanya, hakan yasa Little ta kyaleta sai dai ta maida akalar hirar tata ka Habib. Har suka iso gida Nafi dai idanunta a rufe suke. Tunda suka shigo kuwa tasan lalai biki yazo, dan gida ya cika da mutane, nan Habib yai parking su kums suka fito. Sun fara zuwa b'angaren Mumy suka gaisheta, cikin farin ciki ta kalli Nafi tace " 'yar makaranta kin iso? " Nafi ta d'aga kai, Mumy tace " kije kiyi wanka kice abinci ki huta dan yanzu kinsan da baki dayawa a gidan hutu bazai samu ba anjima. " Nafi ta amsa da to fuskarta cikin farin ciki, b'angaren su suka wuce tana isa ta fad'a toilet tai wanka kafin ta fito Little ta d'auko mata kaya a cikin sababin da Ashraf ya mata bata sa ba. Nafi tai murmushi sannan tasa kaya, taci abinci sosai daj gaskiya tayi rashin abincin gida, ta gama kenan Ashraf ya kira Little a waya, Nafi tanaji Little tace "Hello Yaya! " Taji gabanta yaa fad'i, jitai Little tace "eh ta dawo." sai kuma taji tace to amma yaya..... " Jin shiru yasa Nafi tasan ya katse wayar dan shi dama baya jira. Little tabi wayar da kallo sannan tace " wai kije ki gyaramai d'akinsa, yaba Habib makullin d'akin sannan inkin gama ki ajiye a gunki zai amsa. " Nafi tai murmushi sannan tace " To. " Little cikin b'acin rai tace " Nafi bakiji haushi ba? " Ta kalleta tace name? Little ta ja wani dogon tsaki tace " yau kika dawo bai tambayeki makaranta ba, sai ya saki aiki? " Nafi ta d'an harareta kad'an tace " ke kuma menene naki??? " Little ta kama baki cikin mamaki tasan Nafi indai abu ya mata ko bai mata ba bata tab'a magana sai dai tai kasa da kai, cikin mamaki Little tace " ba komai nawa. " Nafi ta mike tare da wanke hannu tai waje ranta wasai, farin ciki take zataga Ashraf. Da isarta b'angaren taga kofar a bud'e sannan ga kayayyaki nan a waje da alama gyara ma ake, nan ta tsallaka ta shiga falo, mata ta gani su hud'u suna ta jera sababbin kaya a falo, Nafi ta gaishesu, sai dai kowa kallanta yake cikin mamaki, wata daga cikinsu wacce kana ganinta kasan kanwar Umms ce ta d'aure tace " Yarinya ke kuma wacece? Kuma me kikeyi a nan. " Kallansu tai sannan tai kasa dakai, a zahirin gaskiya batasan me zatace ba bata kums san me zata kira kanta ba a gidan nan. Jitai ance " me kike anan ba aiki yasa ki ba? " Da sauri ta d'ago ta kalli inda ake magana Habib ne tsaye a bakin kofar d'akin Ashraf, a hankali ta wucesu zuwa gunsa. Habib ya mika mata makulli sannan yace " gimbiya meye naki na tsayawa? " Ta kalleshi tace " gaishesu nai. " Habib ya d'an matso kad'an yace " ki kiyaye kula mutane irin wannan kar abu ya rutsa dake kisani a tashin hankali. " Da mamaki ta kalleshi, ita zatai abu to shi kuma meye nashi na shiga tashin hankali??? Ta bud'e baki da niyyar tambayarsa kawai taga ya wuceta ya fita. STORY CONTINUES BELOW Bayansa tabi da kallo sannan ta shige d'akin Ashraf ta rufe. Ba shakka yan jere sun sha mamaki, wacce wannan zataxo ta shige d'akin Ashraf?? Itakam Nafi tana shiga ta cire hijabinta ta shiga gyara, ba laifi d'akin yayi kura, ta dad'e tana gyara d'akin kafin ta nufi toilet, ta wankeshi tas sannan ta wanke towel d'in dake ciki. Tana gamawa taji bayanta yad'an amsa, murmushi tai har hakoranta suka fito tace wato jikinki ya fara sanyi ko? Ai in a riga ne aikin dayaci uwar wannan ma batajin wahalarsa.1 Air freshener ta fesa a d'akin, sannan ta jawo mai d'akin ta kulle tare da zare makullin, sallama ta musu basu amsa ba itadai tai gaba. Yau Arabian nights za'ai, bayan magrib kowa ya shiga yin kwalliya ta gani ta fad'a, Nafi kam tana zaune tana karatu, Little wacce kawayenta sukazo sunata shiri. Kallanta Little tai tace " Nafi wai meye hakan? " Tace " name?" "kina ganin kowa yana shiryawa amma ke kina zaune sannan ga kayanki nan na fito dasu banga alamar kinada niyar sa wa ba. " Nafi ta kalli kayan, riga ce da wando sai doguwar riga ce baka (after dress) sai dai an bita da kwalliyar duwatso rigar tayi kyau sosai. Nafi cikin mamaki ta kallesu, kowa riga da wando yasa yanata kwalliya, tace " Little kinsan dai bazan iya fita a haka ba. " Little tai dariya tace " muma ce miki mukai a haka zamu fita? " Ta fad'a tare da ware mata after dress d'in tace "wannan zamusa. " Nafi tai ajiyar zuciya tace " zakuyi kyau nikam ba dani ba. " Little ta d'aga wayarta tace " shikenan bari na kira yaya nacemai kince wai ke bazaki iya zuwa gun bikinsa ba. " Da sauri Nafi ta mike ta kwace wayar, kawayen suka sa dariya. Nafi tai ajiyar zuciya tace " naji zan saka kuma zani sai dai ina gefe. Little ta d'aga mata kafad'a alamar wannan kuma ruwanki. Little da kanta ta zauna ta shiga yima Nafi kwalliya, itakam Nafi bataso gani take kamar ba mai bukatatarta a guri meye nata na wani kwalliya? Nafi tayi kyau sosai, dan zan iya cewa tun datazo birni bata taba yin kyau irin na yau ba, mayafin abayar Little ta nata rolling dashi, tayi kyau sosai da sosai, ba wani kwalliya na kuzo mu gani bane sai dai inkaga Little lalai bazaka tab'a cewa ba a birni take ba. Dukansu wando Ja suka saka, hakan yasa suka sai takalmi ja flat, sannan yar karamar jakar dake rataye a kafad'arsu ma jaa ce, sunyi kyau sosai dan ankon shigar su kad'ai sukai. Sun fita reras dasu, Little na rike da hannun Nafi, tun a gida ma duk wanda ya kallesu sai ya yaba musu, nan suka shiga d'aya daga cikin motocin da aka kawo na d'aukar mutane zuwa gun da za'ai event d'in. ¤¤¤¤¤ A can b'angaren Aneesa kam tana can gidan Aminiyarta ankira mai kwalliya tana tsantasara mata, ganin an kusa gamawa yasa ta d'au waya ta kira Ashraf. Sai data kusa katsewa ya d'aga, cikin salon jan hankali tace " Hubby ka shirya? " Yace " ku mata ai kune aka sani da shiryawa ni wani shiri zanyi? " Tai murmushi sannan tace " ka taho ta gidan su Abida sai mu tafi. Cikin mamaki yace " ban gane ba? " Ta kara shagwab'e murya tace " ba dama kai zaka kaine ba? Ai tare zamuje gun. " Yace " So? " Tace " so shine nake fad'ama ina gidan Abida kazo mu tafi tare. "1 Yace " ni na kasa fahimtarki, meye zaisa sai nazo mun tafi tare? " Mikewa tai ganin yana neman disgata a gaban kawayenta tai d'aki tace " yaya haka fa akeyi. " Yai d'an tsaki yace " in haka akeyi sai akace dole sai nayi? " Mamaki ya kamata tace "Yaya ka tab'a ganin Amarya taje gun biki daban ba tare da ango ba? " Yace " sai a fara a kanki dan ni kam ba driver bane babu kuma dalilin dazai sa inzo in d'aukeki keda kawayen ki bayan inada abinyi. " Idanun Anisa ne suka canza kala tace "yanzu dai kana nufin bazaka zo ba kenan Yaya? " Yace " ba wai bazan zo ba gaba d'aya, sai dai zaki iya zab'a in har nazo na kaiki to kuwa ina ajiyeki zanyi tafiyata. " Aneesa ta furzar da wani iska ta bakin ciki tace " shikenan zamuzo a motar Abida. " Bai amsa ba ya kashe wayar, bin wayar tai da kallo ranta a b'ace sai dai dan karsu gane yasa ta fito tana zumbure zumbure. Abida tace " Neesa ya akai? Ko keda Angon ne?" Ta kara tab'e fuska tace " wai suna tare da abokansa su kuma shine sukace wai inyi hakuri mu tafi dake akwai abinda zasu bashine da bazai samu damar zuwa d'aukana ba. " Sukasa mata dariya, Abida tace "sai kiyi hakuri ai uzuri ne. " Aneesa ta harareta sannan ta zauna akacigaba da kwalliya. An gama kwalliya suka taso suka taho, Amarya tayi kyau sosai da sosai dan maganar gaskiya Aneesa dama kyakyawace. A gun event kuwa, Amarya ta iso sai dai ango shiru, gashi ba dama ta shiga ta zauna ita kad'ai. Duk yanda Aneesa ke kiran layin sa san bai d'aga ba. Little ta taho rai a b'ace ta zauna kusa da Nafi tace " Nafi wlh yaya nema yake ya ja mana magana." Nafi tace " name? " Little tai ajiyan zuciya tace " an nemeshi an rasa kuma Habib yace " wlh yana cikin gun nan dan tare suka shigo. " Nafi da mamaki tace "an kirashi a waya? " "tun d'azu ake kiranshi amma shiru bai d'aga ba, gasu Mumy can da Umma kamar zasuyi fad'a. " Nafi wacce duk jikinta yai sanyi tace " a nemeshi mana to ko wani abun ne ya sameshi." Harararta Little tai tace " yaro ne shi? " Nafi ta mike da sauri bata ce komai ba kawai tai baya da sauri. Sauri takeyi tana tafe tana addu'a Allah yasa ba abu ne ya sameshi ba, duk ta gama rikicewa, sai kutsawa cikin kuryar gun ga gun ba kowa sai dai akwai fitilo suma masu d'an duhu. Nafi tana tafe tana waigewaige, saura kiris ta fa d'a kwata, Allah ya taimaketa sai dai takalminta d'aya ya fad'a, zare d'ayan tai ta rike a hannu. Ko kulawa batai ba haka taketa tafiya, yanzu kam har gudu take had'awa d'ashi jikake tim. Kafarta ta bige wani dutse ta fa d'i, mikewa tai batare data dubaba ko kula da kafarta wacce taji ciwo sai jini yake batai ba. Daga can bakin wani pool ta hango mutum a tsaye ya kurawa ruwan ido, tana ganinshi ta baya tasan shine, da gudu ta karasa inda yake. Ta tsaya kawai tana hakki, Ashraf ya juyo gabansa jin alamun mutum, Mamaki ne ya kamashi yake kallan Nafi. Idanun ta suka zubo da hawaye, tasa hannu ta share da sauri tare da cewa " ba abinda ya same ka? " Kallanta yai daga sama har kasa, kayanta duk sun b'aci, yabi kafar ta yabi da kallo duk jini ya b'ata kafar. A hankali ya matso daf da ita har tanajin numfashinsa, yasa hannu kamar zai rankwasheta a kai, da sauri ta runtse idanta kam. Ya girgiza kai batai auni ba taji ya sureta. Idanu ta bud'e cikin mamaki da tsoro, a can kan kujera wacce ake hutawa in anyi wanka ya ajiyeta sannan ya karasa bakin ruwan ya debo ruwa a hannayensa ya fara zuba mata a kafa. Gaba d'aya Nafi ta kasa d'auke ido daga kanshi, har ya gama d'ebo ruwa ya wanke mata duk da rad'ad'in da takeji sai leb'e kawai da take ciza, sannan ya kalli inda ta yanke, sosai gun ya shiga ciki da alama karfe ne ko kwalba ya mata wannan aikin, hannu yasa a aljihunsa ya ciro handkerchief sannan ya d'aure mata gun dashi. Mik'ewa yai tsaye sannan ya kalleta yace " zaki iya tashi? " Kai ta d'aga mai idanunta subyi tsuru tsuru, ta d'aga zata mike taji wani zugi a kafarta wanda sai da tayi 'yar kara saboda azaba, baya tai kamar zata koma kan kujera da sauri yasa hannu ya taro ta, idanunsu ne suka had'u da juna, Ashraf ya kalleta sannan yace " bakya gani ne? " Kallansa tai batare da ta amsa ba, ya girgiza kai sannan yace " taya zaki bari har kiji irin wannan ciwon? " Kasa tai da idanunta, saukar da ita yai ta koma ta zauna kan kujerar da ta mike. Harararta yai yace " yanzu ya kike so muyi? " Tai kasa da kai sannan tace " kaje kai ai jeranka ake ni zan karaso da kaina." Ta d'auka bazai tafi ba ganin ba yanda za'ai ta iya tafiya, amma ga mamakin ta gani tai yayi gaba, kallansa tai idanunta suka ciciko, ta sukunyar da kanta cikin rashin jin dadi. Batai auni ba taji kawai an sungumeta, a tsorace ta bud'e idanunta cikin rud'ewa tace " Yaya saukeni dan Allah. " Ya murtuke fuska yace " kina tunanin bazan iya ba? " Kai ta girgiza alamar a'a, sannan tace " tsoro nake kar wani ya ganmu a haka." Wani murmushin rainin hankali ya mata yace " ke dai kina tsoro kar Aneesa ta miki duka." Nafi tai kasa dakai sannan tace " Allah dagaske nake ka ajiyeni please." Bai kulata ba ya cigaba da tafiya, sun kusa isa filin gun sai ga Little da Habib sun taho ta gun suna Neman Ashraf. Daga d'an nesa kad'an Little taga alamun kamar sune hakan yasa ta karaso gun da sauri. Kallan mamaki ta musu, Habib ne ya karaso gun shima cikin mamaki yace " Ashraf meye hakan? " Batare da ya kalleshi ba yace " name fa? " Habib ya kalli Nafi wacce tai tsuru tsuru da ita yace " event d'in auranka fa akeyi? " Yace " ehen sai me? Abun haramun nai ko me? " Habib ya kara kallansu, sai dai amsar Ashraf yasa ma ya kasa magana, Little ta daure tace" yaya yanzu in mutane suka ganku a haka me kake tunani? " Zaiyi magana kenan sukaji ana zabga salati daga bayansu. Ashraf ya kallesu Umma ce da 'yan uwanta ga Aneesa a tsaye cikin tsananin mamaki. Ashraf wuce su Little yai ba tare da damuwa ba ya gifta su Umma sannan ya ajiye ta a kan kujera daga baya, sannan ya kalli Umma yace" Umma me kuke anan?? " "Kan jakar uba, abinda za ka tambayemu kenan? " Ashraf ya kalli Aneesa wacce ta fara hawayen bakin ciki sannan yace" naga kamar abun yara ne ban d'auka manya ma zasu zo ba. " A zuciye Umma ta matso tace " me kake aikatawa anan kai da waccan munafukar yarinyar a ranar shagalin bikinka? " Ya kalli Nafi cikin salon rainin hankali yace " wacce? Waccan yarinyar? " Umma ta kumbura kam, yai murmushi sannan yace" karamin accident ne ya sameta shine na taimaka mata." Umma ta kalli Nafi cikin kuluwa sannan ta kalli Ashraf tace " accident? Shi accident d'in bai tashi ba sai a ranar bikinka? Ko dai tsabar kinibibi da muafurci ne hakan? " Ashraf bai tanka ba ya kalli Aneesa da take kuka, matsowa yai kad'an sannan yace " muje ko mutane na jira. " Hawayenta ta share sannan cikin b'acin rai tace " Duk wayar danake ma baka d'auka ba dan kana tare da waccan ne ko me? " Kallanta yai cikin rashin kulawa yace " zakije ko kuwa in tafi? Dan naga kamar lokaci na kawai ake b'atawa anan." Wata 'yar uwar Umma ta kalli Nafi wacce tai kasa da kanta hawaye kawai takeyi, tace " waccan munafukar ai d'azu muna jere itace ta shiga d'akinsa ba kunya ta dade aciki kafin ta fito, kun tabbatar ba wani abu na masha'a tsakaninsu? " Umma ta kalli Ashraf sai dai gani tai kamar ma baisan me suke cewa ba waya kawai yake danna wa, zatai magana taga kamar tafiya ma zaiyi. Da sauri Habib ya rike hannunsa yace " Ashraf ka jiraya mana. " Hannunsa ya fizge sannan yace " zamanta nake? Ita har takai in mata magana taki tahowa? " Aneesa ta matso inda yake jiki a sanyaye tace " Yaya amma.... " Cikin fada yace " amma me? Ba ki yadda dani ba ko me? " Kai ta girgiza sannan tace " ba haka nake nufi ba. " Ya kalli su Umma sannan yace " to me kike nufi?" Tace " ba komai kawai dai dama. " Tsaki yai sannan yace " inzaki wuce muje to, in kuma bazaki ba ni inada gun zuwa. " Nan ya fara tafiya, Umma ta maka mata harara alamar kar taje, da sauri Aneesa ta d'auke idanta akan Umma tabi bayan Ashraf da sauri. Ran Umma ya b'aci sosai lalai ta kosa Aneesa ta auri yarannan insun samu kan dukiyarsa su salwantar dashi dan kuwa bazata iya jurar bakin cikin yaron nan ba. Kan Nafi suka dawo a zuciye, gashi Habib ya tafi, duk yanda Little ke ba umma hakuri amma inaa idanta ya rufe duka ta shiga yima Nafi ba ji ba gani, itakam Nafi hawaye kawai takeyi. Gaba d'ayawannan ranar mutane dayawa da bakin ciki suka taso daga gun nan. Su Nafi suna sauka a mota, Little ta sakala hannunta ta kafa'adarta suka nufi ciki,sai dai me? Suna shiga sukaga cincirindon mutane a tsakiyar farfajiya banda masifa ba abinda akeyi, Little ta kalli Nafi tace"ko me aka sake yi oho. " Ji sukai da karfi wata tace " dan kut...... Uban yarinyar ai karyata zakuyi ba barinta zakuyi ba. " Nafi kam ta rasa me yasa takejin gabanta na fad'uwa haka, jisukai ance " wai yarinyar ma daga ina take? Akan ke zaku yadda ta zauna a nan gidan? " Little ce ta kalli Nafi yanzu kam sun gane inda maganar a dosa, Little ta kalleta tace " mu wuce ciki. " Suna shiga ciki Little ta ajiye Nafi sannan ta fito tai gun Mumy. A zaune taga Mumy tayi tagumi ga 'yan uwanta suma sunata magana, Little ta karasa ta zauna kusa da ita tace "Mumy wlh ciwo taji a dalilin neman yaya, ganin bazata iya takawa ba yasa ya d'auketa. " Mumy tai ajiyar zuciya tace" Little ki fadama Nafi gobe ta shirya da safe a maidata makaranta saboda tsoron abinda mutane zasu mata dan nasan 'yan uwan maman Aneesa sarai bazasu tab'a barin maganar nan ba. " Little tai shiru jikinta yai sanyi sosai, sai dai tana ganin hakan ne yafi sauki. ¤¤¤¤¤¤¤¤ A kachako kuwa d'an litti ya zake sosai yana aikin kasuwancin sa na babur, yana kuma jin dadin yanda uban gidan sa yake sanshi, fatanshi d'aya yai sauri ya kammala kud'insa ya taho kano neman Ashaf........ Little jiki a sanyaye ta fito daga d'akin Mumy tai b'agarensu. A zaune taga Nafi kan sallaya, Little ta karasa gunta tare da sama a kusa da ita, Nafi ta kalleta sannan ta kakaro murmushi tace " Little nayi dana sanin zuwa bikin nan." Dafata Little tai tace " Laifinane dana d'aukoki duk da banga alamun kinasan zuwa ba." Kai Nafi ta girgiza alamar a'a kawai zatai magana taji kamar intai magana kuka ne zai kufce mata. Little ta d'au waya ta kira Ashraf, sai da ta kusa katsewa sannan ya d'aga tace " Yaya." Daga can Ashraf dake zaune kusa da Habib yace " uhm ya akai? " Kasancewar a kusa suke yasa Nafi tana iya jiyo maganar Ashraf, Little tace " dama fadama zanyi gobe Nafi zata koma inji Mumy." D'agowa Nafi tai ta kalli Little, jitai Ashraf yace " to Allah ya kiyaye." Little taso ya hana Nafi tafiya jin ya fad'i haka yasa jikinta yai d'an sanyi tace " Yaya wa zai maidata?" A zuciye yace " da wani karambanin ne ma yasa ku d'auko yarinya tana makaranta? Sai kuje ku sami wanda ya saku ku tambayeshi." Little zatai magana taji ya katse, jiki a sanyaye ta kalli Nafi wacce ke wasa da hannunta a zahirin gaskiya kalaman Ashraf sun mata zafi sai dai tasan koma meye ai laifin ta ne. Ta kalli Little tace taimakamin dan Allah in kwanta." Little ta kalli kafarta tace " Nafi ko muje Chemist? " Kai Nafi ta girgiza mata alamar a'a tace "bafa wani serious bane. " a zahiri kuwa tanajin zafin gun sai dai bataso a cire handkerchief d'in Ashraf daga kafarta. Little ta mike sannan ta shiga taimaka mata ta kwanta, idanu ta rufe kamar mai bacci, hakan yasa Little ta fito daga d'akin. Tana fita Nafi ta fara zubar da hawayen dake cinta, Ashraf ta tuno sanda ya d'auketa, idanu ta runtse kalaman Ferry ta tuna data cemata san Ashraf take, Nafi ta share hawayenta sannan a fili tace " Ina na isa? In kuwa har haka ne lalai ina cikin gararin rayuwa." Kalamansa na mota ta tuna dayace mata zai saketa in ta samu wanda takeso. Ta dad'e tana hawaye kafin bacci ya d'auketa. Washegari da sassafe kuwa Drivern Mumy ya mai da ta makaranta, ko Ashraf bata sa a idanta ba. Nafi ta dage sosai da ta koma makaranta, ba wai a kan karatu kad'ai ba sai dai kullum suna tare da Ferry tana kokarin canza halayenta. A wannan zuwa gidan datai lalai ta fahimci abu biyu, na farko Ashraf wasa kawai yake da ita da jawo mata tsana agun mutane bayan ba santa yake ba, na biyu kuwa lalai in har tanasan Ashraf ya fara santa sai ta zama mace daidai shi. A can kuwa an gama biki lafiya ankai Amarya d'akinta, sannan kowa ya watse. Anyi hutu amma Nafi ta kira Habib akan zata zauna a gidan Principal ya tambayar mata ita, saboda a lokacin hutun ta samu isashen lokaci na karatu, wannan jarabawar ita tazo ta karshe a aji batajin kuma za ta iya nunama Ashraf wannan dakikantar datai. Habib ya tambaya, ba tare da wani dogon Nazari ba ta amince, bayan kowa ya tafi gida itama ta koma quaters. Little taji ba dadi sai dai bayan Nafi ta mata bayani ta waya yasa ta gamsu. Nafi ta dage sosai...... STORY CONTINUES BELOW Shekararta d'aya kenan a makaranta, duk hutu ba ta wani zuwa gida, sai dai duk cikin hutu Little na zuwa ganinta da sakon Provision daga Mumy da kud'in kashewa. A iya wannan Shekara d'aya ba shakka Nafi ta canza sosai da sosai, ita da Ferry kam sun zama Aminai sosai, sai dai in a b'angaren karatu ne kuma da Jibiya sukeyi. Yanzu suna S1 Nafi ta canza sosai, bata tunani ko sha'awar zuwa gida duk da kuwa yanda zuciyarta take tsananin rashin Ashraf kamar ranta. Yanzu sun shiga Ss 2 a a wannan lokacin ne kuma Nafi ta shirya dan zuwa gida, Little tace "wannan karan kam gaskiya sai Nafi tazo gida, dan akwai bikin kawar Little ko ince Aminiyarta da za'ai. A wannan lokacin shekarun Nafi 18, duk da ba kiba gareta ba sai dai kirjinta ya cika da dukiyar fulani, Nafi ta goge sosai, kamar ba makarantar kwana take ba, komai nata tsaf dan in Little zata kawo mata kaya har da mayuka masu kyau take cewa ta had'o mata. Nafi tana tsaye kusa da Ferry ga Jibiya a gefensu, Nafi ta kalli Ferry tace " Na nawa kikai?" Ferry tai d'an tsaki tace " Ai Yaya Yusuf ya rainan hankali wai ta 7 dan tsabar rashin mutunci." Nafi tasa dariya ita da Jibiya, Ferry ta had'e rai tace " kubarni da abinda ke damuna." Jibiya ta sake dariya tace " lalai zakisha Fada'a gun Abba dan ni na 2 nai." Idanu Ferry da Nafi suka zaro, Nafi ta kalleta sannan ta had'a hannayenta ta tafa mata tace " wow! Jibiya kina kasheni." Ferry ta harareta tace " Zama ta raya ki, ke Feena na nawa kika ci?" Nafi ta juya kai tace " Secret." Ferry tai dariya tace " badai irin na last term ba na 12 ba?" Nafi ta d'an rangwad'a kai cikin tsokana tace " na 8 nai." Ferry cikin d'aga murya tace " WHAT?" Nafi tai murmushi tare da ware takardar, murna suka shiga yi sosai, can Ferry tace " Kai naji dadi kin daina cin double number, amma da alama sai na dage kar next term ki dawo gabana." Suka sakeyin dariya. Ferry ta kalleta tace " Feena zakizo d'in ko?" Nafi ta d'an juya ido tace " zanzo insha Allah amma banasan zuwa yayanki nanan." Ferry ta harareta tace " Gaskiya Feena bazan juri wulakantamin yaya da kike ba, tunda yazo visiting ya nuna yana sanki amma kike wani disgashi, in bakiyi wasa ba har gidanku zan kawoshi." Nafi ta zare ido tace " wa? Rufan asiri." Jibiya tace " kema kinsan bazata yarda wani saurayin ya bita gida ba saboda sanda takema yayan nan nata." Tsaki Ferry tai tace " wlh Feena in har kika bari ya gane kin mutu akansa haka lalai sunanki sorry." Nafi ta tsuke baki tace " Ke nima yanzu ba daina sanshi yaushe rabon ma da inganshi, kila ma ko a hanya naganshi bazan ganeshi ba." Ferry ta d'aka mata duka tace " ni zaki maida gara? Kullum fa sai kinyi labarin yayan nan naki." Nafi zatai magana ta hango kamar Little ta fito daga wata zukekiyar mota, tana sanye da sun glass tayi kyau sosai da sosai, Nafi tace " anzo d'aukana." Nan suka mik'e suka taimaka mata da kayanta, Ferry tundaga nesa tace " Kai Feena gaskiya Little tana kasheni da gayu, ki bari nika inje gida dattin makarantar nan ya fita daga jikina lalai zan tsorata maza." Nafi tace " Nima ki bari sai nazo gida kin ganni kiga yanda zan kasheki da nawa gayun." Dariya sukai harda tafawa. Sun karasa gun, Little ta karaso cikin murna, ta rungume Nafi. Sunsa kaya a motar sannan Nafi ta leka dan ganin wanda ya kawo Little. Habib ya sakar mata murmushi yace " Tantancewa akeyi ne?" Murmushi tamai itama tace " Ai ba sai na tantanceba dama can jikina yaban kai ka kawota." Nafi kenan ba shakka kim canza wato yanzu bakya kunyar maidamin kalamai na." Ta d'aga kanta batare da ta amsa mai ba, sannan sukai sallama dasu Ferry ta amshi number Ferry da jibiya tasa a wayar Little. Nan suka shiga mota, Habib jefi jefi yana kallanta ta glass d'in mota, ba shakka yarinyar nan ta girma, ganin haka yasa Nafi ta matsa daga setinshi ta koma ta can b'an garen. Little ce tace " Nafi yau ji kad'ai nasan farin cikin danakeyi, nayi missing d'inki sosai." Nafi tai murmushi sannan tace " nimafa kawai daurewa nakeyi jinake kamar na biyoki inkika zo ganina." Little ta harareta tace " ba wani nan kedai kawai kinzama 'yar college tafi gida dadi." Dariya suka d'anyi Nafi ta juya tan kallan window. Little ta juyo ta kalleta tace " Nafi au Feena baki tambayi ina yaya ba, ko visiting nazo bakya tambayarsa." Habib ne yai katsal yace " ita meya dameta dashi bayan yayi aure yamanta da ita." Har cikin ranta Nafi taji haushin maganar Habib amma sai ta daure tace " Ya Habib kenan, dama can ba wani shiri muke dashi ba balle ya nemini." Little ta kalleta tace " Nafi yanzu kin daina shigar ma yaya ne?" Ta tab'e baki tace " ni a wa? Dama can bawai shigar mai nake ba kece baki fahimceni ba, ai Yaya Neesa itace zata shigar mai bawai ni ba." Habib ya saki dariya yace " Gaskiya ne Feena gwara ki fara bayyana musu komai." Nafi ta kwantar da kanta akan window tare da lumshe ido, tace " Little bacci." Little ta d'an had'e rai tace " shikenan nayi shiru." Habib ya kalli Little yace " Ai cewa tai bacci bawai kiyi shiru ba." "Hmm ai tun da dadewa na gane Nafi au Feena in batasan magana sai tace wai bacci." Habib ya juyo ya kalli Nafi sannan yace "yarinyar nan ta canza dayawa." kai little ta jinjina tace " ai naji dadin makarantar nan." Haka sukai ta maganganunsu itakam tana kwance tana jinsu a cikin zuciyarta take magana " Yaya ba sai ka basar da ni ba, nafi kowa sanin rashin matsayi danake dashi agunka, kila ma inya ganni bazai ganeni ba, ba komai Allah ya kawomin wani mai sona nima inyi kokarin ganin na yakece wannan soyayyar da take one_side." Nace Uhmmmm zaki iya????.

0/Post a Comment/Comments

Recent Posts

Your Ads Here
73745675015091643
Your Ads Here
Your Ads Here