FmD4FRX3FmXvDZXvGZT3FRFgNBP1w326w3z1NBMhNV5=
Your Ads Here
items

ZEHRA CHAPTER 13

ZEHRA CHAPTER 13
hi.+ Ita dai ta rasa yadda zata yi da Mustapha, gaba daya ya kore mata samarin ta kuma gashi yau saura kwana uku lokacin da Papa ya bata su cika. Yanzu haka maganar Aure suke yi da wannan Alhajin domin kuwa ya sanar da ita ko gobe take so a shirye yake.4 Mustapha wanda ya shigo ofis din a yanzu composing kanshi yayi ya kalli Alhajin yace "Baba zan fadi maka maganar gaskiya" ya nuna Zehra yace "wannan da kake gani ba auren ka zata yi ba, cutar ka kawai zata yi coz she is a player" Cike da mamaki Zehra ta miqe tace "what?? Baby meye haka??"2 Da sauri Mustapha ya juya ya kalli Alhaji Yusuf yace "ka ji ko?? Ta kira ni da Baby bayan ni din tayi playing dina.. Anjima kadan wani zai zo ta kira shi honey.. qila kai darling tace maka ko??" STORY CONTINUES BELOW Cike da Masifa Zehra tace "what the hell.." ta kalli Alhajin wanda ya miqe ran shi a bace tace "don Allah ka tsaya ka ji Alhaji, Uhm.. I can explain"2 Alhajin ya daga mata hannu tare da fadin "haba dai Zee, wane explanation kuma banda wanda yaron nan yayi mun yanzun nan da kuma abinda na ji.." Mustapha wanda ya dan yi murmushi yace "ai kawai Alhaji ka kama hanya ka tafi kar ka fada tarkon ta... nima yanzu haka zuwa nayi don muyi settling scores da ita akan kudade na da ta cinye tunda ta yaudare ni"7 Alhaji Yusuf ya miqa ma Mustapha hannu suka yi musabaha yayinda yace "nagode qwarai yaro" Ya kalli Zehra yace "ke kuma Allah ya shirye ki, ni na tafi" Ko da Alhajin ya tafi gani nayi ta fashe da kuka yayinda tace "Allah ya isa tsakani na da kai" Yana dariya ya zauna a kan kujera yace "idan dai akan wadannan dattijan da nake kora zaki dinga yi mun Allah ya isa babu matsala My Angel" Cup of coffee din da yake gabanta ya janyo ya kai bakin shi yayinda yace "by the way I am glad you still acknowledge me as your Baby, you just made my day" Ran Zehra a bace tana kuka tace "ka tashi ka bar mun office dina, I hate you" Babu musu ya tashi yace "I love you my Angel" Gab da zai fita daga office din ne ya ji tana fadin "aikuwa duk zaka yi haukanka ka gama amma kamar yadda na fadi maka da in aure ka gwara na auri zabin Papa" Murmushi kawai yayi bai ce komai ba ya fice. Hidaya ce ta shigo ta tarar da ita tana ta rusa kuka. A yanzu dai ba sai ka tambayi Zehra dalilin kukan ta ba domin ba kowa bane banda Mustapha. Abin ma har dariya yake basu domin kuwa su gani suke yi kamar pretending kawai take yi. Hidaya wadda ta zauna ce tace "Yanzu muka gaisa da zai wuce... me yayi miki kuma this time?" Zehra wadda take kuka tace "wallahi na gaji da abinda yake yi mun, could you believe what he just did??" Daga nan ta ba Hidaya labarin abinda yayi yayinda Hidaya ta dinga kwasar dariya. Hidaya tace "gaskiya Babyn nan naki fa dan rigima ne, dagaske na amince da maganar babe dinnan da tace baya jin magana. toh amma kema ya akayi kika kira shi Baby a gaban Alhajin?" Zehra wadda take kuka tace "toh slip of tongue ne.." Hidaya wadda take dariya tace "slip of tongue?? Kullum?? Haba Zee, you still love this guy.... saura 3 days don Allah ki bashi go ahead mu sha biki" Zehra ta share hawayen ta sannan tace "never, zan amince da zabin Papa even if it will be against my wish afterall Papa bazai taba yi mun zaben banza ba"7 Hidaya tace "toh Allah ya sanya alkhairi" ************* Dayake ayyuka masu yawa suke da su a gaban su nan da nan suka shiga aikin su, hakan kuwa ya sa ta rage damuwar ta. Basu gama abinda suke yi ba sai bayan magrib. A lokacin kuwa mijin Hidaya ya zo ya tafi da ita a dalilin bata zo da mota ba yau yayinda Zehra ta kira Yunusa driver ta zauna zaman jiran shi. ************* Zaune take a ofis dinta tana duba laptop ta ji an turo qofa. Da sauri ta dago kai don tabbatar da qamshin da ta ji. Sanye yake cikin wandon jeans da baqar Polo T-shirt. Sossai yayi kyau wanda har ta kasa dauke idanuwan ta daga kan shi. Tana ta kallon shi ne ta ji yace "I am here to take you home.." STORY CONTINUES BELOW Cikin masifa tace "ka tafi ka bani wuri na riga na kira Yunusa" Murmushi yayi yace "ni nace mishi ya zauna zan dauko ki" Ran ta a bace tace "ban gama ba" Daga nan ta mayar da idanuwan ta a kan laptop din yayinda tayi kamar tana yin wani aiki. Gani nayi ya samu wuri ya zauna yayinda ya zuba mata idanauwa yana jiran ta. A ranta ne tace "aikuwa zaka gaji ka tafi" Shi kuwa ko da ya qura mata idanuwa soyayyar su a can baya yake tunowa. Zehra has changed a lot and its all thanks to him. A da fa duk abinda yace shi take yi ko da bata so amma yanzu gaba daya babu abinda take so irin bacin ranshi. One thing da ya sani shine tana son shi har yanzu.. Toh tambaya anan idan har tana son shi me zai sa ta dinga yi mishi haka?? Could there be a reason why she is displaying this attitude??3 Haka suka cigaba da zama yayinda yake ta kallon ta. Looking at her face a wannan lokacin, it's obvious she is exhausted amma saboda kar ta bi shi shine tayi qaryar bata gama ba. Wuraren qarfe tara da rabi na ga ya kalli agogo sannan ya miqe yace "time up" Bata ankara ba ta ga ya rufe laptop din yace "tashi mu tafi gida" Cike da masifa tace "bazan je ba.." Gani tayi ya zagayo ta gefen ta zai duqa ya dauke ta wanda kuwa ya san bazata taba bari ba. Nan da nan ta miqe tace "meye haka??" Yace "mu je" Tana kumbure kumbure ta janyo Hand bag dinta, tana kallon shi ya bi sockets din office din ya kashe sannan suka fita. ♤♤♤♤♤♤♤♤♤ Tunda suka kama hanya kuwa bai yi mata Magana ba, ita kuwa sai fushi take yi. Gani tayi ya dauki wata hanya daban wadda ba hanyar gidan Papa ba. saboda girman kai kuma ta qi tamabayar shi inda zai kai ta. Bata ankara ba ta ga ya shiga Barrack wanda kuwa bai tsaya ko ina sai quarters din Barrack din. Juyowa yayi ya dan kalle ta yace "dan bani five minutes please.. I will just come" Ko kallon shi bata yi ba har ya fita amma fa yana fita ta sa mishi ido... Hango shi tayi ya nufi daya daga cikin gidajen quarters din yayinda back men din da suke wurin suka dinga gaishe shi. Tana nan zaune ta hango shi ya fito tare da wasu su biyu. Gaba dayan su babu wanda ya kamo qafar shi wurin kyau da haduwa sannan he looked much younger than them. Ajiyar zuciya ta saki sannan ta kauda kanta ganin suna approaching. Bata ankara ba ta ji an bude qofar ta yayinda Col. A Yahaya ya dan duqo yace "finally honoured to meet you amaryar mu.." Cike da mamaki ta kalli Mustapha wanda ya kashe mata ido daya. Murmushi ta qaqalo tace "sannun ku ina wuni" Suka amsa yayinda Col. M Fahad yace "Gaskiya Tafida jinkirin ka ba a banza ba, Allah ya sanya alkhairi" Mustapha yana murmushi yace "ameen ameen, thanks much" Col A Yahaya ne yace "amma ranar Friday din zaka koma??" Yace "yes Insha Allah" Col M Fahad yace "kuma amarya zata barka ka tafi??" Mustapha yayi murmushi yace "ai she is an understanding person..." STORY CONTINUES BELOW Ita dai Zehra ta kasa gane abinda suke nufi. Ta rasa dalilin da yasa Mustapha yake deceiving kan shi akan maganar auren su. Ji tayi ya bude qofar baya ya dauko wani plan paper ya miqa musu yace "wallahi kun hana ni bacci jiya, I was on this throughout the night" Col M Fahad ne yace "mun gode qwarai Tafida, what would we have done without you??" Ya duqo ya kalli Zehra wadda take ta sauraron su yace "amarya a taya mu godiya, your Man is a life saver. A dinga kula mana da shi sossai da sossai" Murmushi tayi ba tare da tace komai ba. Gani tayi sun tafa hannu sannan yace "okay guys Allah ya taimaka, kar ku manta ku turo mun update. Allah ya tsare" Col A Yahaya yace "Insha Allah, Congrats in advance tunda bazamu samu halarta ba" yace "thanks" Daga nan suka yi ma Zehra sallama suka tafi. Aikuwa Mustapha yana shigowa motar ta balbale shi da masifa tace "wai meye haka?? Akan wane dalili zaka dinga fadi ma mutane ni amaryar ka ce?? Na ce maka kai zan aura??"5 Murmushi kawai yayi yace "yi haquri My Angel" Haka ta dinga masifa wanda kuwa bai ce mata komai ba sai dariya ma da yake ta kwasa. Shi kam Mustapha ko dama can yana bala'in son idan Zehra tana masifa.. Kyau take yi mishi idan tana yi. Da ta kula ma ta zama mishi abun dariya ne tayi shiru yayinda take ta kumbure kumbure. Haka ya kai ta gida ya sauke ta yayi tafiyar shi. ♤♤♤♤♤♤♤♤ Wani ikon Allah kuwa tun daga ranar bata qara ganin shi ba. A yanzu kuwa hankalin zehra yayi masifar tashi ganin dagaske dai Papa aure zaiyi mata. Sossai ta shiga tsananin damuwa musamman da ta ga ana ta shiri. Ita kam har ga Allah bata son auren nan musamman da bata ma san ko waye papa zai hada ta da shi ba. Ta yi mamakin yadda Mustapha ya fita batun ta. A tunaninta yadda ya bi ya kora mata samarinta zai matsa mata akan ta karbi tayin shi amma kuma sai ta ga gaba daya ma ya dauke qafa daga gidan nasu kwata kwata. Wani lokaci takan yi tunanin anya ba shi Papa zai aura mata ba?? Idan kuma ta tuno Fadeela ta fadi mata ranar auren nata zai koma Italy sai ta kawar da tunanin. Ita kam abinda dai ta sani shine gwara papa ya hada ta da koma waye banda Mustapha. 🤔🤔🤔🤔 ♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤ ABU-YAZEED RESIDENCE A yau ranar daurin aure, sossai gidan ya cika da baqi. Zehra dai a yau gaba daya ta zama very confused. Komai ta kasa yi. Fadeela da Hidaya kuwa sai matse dariyar su suke yi. Asali babu wanda ta fadi ma zata yi aure amma tana zaune sai ganin qawayen ta tayi sun zo hatta wadanda ta dade ma basu hadu ba. Ta sani sarai aikin Fadeela da Hidaya ne. Har bayan sallan Juma'a Zehra tana nan zaune a kan gado tayi tagumi kamar wadda aka aiko ma saqon mutuwa. Tun ana lallabar ta akan ta je tayi wanka ta shirya har aka gaji aka zuba mata idanuwa. Ana zaune ana ta hira a dakin ne wayar Fadeela tayi ringing. Ko da ta duba murmushi tayi sannan ta amsa da sauri. Ji suka yi tace "sweetheart how far, An daura??" daga nan suka ji tayi ihu yayinda tace "Alhamdulillah, finally.... Toh Allah ya sanya alkhairi. My regards to our latest ango. Bye"3 STORY CONTINUES BELOW Zehra wadda zuciyar ta take ta bugawa tana kallon Fadeela har ta kashe wayar sannan tace "Zee an daura auren ki..." Gani suka yi ta kwanta yayinda ta fashe da kuka tana fadin "na shiga uku, what have I done??" Sossai kuka ta dinga rusawa wanda kuwa qawayen ta suke ta mamaki. Yawanci qawayen ta sun zama confused har suna tambayar dalilin da yasa take ta rusa kuka haka when ita ta zabi mijin da kanta. (a tunanin su) Fadeela wadda ta rungumeta ta kai bakinta saitin kunnen ta tace "Zee please stop crying, na tabbatar Papa bazai zaba miki mutumin banza ba. remember he loves you very much. Yanzu don Allah ki tashi kiyi wanka ki zo ki shirya. Na ji ance Papa da kan shi zai kai ki gidan ki" Kusan awa daya ana ta lallashin ta wanda kuwa har sai da Anty ta shigo ta sa baki sannan ta tashi. Akan dole Zehra ta zauna Fati Mamza tayi mata make up sannan ta sa wani dinkin red aso-eke mai shegen kyau wanda deolasagoe ta dinka. Dukda ta ci kuka sai da Fati Mamza ta fiddo ta tsab. Charles shine ya dinga daukar hotuna wanda kuwa gabadaya ana wannan hidimar amma hankalin Zehra baya tare da ita. 5 Tunani kawai take yi yadda zata fara zaman aure a wani gida, sossai take missing Muhammad a yanzu domin kuwa da yana raye da har yanzu tana tare da shi. ♤♤♤♤♤♤♤♤♤ Da yamma ne aka fara shirin kai amarya wanda kuwa Papa da kan shi zai kai ta. Tunda aka ce mata ta fito kuwa ta dinga rusa kuka, Kuka take yi kamar ranta zai fita. Har mamaki take yi yadda ta amince aka yi mata auren dole when she has the right to choose. Zehra wadda take ta kuka a jikin Papa sai lallashin ta yake yi yayinda yake ta yi mata nasiha tare da gwada mata lallai bazata yi da-na-sanin amincewa da zabin shi ba. Bata ankara ba ta ji Yunusa driver yayi horn alamun an iso gidan. Abinda ya bata mamaki shine ko minti biyar basu yi da barin gidan su ba ace an kawo 'gidan auren ta' Why??? Da sauri na ga ta tashi daga jikin Papa yayinda zuciyarta ta buga, gaban ta kuwa yayi mummunar faduwa ganin gidan da suka shigo. Gidan Mustapha....6 Papa dai ji yayi tace "Inna lillahi wa'inna ilaihir raji'un, Papa don Allah kar ka aura mun shi, wallahi bazan iya zama da shi ba.. don Allah ka aura mun koma waye banda shi" Yunusa driver wanda yake sauraron ta kuwa ya cika da tsananin mamaki. Shi kam ace an kawo mace wannan gidan ai ko bata son angon ta haqura ta zauna ganin cewar zata huta.. sannan ma ya zata ce bata son Mustapha bayan kowa ya san farkon soyayyar su.. STORY CONTINUES BELOW A lokacin da ya faka a gaban porch din gidan kuwa yayi saurin fita don ya ba papa da 'yar tashi privacy. Papa wanda ya riqe ta ne yace "sssshhhhh, My Baby kiyi haquri ki saurari abinda zan fadi miki" Zehra dai tana ta rusa kuka yayinda ta ji yana fadin "Kiyi haquri da hukuncin da na yanke amma ina so ki sani cewar duk duniyar nan babu wanda ya fi cancanta ki aura da ya wuce Mustapha. Mustapha shi kadai zai riqe ku da gaskiya cikin amana da ke da Yasmeen, ko a lokacin da kuka rabu Mustapha bai daina son ki ba domin kuwa ko bayan Muhammad ya rasu ya nemi alfarmar idan akwai hali yana so ya aure ki wanda kuwa nayi mishi alqawari ba don komai ba saboda nasan bazai taba wulaqanta ki ba..." Zehra wadda take kuka tace "Papa wallahi hankali na bazai taba kwanciya a gidan shi ba, don Allah Papa ka mayar da ni gida... ni wallahi bazan zauna a nan ba" Papa yayi mamaki sossai na yadda Zehra ta canza gaba daya, A da yayi tunanin qarya take yi akan bata son Mustapha amma a yanzu ya tabbatar lallai dagaske take yi bata son shi... Toh meyasa?? Rungume ta yayi yace "My Baby listen to me, yanzu kiyi haquri ki shiga dakin ki. Nayi miki alqawari idan zaman naku bazai yiwu ba ni zan raba auren" Da sauri tace "dagaske papa??" yace "yes My baby.. Amma yanzu kiyi mun alqawarin zakiyi haquri ki shiga" da sauri tace "nayi haquri Papa.." Yace "Allah yayi miki albarka" tace "ameen Papa" Haka aka shigar da Zehra gidan ta yayinda ta quduri niyyar lalata auren tunda dai Papa yace zai raba su idan zaman ba mai yiwuwa bane. toh fa... Zee fa ta zama abinda ta zama🤣2 ♤♤♤♤♤♤♤♤♤ MUSTAPHA OMAR TAFIDA RESIDENCE 2 Wannan gida dai shi ake kira aljannar duniya, gida kamar an dauko daga turai. Gidan Mustapha Omar Tafida gida ne wanda a yanzu haka babu irin shi a Maitama. Babu shakka zaka iya samun wanda ya fi shi girma amma kyan tsari dai babu kamar shi.. Gida ne first class... tsayawa kwatanta maka gidan bata lokaci ne mai karatu. Gaba daya qawayen Zehra sunyi mamakin yadda ta bi ta tada hankalinta ganin wannan lafiyayyen Mansion din. A cewar wasu ma ko mijin gurgu ne zasu zauna da shi idan dai wannan gidan ne. Yusra ma sai zagin Zehra take yi akan sakarcin da take yi. A cewar ta wasu suna neman ko da rabin abinda ta samu amma ita tana jan aji bayan kuma kowa ya san qarya take yi tana son shi tunda dai sun san asalin soyayyar su. Sossai aka yaba ma gidan. Kusan dukkanin wadanda suka kawo amarya kuwa cewa suka yi sai sun kwana gidan. Su Anty dai bayan sun zazagaya ne suka sanya albarka suka tafi. Haka qawayen su suka dinga daukar hotuna a gidan suna ta posting a social media. ♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤ STORY CONTINUES BELOW Da daddare Zehra tana kwance a kan lafiyayyen royal bed na dakin da ya kasance nata tana ta kuka. 2 Da qyar Fadeela ta lallaba ta tayi wanka tayi shirin bacci, abincin ma da aka ajiye mata ta qi ci. Dayake qawayen su sun tare a visitors side babu kowa a side din Zehra din sai Khadeeja da Hidaya wadanda suke zaune a qaramin falonta suna kallon Zindagi ki Mehek a tashar Zee TV. (Indian series wanda suke following daily) Fadeela ce ta shigo dakin tana fadin "matar yaya, hope dai ba kuka kike yi ba har yanzu??" Zehra wadda ta ji Fadeela ta kira ta da matar yaya kuwa qara fashewa tayi da sabon kuka. Fadeela ta qarasa kan gadon ta kwanta kusa da ita tace "haba Zee, don Allah kiyi haquri... babyn ki ne fa. Abinda ya faru a baya ya riga ya wuce. The guy has suffered enough, I know you still love him please kiyi haquri ku zauna tare ku cigaba da gina soyayyara ku da kuka faro foundation dinta tun shekaru da suka wuce" Bata bari Zehra tayi Magana ba ta cigaba da fadin "zo mu je ki ga wani abu" Daga nan ta janyo hannunta ta taso babu shiri. Gani nayi Fadeela ta sa hannu ta share mata hawayen fuskar ta yayinda tace "mu je" Zehra wadda ta dakatar da Fadeela tace "ina zamu je? Kin ga kayan da ke jikina kuwa?? Bari in dauko hijab" Sanye take cikin wata sleeveless silk nighty red colour wadda ko cinyoyinta bata gama rufewa ba. Ga gashin kanta duk yayi buzu buzu, ga kuma kuka da ta sha wanda yasa fuskar ta tayi ja.. amma fa dukda haka nan tayi masifar kyau. Da sauri Fadeela ta riqo hannun ta tace "no wait.. manta da Hijabin. Ba fa wani wuri zamu je ba besides babu kowa a gidan aside qawayen mu kuma suna visitors side, mu je kawai in nuna miki mu dawo" Haka Fadeela ta janyo ta suka fita. Tafe suke yayinda Zehra take qare ma gidan kallo, sossai gidan yayi masifar kyau, wasu abubuwan ma tana kallon su bata gama tantance ko meye ba. 4 STORY CONTINUES BELOW Gani tayi sun haura wani stairs wanda ya sada su da wani qaramin farin falo... more like a sitting room. 3 Gaban ta ne ya fara faduwa yayinda tace "dee ina zamu je ne?" Bata ankara ba ta ji Fadeela ta janyo ta yayinda ta yi karo da wani abu. Ji tayi Fadeela tana fadin "here is your bride" Kafin ace wani abu kuwa Fadeela ta bar falon a guje yayinda take ta kwasar dariya. Zehra wadda qafafuwan ta suka yi sanyi da sauri ta ja baya yayinda jikinta ke ta rawa. Mustapha wanda hannuwan shi suke cikin Aljihun sweatpant dinshi ne yake ta kallon ta sama da qasa cike da so da qauna. Mamaki yake yi yadda ta fito a hakan domin kuwa nighty din ta kwanta a jikinta yadda gaba daya curves dinta suka fito... sa'ar ta daya kuwa ba see through bace. Zehra wadda take ta kallon slippers din da ke qafafuwan shi da kuma yadda slippers din yayi fitting lafiyayyun qafafuwan nashi bata ankara ba ta ga ya fara takowa zuwa gareta. Ganin haka kuwa ta fara ja da baya. Haka ya dinga approaching dinta yayinda take ta ja baya cike da tsananin fargaba. Bata ankara ba ta ji ta kai bango alamar no going further. Aikuwa nan da nan jikin ta ya dauki mugun rawa yayinda ta runtse idanuwan ta. Mustapha wanda yake ta murmushi hannuwan shi biyu ya sa a jikin bangon yayinda ya duqo saitin fuskar ta yana qare mata kallo. Shi kam a yau dinnan ji yake yi kamar anyi mishi albishir da gidan aljannah. His biggest dream just came true. Zehra is officially his' Har yanzu gani yake yi kamar a mafarki. Sossai ya cire rai a samun ta amma sai gashi destiny brought them back together. Zehra dai da ta ji shiru ne na ga ta bude idanuwan ta ahankali yayinda ta ga fuskar shi just few inches away. A razane ta mayar ta rufe yayinda bugun zuciyar ta ya qaru. Sossai qamshin turaren shi ya cika ta yayinda ta kasa motsi. Gani nayi ya kai bakin shi daf da goshin ta yayinda ya fara addu'a kamar haka: "Allahumma inni as'aluka khairahaa wakhaira maa jabaltahaa alaihi wa a'udhu bika min sharrihaa wash-sharri maa jabaltahaa alaihi.." Bayan ya gama ne ya kai bakin shi saitin kunnen ta yace "congrats Mrs M. Tafida, what a dream come true for us..." Zehra dai sai rawa jikin ta yake yi yayinda ta ji ya cigaba da fadin "....I am going back to Italy right now, nan da wata biyu zan dawo. Please take care of yourself.. and always remember that your Baby loves you very much" Bata Ankara ba ta ji hannun shi a cikin gashin kanta yayinda yayi placing mata peck a kumatu. Abinda yayi next ne ya sa tayi suman tsaye. Kiss yayi mata a kan lips dinta.. dukda it was a light one sossai jikinta ya mutu murus. Idanuwan ta a rufe ta ji Click na Camera alamar yana snapping dinta hotuna. Bayan ya gama ne ta ji yace "I love you my beautiful Angel... Ni na tafi" Ya shafa fuskar ta sannan ya juya yayi tafiyar shi.3 Aikuwa yana fita na ga ta fashe da kuka. Fadeela wadda ta hauro ta tarar da ita tsaye jikin bango tana ta rusa kuka kamar ranta zai fita. Da sauri ta qarasa wurinta tace "Zee lafiya??" Ji nayi tace "wallahi bazan iya zama a gidan nan ba... Papa yayi gaggawar raba auren nan don bana son shi"1 ♤♤♤♤♤♤♤♤ Sossai ran Zehra ya baci ganin cewar ashe kayan lefen da suka hado a dubai nata ne.2 Ta ji haushi sossai na yadda aka yi playing dinta har aka yi auren ta da Mustapha. Ta rasa dalilin da ya sanya aka yi mata hakan bayan ta fadi musu bazata zauna da shi ba a matsayin miji. Zehra dai har papa sai da tayi confronting dinshi akan rashin adalcin da aka yi mata wanda kuwa ya tabbatar mata da idan har ta bashi qwaqwarar dalilin da yasa bata son zama da Mustapha kuma ya gamsu zai raba auren. Tana da dalilinta but she couldn’t tell anybody... why??? Da wannan kuwa Papa yayi dismissing case dinta. A yanzu haka kwana biyu da tafiyar Mustapha ne Anty ta gayyato Layla Hayat wadda ta tare a gidan Zehra. Zehra dai akan tilastawar Anty ta amince Layla ta fara aikinta a kanta. Adda Ummie da Sareenah har gidan Mustapha suka je don ganin amarya Zehra. Abin mamaki ta sakar musu fuska sunyi hira sossai. Sun yini a gidan sannan suka tafi.. A cikin satin suma suka koma Italy. Khadeeja ce take zama tare da Zehra har zuwa lokacin da Mustapha zai dawo. Hakan kuwa yayi ma Khadeeja dadi domin kuwa bala’in son gidan take yi. Daga nan take zuwa school cikin motar ta da Papa siyo mata tunda ta iya tuqa mota. ♤♤♤♤♤♤♤♤♤ MUSTAPHA OMAR TAFIDA RESIDENCE Kwance take a kan kujerar qaramin falonta da yamma yayinda hankalin ta yayi nisa a kallon wayar ta. Bata ankara ba ta ji sallamar Fadeela wadda dawowar ta kenan daga ofis. A yanzu haka Zehra haushin Fadeela da Zain take ji domin kuwa ta gano su ne suka hada plan din da har aka kawo ta gidan nan. Fadeela wadda take murmushi tace “haba Zee, ai ko ba komai dai kya amsa sallama ko?” Zehra ta danna mata harara tace “ai ba dole bane sai kin ji” Fadeela tana dariya tace “toh Angel, ya gida?? Wallahi zan je gidan Papa karbar wani saqo ne nace bari in biyo in gan ki” Zehra dai bata ce mata komai ba. Fadeela tana kallonta tace “kai gaskiya Layla Hayat tana aiki mai kyau, kin ga yadda kika koma kuwa hajiya?? Ga qamshi ta ko ina..” Zehra dai miqewa tayi ta wuce daki ba tare da tayi ma Fadeela Magana ba. Wayarta da ta bari a falon ne ta fara ringing yayinda Fadeela ta matsa ta duba don ganin ko waye. Lambar turai ce wadda ta tabbatar mata da lallai Mustapha ne. Kai tsaye ta amsa yayinda ta ji ya saki ajiyar zuciya yace “haba My Angel, wayar ma kullum ina ta kira ba kya amsawa?? Wai me nayi miki ne to deserve all this??” STORY CONTINUES BELOW Fadeela wadda ta fashe da dariya tace “Ayyah yayana yi haquri, mu ma nan duk tayi fushi da mu saboda ta gano plan din da aka yi. Gashi nan na zo gidan ta tashi ta shige daki ta barni ni kadai” Ji tayi yace “wai me kike tunanin nayi mata da take yi mun haka?? Wallahi ban taba sa ran cewar she is serious about not wanting to be my wife ba... A tunaninki dagaske ta daina sona ne?” Fadeela wadda ya bata tausayi tace “zan iya rantse maka she still loves you very much, kawai dai gani nake kamar she is scared of something ne” Cike da mamaki yace “scared of what??” Tace “that’s for you to find out Ya Musty” Yace “toh ni da ko maganar arziki bata yi mun balle har in san ko meye” Tayi murmushi tace “I am sure idan ka takura ta zata yi maka revealing komai, just hurry up and get back home already..” A haka dai suka cigaba da hira har suka yi sallama. Fadeela dai tana kashe wayar ne ta ga abin mamaki a fuskar wayar Zehra. Hoton Mustapha wanda aka dauke shi tun ranar bikinta kafin yayi tafiya zuwa maiduguri. Hoton da aka yi snapping dinshi yana dariya which is all thanks to Muhammad Allah ya jiqan shi. Wannan hoton kuwa hatta Daddy yana da shi domin kuwa kowa ya sani a wannan lokacin zai yi wuya ka gan shi yana dariya. Zehra ce kadai mai sanya shi dariya and she wasn't even there. Sossai aka yi mamakin yadda photographer din ya samu shot din a wannan lokacin.  Girgiza kai tayi tace “kina zama kina sa hotunan shi a gaba kina kallo amma idan ance kina son shi sai ki ce baki son shi, ni kuwa anya Zee bata samu matsala a qwalwa ba?”11 Gani nayi ta miqe ta nufi dakin Zehra riqe da wayar. Kwance take a cikin Duvet yayinda tayi zurfi a tunani. Fadeela ce tace “Kina yi mana qaryar baki son shi, do you mind telling me what you are doing with his photos a wayar ki?” Zehra wadda ta juyo da sauri ranta a bace tace “Dee me zai sa ki dinga yi mun bincike a waya??” Fadeela tace “ba bincike nake yi miki ba, it was the last thing da kike kallo a wayar and you forgot to…” STORY CONTINUES BELOW Miqewa tayi ta qwace wayar yayinda tace “Dee don Allah ki tafi ki bani wuri” Fadeela tayi murmushi tace “toh Angel din Baby, he called and I received it.. yace in gaishe ki da kyau and that he loves you very much” Daga nan ta cigaba da fadin “ni na tafi, idan kin sauko nasan zaki neme mu.. Har yau dai muna neman afuwa a bisa laifin da muka yi miki” Zehra dai bata ce mata komai ba har ta fita. Aikuwa Fadeela tana fita na ga ta rushe da kuka. Ni kaina yanzu na fara tunanin lallai Zehra ta samu matsala a qwalwa.🤔 ♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤ A yau sati biyu kenan da tafiyar Mustapha. A kullum Yasmeen sai ta matsa ma Zehra akan tana so tayi Magana da Abbu amman Zehra sai tayi ta kawo mata excuses. A yau daddare suna dakin Yasmeen din yayinda Zehra take ta qoqarin sa ta bacci kamar kullum.  Yasmeen kuwa tada rigima tayi akan lallai sai tayi Magana da Abbu. Excuses din Zehra kuwa sam basuyi tasiri a wurinta ba a yau. Sossai ta dinga rusa mata kuka akan lallai sai tayi Magana da shi. Hankalin Zehra kuwa ya tashi sossai, ita kam ko lambar shi bata yi saving ba sannan ta ya zata fara kiran shi a waya? da ace shi din zai kira ta ne da tayi picking. Babu shiri ta dauko wayarta ta shiga call log ta fara neman lambar wayar shi tunda dai digits din turai daban ne da na Nigeria. Abin mamaki Number din tayi baya domin kuwa sai yanzu ta kula rabon da ta ga missed calls din shi kwana uku kenan. Ko da ta gano lambar zuciyar ta ce take ta bugawa yayinda tayi dialling. Ringing daya kuwa ya dauka kamar dama jiran kiran nata yake yi. Cikin muryar nan tashi mai kashe mata jiki ta ji yana fadin “hello My Angel, finally..” Ba tare da tace komai ba ta miqa ma Yasmeen wadda ta karba cike da murna tace “Abbu… kana ina ne ina ta neman ka?? please come” Can kuma sai ta ji Yasmeen din tace “toh Abbu” Wayar ce ta sake ringing yayinda Tayi saurin miqa ma Zehra alamun tayi answering mata call din. STORY CONTINUES BELOW Zehra wadda ta karbi wayar gani tayi Video call ne. Tana amsawa kuwa ta miqa mata yayinda suka cigaba da hira wanda kuwa Zehra din tana gefe tana ta sauraron shirmen su. Bata ankara ba ta ji yace “koma kusa da Amminki da wayar, I want to see her” Zehra wadda ta cika da mamaki a ranta ne tace “ya aka yi ya san ina nan??” Yasmeen tana riqe da wayar yayinda ta rungume Zehra tace “Abbu ka gan ta??” Mustapha dai shiru yayi ya qura ma Zehra idanuwa wadda tayi masifar kyau, sanye take cikin wata navy blue sleeveless nighty mai shegen kyau, gashin kanta kuwa ya sha gyara sai qyalli yake yi. Ji tayi yace “My angel ki sassauta mun mana, wannan kyan haka ai sai ki sa in baro Italy dinnan ASAP… you look beautiful” Zehra wadda kanta yake a duqe kasa kallon shi tayi yayinda suka ji Yasmeen tana fadin “Abbu don Allah ka dawo, I miss you” Yace “zan dawo my Princess, I miss you too” ya kalli Zehra yace “you too my Angel.. A lot” Dago kai ta dan yi ta kalle shi wanda kuwa ya kashe mata ido daya yana murmushi. Hakan ya sa tayi saurin duqar da kanta yayinda zuciyar ta take ta bugawa, sossai yayi kyau a dan ganin da tayi mishi. Kwance yake a kan gado da alama bacci zai yi. A haka dai suka cigaba da hirar yayinda Yasmeen take rungume da Zehra wadda duk ta zama uncomfortable. Shi kam da gangan ya qi suyi sallama da wuri saboda kallon Zehra da yake ta yi. ************** Tun daga wannan lokacin kuwa kullum sai sunyi waya wanda duk yadda zai yi ya ga fuskar Zehra sai yayi. Sossai Yasmeen take bashi hadin kai wurin tabbatar da yiwuwar hakan. Akan dole kuwa Zehra ta sauko suka koma normal da su Zain. Layla Hayat kuwa bata bar Zehra ba sai da ta gama aikin ta tsab. Ita kanta Zehra idan ta kalli kanta a madubi har tsoro take ji domin kuwa ta qara canzawa gaba daya tayi kyau sai qamshi take zabgawa da qyalli. Gashin kanta kuwa shima sai qyalli yake yi. ♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤ Weeks later.... A kwana a tashi babu wuya. A yanzu saura sati biyu Mustapha ya dawo a lissafin Zehra wanda kuwa gaban ta yake ta faduwa a dalilin fargaba. Ita dai bata qi yayi zaman shi a can ba amma kash, dole ne ya dawo gida babu yadda zata yi. ♤♤♤♤♤♤♤♤ A yau Friday wuraren qarfe takwas da rabi na dare tana tsaye a kicin yayinda take qoqarin kammala Dinner. A wannan lokacin kuwa Yasmeen tana can dakin khadeeja tana wasa yayinda khadeejan take karatu na jarabawar ta da ta kusa farawa. STORY CONTINUES BELOW Ita dai Zehra ko dama idan tana hidimar ta a kicin bata cika damuwa da sai lallai masu aiki suna tare da ita suna taya ta ba don haka ne yawanci da zarar masu aiki sun gama aikin su suke komawa quarters din su sai kuma ta neme su. Zehra wadda take ta shirya dinner dai ta dade tana shaqar qamshin turaren nan wanda take bala’in so a rayuwar ta yayinda zuciyar ta take ta bugawa. A ranta ne tace “meye haka?? why do I feel as if he….” Bata qarasa maganar ta bane ta dauko wani plate ta juyo kawai sai na ga ta sake shi ya fadi qasa ya fashe a dalillin razana ta da yayi. Gani nayi ta dafe qirjinta yayinda zuciyar ta take ta bugawa. Mustapha ne tsaye nesa kadan da inda take wanda ya qura mata idanuwa yayinda hannuwan shi suke cikin aljihun wandon shi. Ya tabbatar da ta sani cewar zai dawo a yau da bata yi shigar da tayi ba. Sanye take cikin wani low waist denim short da wata sleeveless riga very transparent domin kuwa kana ganin Bra dinta clearly a ta cikin rigar. Rigar kuwa daga bayan ta har jan qasa take yi yayinda gaban take a yanke iya cibiyar ta. Ga gashin ta da ta kama a tsakiyar kanta wanda yake ta qyalli banda qamshi da take ta zabgawa. Sossai Zehra ta tafi da hankalin Mustapha. Ita kanta kallon da take yi mishi na bala’in kyau ne da yayi mata. Ganin irin kallon da yake yi mata ne tayi saurin kallon jikin ta. Sossai bugun zuciyar ta ya qaru wanda kuwa tayi yunqurin guduwa amma kash.. bata ankara ba ta ji ta taka piece na broken plate din. Ihun da tayi ne ya ankarar da shi wanda kuwa yayi saurin qarasawa wurinta yana fadin “hey me ya faru??” Zehra wadda take a duqe riqe qafar ta tayi yayinda hawaye suka fara gangarowa daga idanuwan ta. Bata ankara ba ta ji ya dauke ta cak yayinda ta ji yace “yi haquri My Angel, duk laifi na ne…” Ita kam gaba daya ma bata jin abinda yake fadi domin kuwa hankalinta yayi mugun nisa. Tunda ya dauketa ta ji rayuwarta ta canza gaba daya.. ji tayi kamar ta suma domin kuwa jikin ta yayi mugun sanyi. Ga qamshin turaren shi da ya cika ta. Shi kan shi Mustapha a yadda ya dauke ta ji yayi kamar yayi ta zuba mata kisses domin kuwa Zehra ta ruda shi gaba daya. Ga wani asirtaccen qamshi da yake tashi daga jikinta. She looked hot and beautiful.. Idanuwan ta a rufe ta ji ya ajiye ta gently a kan sofa yayinda ya zauna gefenta tare da daga qafarta ya dora bisa cinyar shi yana dubawa. Zehra dai gaba daya jikinta rawa yake yi domin kuwa duk inda ya taba a jikin ta sai ta ji kamar yayi mata shocking. Bata ankara ba ta ji yana ta hura mata iska wanda ya sa ta qara runtse idanuwan ta, hawaye kuwa kamar an saki famfo. Khadeeja ce ta shigo falon yayinda na ga ta tsaya turus tana kallon shi. Sossai ta cika da mamakin ganin shi. STORY CONTINUES BELOW Qarasa shiga falon tayi da sauri tace “laaaa, Ya Musty yaushe ka dawo??” yayinda ta juya ta ga Zehra kwance tana ta kuka. Cike da mamaki tace “why is she crying??” Kai tsaye yace “Deeja kawo mun First aid kit, she stepped on a broken plate..” Khadeeja wadda ta zaro idanuwa tace “shine take rusa kuka haka kamar ta karye?? Wallahi Anty Zee akwai shagwaba..” Mustapha wanda yake qoqarin boye dariyar shi yace “Deeja ina wasa da ke??” Da sauri tace “sorry Sir” yayinda ta tafi dauko first aid din. Zehra dai sai qoqarin janyo rigar ta take yi don ta rufe jikinta amma inaa, babu yadda zata yi. Nikuwa nace "rigar da take a yanke??"🤔 Mustapha wanda ya kula da hakan kuwa yana murmushi ya riqe hannun ta yace “My Angel kar ki yaga rigar, tayi kyau sossai I love it.. Allah yasa kina da irin su dayawa” 🤣🤣🤣 Khadeeja ce ta shigo riqe da first aid kit yayinda ta miqa mishi. Tana nan tsaye yayi mata dressing. Ni da na leqa don ganin ciwon ma ban gan shi ba. Da alama dai kukan wani abu daban take yi ba na ciwon ba. Bayan ya gama ne ya ajiye qafar a hankali sannan ya dago ta ya rungume ta kamar wata Baby yana fadin “sssshhh, daina kuka My Angel” Khadeeja wadda take tsaye sai mamaki take yi yayinda ta ji yace “where is Yasmeen ban gan ta ba, ko tayi bacci….” Aikuwa kafin ya qarasa tambayar ya ganta ta shigo falon. Tana ganin shi kuwa ta sa ihu. A guje ta qaraso wurin shi amma kuma ganin Zehra tana ta kuka ne tayi pause yayinda tace “Ammi why are you crying??” Khadeeja dai tana dariya ta wuce kicin don qarasa dinner domin kuwa da alama mai girkin bazata waiwayi kicin din ba. Mustapha wanda ya janyo ta jikin shi yace “Ammi tana kuka saboda ta ji ciwo a qafa amma she will be fine kin ji??” Yasmeen kuwa har leqa ciwon tayi yayinda hankalin ta duk ya bi ya tashi. Zehra wadda har yanzu yake rungume da ita jikinta gaba daya ya saki domin kuwa ko motsi ta kasa yi. Yasmeen ce take ta share mata hawaye yayinda take ta yi mata sannu. Ko da Khadeeja ta kammala dinner shigowa tayi ta tarar da har wannan lokacin Zehra tana kuka yayinda suke ta lallashin ta shi da Yasmeen. Tana ta danne dariyarta ne tace “dinner is ready” Mustapha ne ya kalli Zehra yace “mu je ki ci abinci..” Zare jikin ta tayi daga nashi sannan tace “na qoshi” ta miqe tana takawa a hankali ta wuce daki. Shi kam zare jikin ta da tayi daga nashi ya taba zuciyar shi domin kuwa sossai yayi enjoying closeness dinsu... he felt her body so soft... ga qamshin da take ta yi wanda yake bala'in so. STORY CONTINUES BELOW Wata nauyayyar ajiyar zuciya ya saki yayinda ya kalli Khadeeja yace “please make sure she eats” Khadeeja ce tace “Yasmeen mu je ki ci abinci” v Yasmeen tace “ni tare da Abbu zan ci” Shi kam Mustapha ba yunwa yake ji ba don haka ne yace “Princess je ki ci abinci, Abbu zai je ya huta. Idan kin gama Anty Deeja zata kawo ki wurina kin ji??” Tace “okay Abbu” ♤♤♤♤♤♤♤♤ Washegari wuraren qarfe tara da rabi na safe yana kwance a kan gadon shi yana bacci ne ya ji alamun ana ta taba shi. Muryar ta ya ji tana fadin “Abbu ka zo ka ga Ammi tana kuka” Mustapha wanda ya juyo ne ya ga Yasmeen a rude. Janyo ta yayi yace “me ya same ta take kuka??” tace “nima ban sani ba Abbu” Mustapha dai a yanzu ya fara shiga damuwa akan wannan kukan na Zehra, shi kam ya rasa ma me zai ce mata. Tashi yayi yace “mu je mu bata haquri” Kwance take cikin Duvet tana ta kuka a lokacin da suka shigo dakin. Da sauri ta dago don ganin ko waye wanda kuwa tana ganin shi ta koma ta shige cikin Duvet din. Ita dai bata so ko alama Mustapha yana zuwa inda take. Yanzu haka da ta gan shi dukda daga bacci ya tashi yayi masifar yin kyau. Bata ankara ba ta ji ya shige bargon ya kwanta a bayan ta tare da janyo ta jikin shi. Aikuwa nan da nan jikin nata ya fara rawa, numfashinta kuwa ya ma kusa daukewa. Bakin shi ya kai saitin kunnen ta yace “I swear idan baki daina wannan kukan naki ba zanyi ta baza miki kisses a gaban Yasmeen..” Zehra dai jin wannan maganar tashi ce na ga ta fara share hawayen ta yayinda Yasmeen tace “Abbu meyasa take kuka?? Ciwon ta ne yake zafi??” Yana shafa gashin Zehra yace “Ammi tayi missing dina ne shiyasa take kuka” Yasmeen tace “nima nayi missing dinka Abbu” murmushi yayi yace “I missed you too my Princess” Mustapha wanda yake rungume da ita ne yace “My Angel ki daina kuka, I am home now...” Bata ankara ba ta ji ya yaye Duvet din wanda kuwa na ga yayi pause a dalilin ganin yanayin kayan baccin da ke jikinta. Wata baqar sleeveless nighty ce wadda iyakar tsawon ta saman gwiwowinta. A yanzu haka kuwa ta tattare domin kuwa cinyoyinta a bude suke. Komawa yayi ya kai bakin shi saitin kunnen ta yace “My Angel idan kina sa irin wadannan fa zaki sa in fara kwana dakin nan” Runtse idanuwa tayi yayinda take ta qoqarin gyara rigar. Shi kam dariya yayi sannan ya zame wurin qafarta yace “ciwon ya daina zafi??” Zehra dai bata amsa shi ba, gaba daya a rude take. Ji tayi yana ta shafa qafar nata yayinda yace “I think its okay” Komawa yayi daf da ita yace “I am sorry for everything My Angel” yayi mata kiss a kumatu sannan ya sauka daga kan gadon ya janyo Yasmeen wadda tace “Abbu ta daina kuka??” Yace “yes Princess, idan tayi kuka zan zane ta” Yasmeen kuwa ta dinga dariya yayinda suka bar mata dakin. Aikuwa suna fita na ga ta shafa kumatun ta sannan ta kwanta yayinda ta tura kanta qarqashin pillow tana ta rusa kuka.. Ji nayi tace “Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un, na shiga uku... ya zanyi ne??” ♤♤♤♤♤ MUSTAPHA OMAR TAFIDA RESIDENCE A yau sunday Khadeeja dai tun da safe ta tattare kayan ta tayi tafiyar ta gida domin kuwa sossai abinda Zehra take yi yana bata haushi.3 Laifin Mustapha take gani da ya biye mata yana ta wani lallashinta, tana wani pretending bata son shi bayan kowa ya san bala’in son shi take yi.5 Mustapha yayi da ita akan ta qara ko da sati daya ne kafin ta tafi amma sam ta qi zama dukda kuwa bata gaji da gidan ba amma dayake Zehra tana bata haushi shiyasa tayi tafiyarta. ************* Bayan sallan la’asar yana tsaye gaban Vanity mirror din dakin shi yana brushing gashin kan shi. Sanye yake cikin wandon sweatpant grey colour da baqar T-shirt. Sossai yayi kau. Da alama ma fita zai yi. Bayan ya gama feshe kan shi da turaruka ne ya ji an bude qofar dakin shi wanda kuwa yana juyowa ya ga Yasmeen da gashin ta buzu-buzu ta rugo a guje tana fadin “don Allah Abbu ka boye ni.. Ammi zata kama ni” Da gudu ta qarasa wurin shi yayinda ta boye a bayan shi. Zehra wadda ta biyo ta a guje ji nayi tana ta masifa tana fadin “wallahi Yasmeen idan kika bari na kama ki sai na mare ki…” Tsayawa tayi cak yayinda na ga tana qare ma dakin kallo. Sossai dakin Mustapha yayi ma Zehra kyau. Abin mamaki babu wasu tarkace a ciki amma fa komai white, looking so simple but very elegant. Ga sanyin AC wanda ya gauraye da qamshin turaren shi ya bada wani yanayi mai dadin gaske. Ajiyar zuciya ta saki yayinda ta jiyo muryar shi yana fadin “hey, meyasa kike gudu?” Ji tayi Yasmeen din tana fadin “Ammi ce zata yi mun kitso kuma ni bana so” Yace “haba Princess, tomorrow is Monday kiyi haquri tayi miki, ko kina so idan kika je school a aske miki gashi??” Yasmeen wadda take bala’in son gashinta kuwa nan da nan tace “a’a Abbu” Yace “toh yanzu dai ki je tayi miki kin ji?” Gani yayi ta bata rai har tana neman yin kuka yayinda yayi saurin fadin “idan tayi miki nima zata yi mun, kin amince??” Gani suka yi tayi murmushi ta kalli Zehra tace “Ammi zakiyi ma Abbu??” Ita dai Zehra shiru tayi tana kallon su yayinda yace “zata yi mun My Princess amma ke ce first, Oya follow your Ammi..” Da sauri tace “No Abbu, a nan zamu yi” Bai ankara ba ya ga ta haye kan gadon shi yayinda yayi murmushi yace “a kan gado ake yin kitson??” tace “eh Abbu, come” Mustapha wanda ya kalli Zehra ne yace “yi haquri kiyi mata anan din My angel” Zehra dai bata ji dadin wannan abun ba. Ji tayi kamar ma tace ta fasa. Hakanan ta dauko kayan kitson ta dawo. Tana zaune a kan gadon yayinda Yasmeen take kwance a kan cinyarta riqe da hannun shi suna ta hira. Ita dai Zehra sauraron su kawai take yi yayinda take mamakin yadda Mustapha baya gajiya da wasa da yara. Tambayoyi kuwa ya sha su. Shi kam gaba daya hankalin shi na kan Zehra wadda tayi mishi masifar kyau. A yanzu haka sanye take cikin wandon three quarter na Jeans da wata 'yar qaramar T-shirt wadda tayi Mata kyau sossai. Kanta akwai hula don haka bai samu damar ganin gashin nata ba sai jelar shi da ya kwanta har gadon bayan ta. STORY CONTINUES BELOW A yau kuwa nan da nan aka gama kitson saboda ta natsu sossai ba kamar sauran ranaku ba. Zehra dai tana gama mata ne ta yuqura zata tashi yayinda Yasmeen tayi saurin riqe hannun ta tace “Ammi bakiyi ma Abbu ba” Zuciyar ta ce ta buga yayinda tace “sai gobe zanyi mishi” Mustapha wanda ya kula duk ta bi ta rude ne yace “ban yarda ba Ammi, yanzu zakiyi mun nima” Yasmeen tace “please Ammi” Zehra dai gaba daya ta daburce. Banda shirme irin na Yasmeen ya za’ayi tayi ma Mustapha kitso. Bata ankara ba ta ji ya kwanta a kan cinyar ta wanda har sai da ta zabura saboda razana da tayi. Yasmeen wadda ta ga Zehra tayi pause ne tace “Ammi kiyi ma Abbu...” Babu shiri Zehra ta sa hannu a bisa gashin kanshi wanda yayi daidai da faduwar gaban ta. Gashin da ya dade yana bata sha'awa... Wanda ta dade tana son tabawa... yau gashinan an bata damar tayi yadda ta ga dama da shi. Qamshin da yake tashi daga kan nashi ne ya sa ta lumshe idanuwa yayinda hankalinta yayi nisa. Shi kam kwanciya da yayi akan cinyarta ne yasa shi shiga wani yanayi mai dadi. Ji yake kamar su kasance a haka har abada. Wani sanyi yake ratsa shi musamman yadda ya ji take shafa kan shi. Gani nayi ya gyara kwanciyar shi akan cinyar ta wanda kuwa suka cigaba da hira da Yasmeen. Nan da nan bacci ya kwashe shi. Yasmeen kuwa tana ta magana ta ji Abbu shiru, itama daga nan ta zame ta kwanta ta qirqiro baccin. Tsawon awa daya da rabi Mustapha yana ta baccin shi cikin kwanciyar hankali yayinda take ta kallon shi, ko motsin kirki ta kasa yi saboda kar ta tada shi ganin yadda ya ji dadin kwanciyar. Abin mamaki har a wannan lokacin tana ta shafa kanshi yayinda ta kafa mishi idanuwa. wasu tunani take ta yi wanda suka tafi da hankalinta gaba daya. Bata ankara ba ta ji ya motsa wanda tayi saurin zare hannun ta daga kan shi yayinda take qoqarin composing kanta. Tashi yayi zaune yana kallon ta cike da mamaki. Ji tayi yace “My Angel shine kika yi ta zama baki tada ni ba??” Zehra dai duk ta bi ta rude yayinda ya cigaba da fadin “I was even supposed to go out fa..” ya kalli agogo ya ga magrib ta kusa sannan ya juyo ya kalle ta yayi murmushi yace “But I really enjoyed my sleep, looking forward to having more of it.. thanks” Ya duqo yayi Mata kiss a goshi sannan ya sauka daga kan gadon ya wuce dressing room din shi. Ajiyar zuciya ta saki yayinda ta sauka daga kan gadon ta bar dakin kafin ya dawo domin kuwa wani yanayi yake sa ta shiga a duk lokacin da take within same space da shi. ************* Bayan sallan Isha’I yana zaune a falon shi yana waya da Mummy wadda take yi mishi tsiya ya dawo daga tafiya ya maqale a cikin gida saboda amarya. Mustapha wanda yake dariya yace “wallahi Mummy dazu na so fitowa amma bacci ya kwashe ni.. Insha Allah gobe zaki gan ni” Mummy a dayan bangaren tace “Kayi zaman ka ma ka huta Mustapha, ai da gajiya” Yana murmushi yace “ai na saba..” Tace “ina amaryar taka da Yasmeen? suna lafiya ko?” yace “they are fine Mummy” tace “my regards to them” yace “Insha Allah, sai na zo gobe” STORY CONTINUES BELOW Bayan ya kashe wayar ne Yasmeen ta shigo falon riqe da wani drawing ta qaraso wurin shi tace “Abbu see” Mustapha wanda yake murmushi ya karbi drawing din ya ga zanen mutane uku. Yana dariya yace “su waye wannan Princess??” Tace “da kai da ni da Ammi” Zaro idanuwa yayi yana dariya yace “yanzu ni ne mai qaton kan nan Princess.. haba dai” Gani nayi ta kalli kan shi sannan ta kalli drawing din tace “sorry Abbu, zan zana wani” yana murmushi yace “okay my princess please do, ina Ammin ki??” Tace “tana kicin” Gani nayi ya miqe yace “mu je mu ga abinda take yi” ************* Tsaye take a wurin kicin Island yayinda take sa Greek Yoghurt akan desert din da tayi. Sanye take cikin wata Jumpsuit wadda tayi mata kyau sossai. Jin motsin su ne ta waigo ta dan kalle su sannan ta kawar da kanta. Bata ankara ba ta ji yayi hugging dinta ta baya tare da yi mata kiss a kumatu yace "hello beautiful.. kinyi kyau" Zehra dai pause tayi yayinda zuciyarta take ta bugawa... gaba daya jikin ta yayi sanyi sannan ga qamshin turaren shi da ya haukata ta. Mustapha wanda ya sake ta ne ya ja kujerar da take kusa da ita ya zauna sannan yace “My Angel this looks good...” Ita kam hankalinta yayi nisa da bata ma san yana magana ba. Daukar Yasmeen yayi ya dora ta bisa Island din yayinda suka cigaba da kallon ta har Yasmeen tana fadin “Ammi zan ci wannan” Wayar ta ce tayi ringing, ko da ta duba sunan Hidaya ta gani... jiki a sanyaye ta dauki wayar ta bar musu kicin din. Aikuwa tana fita Yasmeen tace “Abbu ni zan ci..” Mustapha wanda shi kan shi desert din yayi mishi kyau ne yace “bari ta dawo sai mu tambaye ta Princess”5 Ganin ta bata rai ne yace “okay toh bari mu dan ci kadan sai mu rage mata”  Gani nayi ya janyo bowl din suka fara ci. aikuwa sossai desert din yayi mishi dadi. Zehra dai shigowa tayi ta tarar sun cinye mata shi tas. Sossai ran ta ya baci yayinda tace “meye haka??” Juyowa suka yi suna kallon ta yayinda suka zaro idanuwa kamar wadanda suka yi qarya. Da sauri Yasmeen ta nuna Mustapha tace “Abbu ne..” cike da mamaki yace “whaat?? My angel don’t listen to her… she wanted to” Kafin ya qarasa maganar Zehra ta fita tana kuka.4 Sossai ta ji haushi domin kuwa ta so cin desert din. Gani nayi suna kallon juna yayinda Yasmeen tace “Abbu, Ammi tana kuka ne??” ya girgiza kai alamar 'eh' sannan yace “My princess I think we need to make another one for her. STORY CONTINUES BELOW ************ Zehra tana kwance a dakinta tana kuka ne ta ji motsin shigowar su. Mustapha ne riqe da bowl yayinda Yasmeen ta haye kan gadon tace “Ammi ki daina kuka, ga wani mun kawo miki” Zehra dai yi tayi kamar bata ji ta ba. Bata ankara ba ta ji ya sa hannu ya dago ta wanda kuwa babu shiri ta zauna. Yana ta kallon fuskar ta yace “My angel wai dama tun da can ke cry baby ce ban sani ba??” Yasmeen tana dariya jin an kira Amminta da cry baby yayinda ya dauko bowl din dessert din da suka hada ya ajiye a gaban ta yace “its not exactly the same but you should manage please, kiyi haquri bazamu qara ba” 6 (hahahahaha... kayi qoqari Musty🤣) Zehra dai gani nayi ta qura ma bowl din idanuwa yayinda ta ji yace “sorry for stirring the Yoghurt, Yasmeen ce ta motsa...” Ita dai Zehra duk ba wannan bane matsalar ta. Kiwifruit din da ya zama missing shine problem din. Wanda ya rage mata na qarshe shi tayi using and its very important for her saboda sleep inducer ne which has no side effect. Tun dawowar Mustapha baccin kirki yake gagarar ta saboda yawan tunani da take yi. Shi kam Mustapha da bai ga Kiwifruit din bane yayi replacing da Gooseberries. A tunanin shi duka fruits ne kuma tunda dukkan su green colour ne its the same. 😏😏 Zehra dai bata ankara ba ta ga spoon saitin bakin ta alamar yana so ya bata da kanshi. Yasmeen wadda ta sa musu idanuwa ce tace “Ammi Please ki ci” Gani yayi ta fashe mishi da kuka. Sossai Mustapha yayi mamaki. ya zama so confused that he didn't know what to do. Ya kula Zehra cries over trivial issues which is not normal.. Ya sani sarai shine yake sanya ta kuka. the question still remains... WHY?? Gani nayi ya matsa daf da ita yayi hugging dinta tare da fadin "don Allah kiyi haquri ki daina kuka, I am sorry please... kin ga we made this with so much love" Ya nuna Yasmeen yace "idan baki ci ba she won't be happy.. please ko kadan ne ki ci" Ita kam Zehra gaba daya ya birkita mata qwalwa.. bata so yana kusantar ta haka. Jikinta mugun sanyi yake yi. Cokali ya kai saitin bakin ta sannan yace "please my Angel" Hakanan ba don ta so ba ta bude baki ya sa mata. Yasmeen ce tace "Ammi akwai dadi??" Akan dole ta daga mata kai alamar 'eh' wanda kuwa ta dinga murna. A haka nan ta dinga ci yayinda zuciyarta take ta bugawa a dalilin kusancin da yake tsakanin su a wannan lokacin. STORY CONTINUES BELOW Sai da ta cinye shi tas sannan yace “thanks My Angel” Yayi mata kiss a kumatu yace "good night, I love you" Yasmeen ma kiss tayi mata a kumatun sannan suka fita. Suna fita kuwa ta cigaba da sana'ar ta... kuka.3 🤔🤔🤔 ♤♤♤♤♤♤♤♤♤ Washegari.. Da safe ne Zehra ta fito zata tafi ofis yayinda za’a sauke Yasmeen a school. Driver ne yace “madam Good morning, Oga said he will take you…” Kafin ya qarasa Magana ne Mustapha ya fito sanye cikin wandon three quarter na Camo da T-shirt. Da ganin shi ma kasan tashin shi daga bacci kenan. Ko da Yasmeen ta hango shi a guje ta ruga wurin shi tace “Abbu Good morning” Mustapha ya dauke ta yace “morning my Princess, yau Abbu zai kai ki school da kan shi” Cike da murna tace “yeeey” Daya daga cikin masu aikin gidan mai suna Rabi wadda take riqe da Lunch box din Yasmeen ce ta duqa har qasa ta gaishe shi yayinda ya amsa, Haka sauran ma’aikatan gidan suka dinga kawo mishi gaisuwa yana amsawa.. As usual dai fuskar shi babu fara’a. Zehra wadda take tsaye kallon su kawai take yi yayinda ranta yake a bace. A yau tayi regretting rashin iya tuqa mota because da ta iya kuwa babu abinda zai sa ta bi shi. Bata ankara ba ta ji yayi mata kiss a kumatu tare da fadin “morning My Angel” hakan kuwa sai da ya sa ta zabura yayinda ta ji yace “mu je kar Yasmeen tayi latti” Haka nan ba don ta so ba ta bi bayan shi yayinda suka nufi parking lot. Gani tayi yawan motocin da suke wurin sun qaru a yanzu. Kenan dawowar shi ne aka qaro su. Motoci guda shidda a cikin takwas din da suke parking lot din duka farare sannan duka Mercedes Benz. Asali guda biyun da drivers suke using su ne kadai black. Wata dalleliya ta ga ya nufa yayinda ya bude baya ya sa Yasmeen. Rabi ta zuba Lunch box din Yasmeen sannan tayi ma Yasmeen din bye-bye ta koma cikin gidan. ♤♤♤♤♤♤♤♤ Ko da suka bar gidan Yasmeen ce take ta yi musu surutu wanda kuwa kamar kullum Ya biye mata suna ta yi. Zehra wadda take kallon gefe ne ta ji ya riqo hannun ta wanda kuwa hakan ya sa ta waigo da sauri tana kallon shi yayinda zuciyarta take ta bugawa. Shi kam yana riqe da hannun nata ba tare da yace mata komai ba har suka iso school din. Bayan sun sauke Yasmeen a school ne suka wuce ofis din Zehra. A yanzu kuwa tension ya qaru mata domin kuwa har ga Allah bata so a barta daga shi sai ita... Muryar shi ta ji yana fadin "My Angel don Allah ki fadi mun abinda nayi miki da kike treating dina haka. A tunani na abinda ya faru a baya ya riga ya wuce... Bana son ganin ki cikin damuwa my Angel.. bana so in ga kina kuka a dalili na.. wallahi zuciya ta quna take yi. Idan akwai abinda nayi miki please tell me and I will apologize to you, anything you want I swear I will do but please.." Kafin ya qarasa maganar shi kuwa ya ji ta fashe da kuka. Hakan kuwa ya tada mishi hankali sossai. Da sauri yace "yi haquri please ki daina kuka.. na bar maganar" ♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤ EM-ZEE KITCHEN AND CATERING SERVICE Har suka iso ofis dinta bai qara yi mata magana ba sannan bai saki hannunta ba. Zehra kuwa sossai ta ji dadin da suka iso domin kuwa ita kadai ta san yadda take ji a dalilin wasa da yatsun hannunta da yake yi. Ko da yayi parking qin sakin hannun nata yayi. Muryar ta tana rawa tace “zan tafi” Juyowa yayi ya fuskance ta sannan yace “gashi ni kuma bana so ki tafi My Angel” gani tayi ya dago hannun nata yayi mata kiss wanda ya sa duk ta bi ta rude. Ji tayi yace “take care, see you later… I love you” Yana bude mata lock ta fita jikinta a sanyaye yayinda ya bi ta da kallo har ta shige cikin ofis din wanda kuwa sai gaishe ta ake yi. Zuciyar ta tana ta bugawa ta shiga ofis din. Tana zama bisa kujerar ta kuwa na ga ta dora kanta a bisa table dinta ta fashe da kuka.2 Hidaya wadda ta ga shigowar ta ce ta shigo ofis din, Ganin ta tana ta rusa kuka ne ta qarasa wurin ta da sauri yayinda ta dafa ta tana fadin “Zee what is wrong with you, me ya faru?? hala Babyn naki ne??” Cikin kuka tace “Na shiga uku Hidaya, living with him under the same roof is going to make me run mad.. His presence makes me restless... Hatta bacci gagara na yake yi. Ni wallahi bazan iya ba” Hidaya wadda take cike da mamaki tace “bazaki iya me ba?? wai Zee me ke faruwa ne?? why are you hell-bent on claiming you don’t love him anymore?? Kowa fa ya san cewar bala’in son shi kike yi… what is the reason behind all these façade of yours?? Please tell me” Zehra wadda take kuka ta girgiza kai alamar bazata fadi ba yayinda tace “ni kawai a raba ni da shi, Its true I loved him before… I loved him very very much even more than my life amma abubuwa sun canza yanzu I don’t love him anymore, I don’t want to be his wife I don’t want to live with him.. ” Ta qara fashewa da kuka tace “please help me Hidaya, wallahi I feel suffocated whenever he is around me.. zuciya ta tana shiga matsala a duk lokacin da ya matso kusa da ni, qafafuwa na sanyi suke yi idan ya taba ni yayinda nake ji kamar numfashi na zai dauke, qamshin turaren shi ruda ni yake yi, being close to him is torture” Hidaya wadda ta tausaya ma halin da qawar ta take ciki ne ta rungume ta yayinda tace “ssssshhhh, Zee I really don’t know what to say, the truth is that you are madly in love with him… the truth is you can't live without him.. He is your life Zee… you loved him years ago, you loved him even after you got married to his brother, you still love him now. Ki amince da hakan kawai ki...” Zehra dai janye jikinta tayi daga Hidaya yayinda ta miqe ta shige wash room. Ita kam Hidaya bin ta tayi da kallo sake da baki yayinda take mamaki. Ji nayi tace "Anya lafiyar Zee kuwa???” ♤♤♤♤♤♤♤♤ What is wrong with our Zee???7 I remember somebody commenting that qila Aljanu suka shige ta🤣🤣🤣8 Get ready for an outburst my people!!!8 Zehra ta fara jin pressure... da alama ta kusa bayyana mana sirrin da yake zuciyarta a game da Mustapha..3

0/Post a Comment/Comments

Recent Posts

Your Ads Here
73745675015091643
Your Ads Here
Your Ads Here